Posts

Showing posts from December, 2017

AISHA AUGIE KUTA

Image
AISHA AUGIE KUTA An haifi Aisha Augie a garin Zaria, a ranar 11th April, 1980. Ɗiya ce ga marigayi   Sanata Adamu Baba Augie da Justice  Amina Adamu. Ta yi aure tana da yara uku maza.   Ta yi karatun digiri ɗinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta karanci fannin Mass Communication. Inda ta ke Masters ɗinta a bangaren Media and Communication a jami'ar Pan African University da ke Lagos.  Aisha Augie kwararriyar mai daukar hoto ce, wanda hakan ya samo asali daga kyautar kyamara (camera) da mahaifinta ya ma ta.  Abin mamaki ne a Nijeriya kuma yankin Arewa a ga mace na daukar hoto, sai dai a wajen Aisha Augie daukar hoto abu ne da ta dade tana sha'awar yi.  Aisha Augie mace ce da ta jajirce wajen ganin cigaban yara mata da kuma matasa baki daya. Ta kasance mai bada gudunmuwa a harkokin da suka shafi yara mata, dalilin hakan ne ma UNICEF ta rantsar da ita a matsayin "High Level Women Advocate on Education with a focus on girls and young women&qu

UMM ZAKIYYAH

Image
UMM ZAKIYYAH   An haifi Umm Zakiyyah a shekarar 1975, a Long Island dake ƙasar New York. Kafin a haife ta iyayenta mabiya addinin Kirista ne, Mahaifiyarta mai suna Delores Moore da mahaifinta Clark sun musulunta ne ana dauke da cikin Umm Zakiyyah. Ita ce ɗiya ta farko da aka haifa cikin musulunci a gidansu, inda aka sa ma ta suna "BAIYINAH". Umm Zakiyyah ta kashe mafi yawan lokuttan ta wajen rubuce-rubucen maƙala, rubutun waƙe a jaridu. Zamanta ɗaliba a jami'ar Emory da ke a Atlanta ta ƙasar Georgia. Ta sadaukar da mafi yawan lokuttan ta wajen rubuce-rubuce a jaridar da makarantar su ke fitarwa ta ɗalibai. A shekarar 1997 ta kammala karatunta na digiri, inda ta fito da kwalin digiri a bangaren BA. Elementary Education. Daga nan ta fito a matsayin Marubuciya, Malama kuma mai bada darussa akan al'amuran rayuwa. A shekarar 2001 ne ta fitar da littafinta na farko mai sunan IF I SHOULD SPEAK, littafin da ya ƙara fito da baiwar da Allah ya yi ma Umm Zakiyyah a banga

LALE MARHABIN

Image
Lale marhabin da zuwan wannan rana Ranar da garin Makka ya haskaka Ranar haihuwar fiyayyen halitta  Ɗaha Musɗafa baban Zarah Duk mai son Ɗaha ya so ahalinSa Miji ga Khadijatu, angon Aishatu Amini ga Abubakar Saddiqu Siriki ga Aliyu ɗan abi Talib Zuwan Ɗaha duniya ta haskaka Ya kawo mana hanyar shiriya  Domin tsira a gobe ƙiyama Muna ma su Haske da walwali Ɗaha ya zo mana da littafi  Wanda anka kira da Qur'ani Saƙo daga sarkin sarakuna Allah mabuwayi gagara misali   Ɗaha mai kira zuwa ga tauhidi  Domin tsira  a hawan siraɗi Ɗaha masoyi ga al'ummarsa Ya roƙi salama ga al'ummarsa Mu so Manzonmu mai dubun falala  Kyawawan halayen Ɗaha sun yawaita  Duk wanda ya yi koyi da shi ya rabauta  Kowa ya ƙi Ɗaha ya kafirta  Lale marhabin da wannan rana  Ranar haihuwar fiyayyen halitta  Ɗaha Musɗafa baban Al-Qaseem Kaka ga Hassan da Hussaini Ya Allah ka dado tsira  Ga Manzonka mai farar aniya Don shi anka ƙagi duniya Ɗa ga Aminatu da Abdallah  Sallallahu a

MARUBUCIYA HAFSAT ABDULWAHEED

Image
MATAN AREWA HAJ. HAFSAT ABDULWAHEED An haifi Hajiya Hafsat Abdulwaheed a jihar Kano, an haife ta a ranar 5th May, 1952. Tayi karatun firamare ɗinta a ' Shahuci Primary School' dake a Kano. Daga nan ta wuce sakandiren ƴan mata ta Provincial Girls School wanda aka sauya ma suna zuwa Shekara Girls Secondary School. Tayi aure a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida ( 1966 ),ta auri Muhammad Ahmad Abdulwaheed, tana zaune a jihar Zamfara. Ta na da ƴaƴa, daga cikin ƴaƴanta akwai Kadaria Ahmad fitacciyar ƴar jarida. Marubuciya ce dake rubutunta cikin harshen Hausa. Hajiya Hafsat ta fara rubutu ne tun tana makarantar firamare, inda ta samu damar ƙarbar lambobin yabo daga British Council. A shekarar 1970 Haj. Hafsat ta shiga gasar Rubutu da kamfanin maɗaba'ar wallafa littatafai ta Northern Nigerian Publishing Company (NNPC) ta gudunar, inda ta shigar da labarinta mai suna 'SO ALJANNAR DUNIYA'. Wanda ta rubuta shi tun tana aji biyar na firamare. Labarin SO AL