LEFE

LEFE 
©AYEESH CHUCHU 
  Lefe dai kaya ne na al’ada da ango ke haɗawa matar da zai aura akai gidansu kafin aure (a tawa fahimtar). 

   A wannan zamanin da mu ke ciki lefe yayi sanadiyar hana aure da dama. Wasu saboda ba’a haða lefen yanda su ke so ba. Yawancin matsalar tsegumin lefe na tasowa ne daga dangin amarya. 

 Daga ranar da aka kawo lefen budurwa gidansu, tofa maganar lefen nan ya zama hot talk a cikin unguwa da gari baki daya, ba kamar dai idan an haða duk abubuwan da yarinyar da danginta ke bukata. 

 Sai ka ji ana cewa “Ai Indo ta yi goshi wallahi wannan lefe haka”. 

 “kai yarinya mai farin jini”. 

“Lallai wannan angon na ji dake irin wannan ubansun kaya da ya lafto”. 

 Da dai makamanta zance irin haka. Idan kuwa aka yi rashin sa’a lefen be haɗu yanda ake so ba, sai ku ji ana cewa “Amma dai wannan angon anyi matsiyaci”. 

“abin haushi ko yar super nan ta yayi be saka ko guda ba, babu Dubai Lace bare wata babbar shadda”. 

 “Yoo abinda atampopin ma duk na dubu uku ne da yan dubu biyu”. 

“Ke ni har atampa a yadi (aqaqira)  na gani ciki”. 

 “tab Lallai Indo baki yi sa’a ba, wai kinga lefen Lantana kuwa? Abin ba’a cewa komi”. 
 Daga nan sai a fara zuga yarinya, itama kuma idan  son abin duniya ya ma ta yawa shikenan ta hau dokin tsiya. Wasu ma fa iyayen mata ne ke zuga su saboda shegen buri da suke cusa ma ya’yansu. 
  BABBAR ANNOBA

Babbar annoba da ke addabar mata yanzu be wuce duk wadda aka kawo ma lefe ba, ta dauka da waya tana tura ma kawaye ta kafar social media. 

Wasu saboda birgewa da zaqewa har haða hoton lefen ake da na ta ana yawo da shi group-group, dp-dp, profile pictures, instagram ga lefen wance wane. Nan za ku ji Comment iri-iri duk nan da sunan birgewa ce. 

  Toh wallahi ki sani yar uwa ba birgewa ba ne face kauyanci da jahilci, ni sam be burge ni. Duk wadda na ga tana haka dauka nike bata san abinda take ba. 

Don idan kina tunanin Kin birge an maki lefe na gani na fada sai kuma kiga na wa ta wanda ya linka naki shikenan fa sai ki raina wanda akai ma ki, to ina amfanin hakan?

Wai ba ki tunanin wa ta ta lefen da taga kina talla da shi, za ta fara kishi dake. Ba dukka wadanda kika tura mawa ne zasu ji dadi ba har su taya ki celebrating har zuci. Wata dama take nema ta lalubo miji irin naki. Kinga idan taga bata samu ba, ayam! Sai ta faɗa ma naki ko ta tsiya ko ta arziki. 

  Wata za ta bi duk hanyar da za ta bi wajen ganin ta lalata auranki, ina wannan maganar ne daga abinda ya faru da wasu. 

Ni idan ba a Nijeriya ba banga inda ake tafka irin wannan kauyancinba. Ni rashin aji da sanin ciwon kai na dauki abun. 

  Ni anawa tunanin idan har ana son kawo karshen tsegumi akan lefe a daina kawo shi. Bance kar ayi ma yarinya lefe ba, dan wasu mazan kam It takes them forever suyi ma matansu dinki, wasu daga na lefen nan sai a dau tsayin shekaru ba maganar yi mata sutura. 

  Amma idan anyi lefeb ango ya adana gidanshi, idan an kawo ma matarka ka nuna ma ta khalas!

 Ba ruwanku da tsegumi. Na san wasu zasu ce na cika kilibibi ra’ayina ne nike faða. 

  Idan har iyayen amarya zasu rika sa wannan dokar da an zauna lafiya, an rage yawan magulmata masu haddasa husuma a dalilin lefe.

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa