Posts

Showing posts from 2017

AISHA AUGIE KUTA

Image
AISHA AUGIE KUTA An haifi Aisha Augie a garin Zaria, a ranar 11th April, 1980. Ɗiya ce ga marigayi   Sanata Adamu Baba Augie da Justice  Amina Adamu. Ta yi aure tana da yara uku maza.   Ta yi karatun digiri ɗinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta karanci fannin Mass Communication. Inda ta ke Masters ɗinta a bangaren Media and Communication a jami'ar Pan African University da ke Lagos.  Aisha Augie kwararriyar mai daukar hoto ce, wanda hakan ya samo asali daga kyautar kyamara (camera) da mahaifinta ya ma ta.  Abin mamaki ne a Nijeriya kuma yankin Arewa a ga mace na daukar hoto, sai dai a wajen Aisha Augie daukar hoto abu ne da ta dade tana sha'awar yi.  Aisha Augie mace ce da ta jajirce wajen ganin cigaban yara mata da kuma matasa baki daya. Ta kasance mai bada gudunmuwa a harkokin da suka shafi yara mata, dalilin hakan ne ma UNICEF ta rantsar da ita a matsayin "High Level Women Advocate on Education with a focus on girls and young women&qu

UMM ZAKIYYAH

Image
UMM ZAKIYYAH   An haifi Umm Zakiyyah a shekarar 1975, a Long Island dake ƙasar New York. Kafin a haife ta iyayenta mabiya addinin Kirista ne, Mahaifiyarta mai suna Delores Moore da mahaifinta Clark sun musulunta ne ana dauke da cikin Umm Zakiyyah. Ita ce ɗiya ta farko da aka haifa cikin musulunci a gidansu, inda aka sa ma ta suna "BAIYINAH". Umm Zakiyyah ta kashe mafi yawan lokuttan ta wajen rubuce-rubucen maƙala, rubutun waƙe a jaridu. Zamanta ɗaliba a jami'ar Emory da ke a Atlanta ta ƙasar Georgia. Ta sadaukar da mafi yawan lokuttan ta wajen rubuce-rubuce a jaridar da makarantar su ke fitarwa ta ɗalibai. A shekarar 1997 ta kammala karatunta na digiri, inda ta fito da kwalin digiri a bangaren BA. Elementary Education. Daga nan ta fito a matsayin Marubuciya, Malama kuma mai bada darussa akan al'amuran rayuwa. A shekarar 2001 ne ta fitar da littafinta na farko mai sunan IF I SHOULD SPEAK, littafin da ya ƙara fito da baiwar da Allah ya yi ma Umm Zakiyyah a banga

LALE MARHABIN

Image
Lale marhabin da zuwan wannan rana Ranar da garin Makka ya haskaka Ranar haihuwar fiyayyen halitta  Ɗaha Musɗafa baban Zarah Duk mai son Ɗaha ya so ahalinSa Miji ga Khadijatu, angon Aishatu Amini ga Abubakar Saddiqu Siriki ga Aliyu ɗan abi Talib Zuwan Ɗaha duniya ta haskaka Ya kawo mana hanyar shiriya  Domin tsira a gobe ƙiyama Muna ma su Haske da walwali Ɗaha ya zo mana da littafi  Wanda anka kira da Qur'ani Saƙo daga sarkin sarakuna Allah mabuwayi gagara misali   Ɗaha mai kira zuwa ga tauhidi  Domin tsira  a hawan siraɗi Ɗaha masoyi ga al'ummarsa Ya roƙi salama ga al'ummarsa Mu so Manzonmu mai dubun falala  Kyawawan halayen Ɗaha sun yawaita  Duk wanda ya yi koyi da shi ya rabauta  Kowa ya ƙi Ɗaha ya kafirta  Lale marhabin da wannan rana  Ranar haihuwar fiyayyen halitta  Ɗaha Musɗafa baban Al-Qaseem Kaka ga Hassan da Hussaini Ya Allah ka dado tsira  Ga Manzonka mai farar aniya Don shi anka ƙagi duniya Ɗa ga Aminatu da Abdallah  Sallallahu a

MARUBUCIYA HAFSAT ABDULWAHEED

Image
MATAN AREWA HAJ. HAFSAT ABDULWAHEED An haifi Hajiya Hafsat Abdulwaheed a jihar Kano, an haife ta a ranar 5th May, 1952. Tayi karatun firamare ɗinta a ' Shahuci Primary School' dake a Kano. Daga nan ta wuce sakandiren ƴan mata ta Provincial Girls School wanda aka sauya ma suna zuwa Shekara Girls Secondary School. Tayi aure a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida ( 1966 ),ta auri Muhammad Ahmad Abdulwaheed, tana zaune a jihar Zamfara. Ta na da ƴaƴa, daga cikin ƴaƴanta akwai Kadaria Ahmad fitacciyar ƴar jarida. Marubuciya ce dake rubutunta cikin harshen Hausa. Hajiya Hafsat ta fara rubutu ne tun tana makarantar firamare, inda ta samu damar ƙarbar lambobin yabo daga British Council. A shekarar 1970 Haj. Hafsat ta shiga gasar Rubutu da kamfanin maɗaba'ar wallafa littatafai ta Northern Nigerian Publishing Company (NNPC) ta gudunar, inda ta shigar da labarinta mai suna 'SO ALJANNAR DUNIYA'. Wanda ta rubuta shi tun tana aji biyar na firamare. Labarin SO AL

SAI MAZA SUN CANZA

Image
SAI MAZA SUN CANZA! © AYEESH CHUCHU ayeeshasadeeq2010@gmail.com A wannan zamanin da mu ke ciki rayuwar aure ta zama wata irin bahaguwar rayuwa, wadda akan kasa gane kanta a wasu lokuttan. Maza kune Allah ya ba ragamar jan akalar gidajenku, ku ne shuwagabanni masu mulkin alƙaryar gidajensu. Hakan ya zama abin tutiya, nuna iko da isa a cikin alƙaryarku. Har wasu kan yi amfani da wannan damar wajen aiwatar da mulkin kama karya a cikin gidajensu. Dukkanku za ku tsayu gaban Allah a ranar gobe ƙiyama kuna q nannaɗe acikin sarƙa har sai kun tsira daga kun sauke haƙƙin da Allah ya rataya a wuyanku na iyalanku. Ba'a ba ku wannan mulkin ba face dan kun kasance marasa rauni,amma kadan daga ciki ne ke kwatanta adalci a tsakanin su da iyalansu. A wannan zamanin ne da mu ke ciki miji da Allah ya daura ma nauyin iyalinshi be damu da su ba, kullum cikin fita yake ya nemo amma hakan be sa ya sauke nauyin da ya rataya akansa ba. Wani ya tafi ya bar matar da ɗawainiyar ƴaƴansu, ita ce cinsu it

IYAYE MATA

Image
IYAYE MATA Iyaye su ne mafi kusa da yaransu, wadanda su ka san shige da ficen yaransu saboda su ke zaune da su gida fiye da iyaye maza. Iyaye mata su ne mafi kusanci da yara musamman ma ɗiya mata. Wasu iyaye mata za a samu sun zama tamkar ƙawayen juna a cikin ƴaƴansu mata, har ta kai mutum zai iya shigowa gida ya ƙasa bambance uwa da yaran ta. Wasu iyayen mata na ganganci wajen watsi da al'amuran yaransu musamman mata. Ba su damu da su zama abokan ƴaƴansu ba, ta hakan hanya mafi sauki da uwa za ta janyo ƴaƴanta kusa da ita, ya zama ko matsala gare su itace ta farko da zasu fara tunkara dan ta warware ma su matsalolinsu, ita ce abokiyar shawararsu. Idan Uwa ba ta jawo ƴaƴanta a jiki ba wa zai ma ta? Musamman yara mata sai sun zama tamkar kawayen juna ta hakan ne za ta yisaurin gane matsalolinta,idan kuna da kusanci sosai kun zama tamkar abokan juna da ɗiyarki kafin ta je wani waje neman shawara wajen ki za ta fara zuwa neman shawararki. Amma watsi da yaran da iyaye mata kanyi na

ILIMIN ƳA MACE

Image
MUHIMMANCIN ILIMI, AIKI KO SANA’AR ĎIYA MACE  ©Ayeesh Chuchu  Musulunci cikakkiyar hanya ce dake cika kamalar mutum. Duk wani aiki da musulmi zai gabatar matukar da kyakkyawar niyya zai samu ladan aikinsa.  Babu addinin da ya ba mace ‘yancinta kamar addinin musulunci. Addinin musulunci ne ya yi adalci a tsakanin hakkin mace da na namiji. Hakanne ma ya sa addinin islama be bambamce tsakanin mace da namiji ba wajen neman ilimi.  Addini musulunci addini ne na masu ilimi, wanda ya kwadaitar da neman ilimi. Ba’a turo annabawa ba face dan su isar da sakon Allah SWT na ilimi, kamar yadda yazo a cikin ALQUR’ANI mai girma in da Allah SWT Ya bayyana dalilin aiko da Manzo.  [Suratul Baqara aya ta 151  ﴿ﻛَﻤَﺂ ﺃَﺭْﺳَﻠْﻨَﺎ ﻓِﻴﻜُﻢْ ﺭَﺳُﻮﻻً ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﻳَﺘْﻠُﻮﺍْ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﺀَﺍﻳَــــٰـــﺘِﻨَﺎ ﻭَﻳُﺰَﻛِّﻴﻜُﻢْ ﻭَﻳُﻌَﻠِّﻤُﻜُﻢُ ﭐﻟْﻜِﺘَــــٰـــﺐَ ﻭَﭐﻟْﺤِﻜْﻤَﺔَ ﻭَﻳُﻌَﻠِّﻤُﻜُﻢ ﻣَّﺎ ﻟَﻢْ ﺗَﻜُﻮﻧُﻮﺍْ ﺗَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ﴾  “Kamar yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ayoyinMu a gare ku kuma y

LEFE

Image
LEFE  ©AYEESH CHUCHU    Lefe dai kaya ne na al’ada da ango ke haɗawa matar da zai aura akai gidansu kafin aure (a tawa fahimtar).     A wannan zamanin da mu ke ciki lefe yayi sanadiyar hana aure da dama. Wasu saboda ba’a haða lefen yanda su ke so ba. Yawancin matsalar tsegumin lefe na tasowa ne daga dangin amarya.   Daga ranar da aka kawo lefen budurwa gidansu, tofa maganar lefen nan ya zama hot talk a cikin unguwa da gari baki daya, ba kamar dai idan an haða duk abubuwan da yarinyar da danginta ke bukata.   Sai ka ji ana cewa “Ai Indo ta yi goshi wallahi wannan lefe haka”.   “kai yarinya mai farin jini”.  “Lallai wannan angon na ji dake irin wannan ubansun kaya da ya lafto”.   Da dai makamanta zance irin haka. Idan kuwa aka yi rashin sa’a lefen be haɗu yanda ake so ba, sai ku ji ana cewa “Amma dai wannan angon anyi matsiyaci”.  “abin haushi ko yar super nan ta yayi be saka ko guda ba, babu Dubai Lace bare wata babbar shadda”.   “Yoo abinda atampopin ma duk na dubu uku ne da

AMOSARIN JINI (SICKLE CELL ANEMIA)

Sickle Cell Disease (CUTAR AMOSARIN JINI)  ©Ayeesh Chuchu  Sikila cuta ce da ake gada daga iyaye wadanda suke dauke da carrier na sicklecell wato S a cikin jinin su. Walau su kasance dukkansu AS ko SS..  Ita wannan cuta ta Sikila tana kama jajayen jinin halitta (redblood cells) wanda take saka su lankwashewa su yi kamar lauje. Wannan tauyewar da red blood cells keyi Shi ake kira da Sicklecell Disorder.  Su wadannan red blood cells ɗin da suka gurbace su kan toshe magudanan jini su hana Iskar oxygen shiga yanda ya kamata.  A sanadiyar hakan sikila takan jawo lalacewar zuciya, hunhu, koda, hanta, kasusuwa (bones) da spleen. Masu dauke da wannan cutar suna fama da ciwuka akai-akai a sanadiyar gurbataccen jinin da ke dunqula a gefe guda yana toshe hanyoyin jini.  Ana yawan samun cutar sikila a yankin Africa, African-American, South and Central America etc. Mutane ma su dauke da sikila suna fama da yawan kasala, ciwon gabbai,sarkewar numfashi, karancin kwayoyin halitta da ke sa girma

JIN ƘAN IYAYE

JIN KAN IYAYE   © Ayeesh Chuchu   Muna cikin wani zamani da ƴaƴa basu cika jin tausayin iyayensu ba. Ka yi girman da Allah ya hore ma ka amma ba za ka iya daukar nauyin iyayenka ba. Iyayen nan fa su suka raine ka har ka kai wannan matsayi da ka ke a yanzu.    Su suka tarbiyyantar da kai har wata ta gani ta kyasa. Bayan Allah madaukakin sarki babu halittar da ta cancanci godiya irin iyaye da su ka kawo ka duniya har ka zama abin da ka zama a rayuwa.   Allah SWT ya umarce mu da mu kyautatawa iyaye matukar kyautatawa. Wanda a yanzu kadanne ke kyautatawa iyaye, hakan yafi yawa ga maza waɗanda hakkin iyaye yafi rataya akawunansu, wasu daga sun yi aure sun fara tara iyali shi kenan sai su fita harkar kyautatawa iyaye, sun fifita iyalansu sama da iyayensu. To ɗan uwa bari ka ji, iyalanka da ka kyautatawa sama da iyayenka yanda ka yi ma iyayen nan suma sai sun maka sama da haka. Yanda ka ke kyautatawa iyayenka haka yaranka za su taso da ƙaunar ganin sun ji tausayinka.   Har aya aka saukar

ADDU'A MAKAMIN MUMINI

ADDU'A MAKAMIN MUMINI ©Ayeesh Chuchu  Ina matasa marasa aure?    Kun taɓa kawowa a ranku cewa addu'a babban makami ne  a yayin da ka/ki ke neman aboki ko abokiyar zama?    Ita addu'a makami ce ga mumuni, tana kaɗe masifu da dama.    Idan san samu ne tun kafin ka/ki yi aure ya kamata a fara addu'a ga abokan rayuwa.  Misali ke mace  Yaa Allah Ubangiji sammai da kassai, sarkin sarakuna, Kai ne mai rahama da jin kai, kai ne mai biyan bukatun bayinka. Yaa Allah Kai kace mu roke za ka amsa mana.   Yaa Allah Ka ba ni miji nagari, wanda zai soni, ya kaunace ni, wanda zai kula da ni, wanda zai kyautata mun,wanda zai tsayamun duk tsanani duk wuya. Yaa Allah Ka dauwamar da soyayyata da kaunata a cikin zuciyar mijina. Yaa Allah Ka bani Ikon yin biyayya ga umarnin mijina, ka bani Ikon kyautata masa, ka sa in zama mace ta gari a gidan mijina, Ka azurta mu da zuriya Dayyiba, ka bani Ikon sauke hakkin mijina da ya’yana.  Yaa Allah ka shiryarmun da mijina hanya madaidaiciya, k

ƘALUBALE

ƘALUBALE ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Kowane abu ka sa a gaba dole ka fuskanci ƙalubale a ciki, walau ƙalubalen yazo ma ka cikin sauƙi walau akasin hakan. Ita rayuwa ba ka taɓa samun yanda ka ke so dari bisa dari, hakan ba zai sa ka karaya ba, amfanin ƙalubalen a rayuwa ka san yanda za ka kauce ma faruwar wani abu a gaba, kwatankwacin abinda ya faru. Da yawan mu na da saurin karaya akan abubuwa masu muhimmanci, musamman idan mun fuskanci ƙalubale. Maimakon mu tari ƙalubalen da hannu biyu, don mu san taya zamu warware sa, a'a sai mu yi kwallo da abun da mu ka dade muna muradi. Wani sa'in maimakon mu dubi ƙalubalen da mu ka fuskanta da idon basira, mu san hanyoyin da za mu bi mu warware su, mu san musababbin wanzuwar su, idan sun faru a gaba ta ya zamu fuskance su, a'a sai fara tunanin da sa hannun wane da wance, ko kuma mu bijire ma Allah. Mu riƙa tunanin kamar mu kadai Allah ya jarabta, mu kasa gode ma Sa akan sauran ni'imomin da ya yi mana. Sai mu b

ABIN DUNIYA

Dazu ne ina kallon wani shiri (tv show) akan relationships mai suna Home Affairs. Ana kiransu a waya ko a tura ma su saƙo ga masu neman shawara ko ga masu son bada ta su gudunmuwar. Su kan gayyato masana a bangaren zamantakewa don a tattauna da su akan wani maudu'i, su kuma bada shawara. Ana tsaka da shirin ne wani ya kira yana koken budurwarsa ta cika demanding, shi kuma yana sonta. Mutane da dama sun kira a shirin kowa da irin matsalarsa. Abinda ya ja hankalina na kawo batun anan ba komi bane face tabbas akwai mata masu irin wannan halayyar, wasu su na son samarin na su amma son abin hannun samarin ya rinjaya. Akwai wadanda su dama abin hannunka su ke so, sai bukatar su ta taso zasu neme ka. Irin su kuwa da dama cikin samarin idan su ka ga kiransu ko suka gansu sai gabansu ya fadi saboda fargabar abinda zasu fada kuma. Na taba fadar cewa shi fa namiji ba ATM ba ne da kowane lokaci ake tatsar kudi a wajensa, ko ATM akwai loton da yake sa "Unable to dispense cash "

GWAJI KAFIN AURE

GWAJI KAFIN AURE © AYEESH CHUCHU A yau zan sake taɓo wannan maudu'in wanda a waccan shekarar na taɓa yin rubutu makamancin hakan, sai dai a wannan karon akwai bambanci. Abinda ya ja hankalina na son yi bayani dangane da GWAJI KAFIN AURE sai yanda masoya suka dau duk mai wannan maganar a matsayin maƙiyinsu. A jiya ne wani ɗanuwa a kafa ta sada zumunta (Facebook) yake bayyana mun irin damuwar da yake ciki, a dalilin yace ma wadda yake tunanin za ta zama matarshi kuma uwar ya'yanshi su je GWAJI dan a tabbatar da lafiyar junansu. Buɗar bakinta “ Ashe wane ba ka sona baka yarda da ni ba? Idan har sai na je gwaji na gwammace in hakura da aurenka”. What nonsense is that? Ban san cewa har yanzu akwai ma su jahiktar gwaji kafin aure ba,gwajin nan ba karamin taimako yake ba wajen rage yaɗuwar cututtuka a tsakanin al'umma. A kiyasin shekarar (2016) Nijeriya ta zo ta biyu a cikin kasashen da ke fama da masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki (HIV/AIDS), sannan ta na ciki

FAHIMTAR JUNA

RASHIN FAHIMTAR JUNA © Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Rashin fahimtar juna na daya daga cikin ababen da ke kawo rikici a rayuwar zamantakewa tsakanin mata da miji, abokai da duk wata mu'amala da za ta haɗa ka da jama'a. Duk yanda kuke ƙaunar juna, idan har baku fahimci junanku ba to fa kun buɗe ƙofar gaba a tsakaninku. A nazarin da nayi na duba da kyau akan musabbabin mutuwar wasu daga cikin rayuwar Auren da na ji ko na gani. Ma'aurata da dama auren soyayya su ka yi da juna, amma daga an gama ɗokin auren sai matsaloli su fara kunno kai, a rasa dalilin da ke kawo rikici a tsakanin Ma'aurata wanda ya samo asali daga RASHIN FAHIMTAR JUNA da basu yi ba. Idan kuka fahimci junanku ba komi bane zai riƙa kawo hargitsi a tsakaninku ba. Shiyasa masana halayyar Dan Adam suka ce FAHIMTAR JUNA YAFI SO. Dalili kuwa da yawan ma'auratan da suka rabu da juna ba rashin SO yasa suka rabu ba, yawanci ma sai a tarar da suna matuƙar son junansu, amma rashin fahim

... LEDAR PURE WATER

… LEDAR PURE WATER © Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com “ Mata fa sunyi yawa kamar ledar pure water”. Zancen da za ka riƙa ji kenan daga bakunan jama'a yara da manya. Eh! Mata fa sunyi yawa banda ja, amma kuma samun wadda kake so, take sonka kaso ɗari sai an tona. Za ka taso kana da buri da tsari akan Macen da kake son aura. Sai lokaci ya yi kaga an sami canji wani abu ya canza ma raayin ka ko rayuwarka gaba daya da har ba ka iya cimma burinka akan irin macen da ka ke so. A da za ka riƙa tunanin ina son mace mai kaza da kaza, ta kasance cikin yanayin da ka ke so. Duk yanda ka kai ga wannan mafarkin bai zama lalle ya tabbata ba, ya na iya canzawa. Akwai hints ɗin da nake son kawowa akan mata, akwai lokacin da za ka ga macen da ta yi ma ka, kana tunanin ka yi dace, ka samu matar aure. Sai dai kash! Ita a wajenta ba haka bane ba. Ba ka cikin tsarin mazajen da ka ke so, tana da ta ta manufar akanka. Abu ne mai sauƙi ka samu macen da kake so, abu ne kuma mai wahala

WA ZAN AURA?

WA ZAN AURA???  ©Ayeesh Chuchu  ayeeshasadeeq2010@gmail.com   Wannan ce tambayar da ke zuwa a zukatan wadanda ba su yi aure walau mace ko namiji.    Muna cikin zamanin da competition ya yi yawa,saboda yawan competition ɗin sai ya zamo muna manta abubuwa ma su muhimmanci da ya kamata mu duba kafin a yi aure, burinmu dai ayi auren dan wance ko wane ya yi, ko dan sha'awa da makamantansu wanda at long last we end up in the wrong hand,ko kuma auren yaƙi zuwa ko'ina.     Aure ba abin wasa bane, ba kuma je ka dawo ba ne, ana Fatan idan anyi aure ya zama har abada,mutuwa kadai za ta raba wannan auren.   Rashin nazari da kuma tantance abinda ya dace da mutum a yayin neman aure babban matsala ce, yana daga cikin ummul aba'isin da mafi yawan auren da ake yi basu zuwa ko ina. Saboda rashin dace a cikin aure ba abinda bai haifarwa, yana iya illata rayuwar mutum gaba daya.  Da yawan mutane sun yi aure amma su na jin ina ma za su dawo basu da wannan auren saboda irin matsalolin da

SADARWA DA FAHIMTAR JUNA

SADARWA DA FAHIMTAR JUNA ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Idan mu ka yi duba ga yadda iyaye da kakanninmu suka yi rayuwar su cikin aminci da ƙaunar juna, akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin junansu. A lokacin babu wayar sadarwa, babu kafofin sada zamunta (social media platforms). Sai tsirarun ƴan boko da kan rubuta wasiƙa zuwa ga ƴan uwansu da masoyansu, duk da haka akwai fahimtar juna a tsakanin su. Ba kamar yadda zamantakewarmu ta taɓarbare ba, ga wayar ga kafofin sada zumuntar, duniya a tafin hannunmu amma duk basu kawo mana sauyi ba, sai ma ƙara taɓarbarewar zamantakewarmu. Da yawanmu mun ba waya mafi yawan lokutanmu, har ta kan sa mu manta da kawunan mu. Mun tsunduma tsulundum muna fira da abokanmu,mun manta da kawunan mu. Mun yi wancakali da sada zumunci a fili, waya ta dau hankalinmu. Duk yadda za mu kai ƙololuwa wajen faranta ran juna ta waya be kai na fili ba. Sai ku ga ma'aurata na zaune a waje ɗaya, wasu ma har da yaran su amma ba su da lokacin junansu

BA SOYAYYA KADAI AKE BUKATA BA

BA SOYAYYA KADAI AKE BUKATA A ZAMANTAKEWA BA ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Da yawan mutane na tunanin soyayya kadai su ke bukata a rayuwar zamantakewar su, har wasu kan kwatanta cewa "In dai wance ko wane na so na ai shikenan banda matsala". Ba ku da matsala ko? Shin soyayya kadai ku ke ganin ta ishe ku a zamantakewar ku? Akwai abubuwa muhimmai da ake bukata a zamantakewa, wanda idan babu su ba inda soyayya za ta je. Ita soyayya a matsayin tubali take a zamantakewa, da ita ne ake samun damar daura gini ta hanyar amfani da muhimman sinadaran ginin zai bukata. Akwai masoyan da su na matukar son juna, amma ba su girmama junansu, basu da fahimtar juna a tsakaninsu. Wa su kuma su na son juna, amma ba su farin ciki da junansu, ba ta inda soyayya ba ta zuwa, za ta iya sa ka so wanda ko a mafarki ba ka tunanin za ka so, amma kwatsam ka ji kayi dumu-dumu cikin soyayya. Matsaloli su yi ta faruwa a tsakanin ku, ku kasa magance su, wanda sun samo asali ne daga rashin b

RAYUWA

RAYUWA ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Burin kowane mutum a rayuwa ya samu jin dadi, ya ji ba shi da wata matsala,sai dai ita rayuwar ta mu kullum cike take da ƙalubale,daga wannan sai wancan, sai muyi ta tunanin ina ma mune wane, bayan wanen ma cewa yake ina ma ni ne wane, haka rayuwar take tafiya. Kowane mutum na rayuwa cikin wani mafarki da yake fatan ina ma zai tabbata, sai dai kadan ne ke cimma wannan mafarkin na su. Wasu sun rasa rayukan su wajen gwagwarmaya, wasu kuwa rayuwar ta zo ma su a bai-bai.A duk inda ka tsinci kan ka, har in kana son cimma burinka a rayuwa sai ka jajirce, ba wai za ka wa yi gari ka ga mafarkin ka ya cika ba, kana bukatar tsayuwa tsayin daka matuƙar kana son cimma Burin nan, sai kayi kamar ba ka son kanka.Sai ka jajirce kamar manomi, da idan ya shuka ce iri mai kyau a ƙasa mai kyau, za ka samu amfanin gona mai kyau. Shi ma manomi bawai daga shuka yake zuba ido ba, sai ka jajirce wajen zuba taki, ban ruwa, cire duk wani abu da ka iya barazan