RAYUWA

RAYUWA

©Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Burin kowane mutum a rayuwa ya samu jin dadi, ya ji ba shi da wata matsala,sai dai ita rayuwar ta mu kullum cike take da ƙalubale,daga wannan sai wancan, sai muyi ta tunanin ina ma mune wane, bayan wanen ma cewa yake ina ma ni ne wane, haka rayuwar take tafiya.
Kowane mutum na rayuwa cikin wani mafarki da yake fatan ina ma zai tabbata, sai dai kadan ne ke cimma wannan mafarkin na su. Wasu sun rasa rayukan su wajen gwagwarmaya, wasu kuwa rayuwar ta zo ma su a bai-bai.A duk inda ka tsinci kan ka, har in kana son cimma burinka a rayuwa sai ka jajirce, ba wai za ka wa yi gari ka ga mafarkin ka ya cika ba, kana bukatar tsayuwa tsayin daka matuƙar kana son cimma Burin nan, sai kayi kamar ba ka son kanka.Sai ka jajirce kamar manomi, da idan ya shuka ce iri mai kyau a ƙasa mai kyau, za ka samu amfanin gona mai kyau. Shi ma manomi bawai daga shuka yake zuba ido ba, sai ka jajirce wajen zuba taki, ban ruwa, cire duk wani abu da ka iya barazana ga rayuwar shukarsa, da Hakan yake samun amfanin gona mai yawa da inganci.
Haka rayuwar mu take a matsayinmu na matasa, sai mun shuka alheri za mu girbi alheri,akasin alheri kuwa mun san abin da ka iya biyo baya.
Da yawanmu mun fi so a ce dare ɗaya mun cimma burikanmu wanda hakan ba mai yiwuwa bane, sai mun tashi haiƙan.
Muna da wani abu matasan Arewa Da yawanmu na da wata baiwa ta daban, amma mun kasa amfani da wannan baiwar, mun dogara kacokam ga gwamnati. Duk yadda gwamnati ta so kyautata mana ba za ta taɓa daukar dukkanmu aiki ba.
Amfanin wannan baiwar kenan, mu fiddo da ita mu amfani al'umma. Wani baiwar zane-zane gare shi, wani ƙare-ƙare, wani sarrafa abubuwa, kowane da inda yafi bajinta. Mu fito da bajintar mu fara da kadan.
Babu babbar illa ga mutum da ta wuce na ya samu mutuwar zuci, ba zai taba iya taɓuka abin arziki ba, kar mu bari zuciyoyin su mutu, mu taimaki kanmu da nahiyarmu.
Kana da ƙafafu, idanu da hankali amma kana zaune zaman banza,shin ka kuwa godewa Allah da wannan ni'imar? Muyi duba na tsanaki wani bai da ƙafa, wani kunne, wani ido amma hakan be hana shi neman na kansa ba.
Babu nakasashshe sai wanda zuciyarsa ta mutu, mu tashi tsaye mu cimma burikanmu.
Mu sa a ran mu zamu iya, komin wuya komin dadi.
A lokutta da dama idan na samu kaina cikin bacin rai, na kan ji kamar in daina duk wasu abubuwa da nake, amma idan nayi tunanin wani ko wata na can na fatan ina ma su ne? Sai inji kwarin gwiwa, ko kuma in yi tunanin akwai wadanda ba su samu damar da na samu ba, su kuma su ce mi?
Rayuwar nan dama ce, idan har muka bari damar da mu ke da ita ta kuɓuce mana, haƙiƙa muna cikin da na sani.

Indo Shatu🌸

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa