FAHIMTAR JUNA

RASHIN FAHIMTAR JUNA
© Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Rashin fahimtar juna na daya daga cikin ababen da ke kawo rikici a rayuwar zamantakewa tsakanin mata da miji, abokai da duk wata mu'amala da za ta haɗa ka da jama'a.
Duk yanda kuke ƙaunar juna, idan har baku fahimci junanku ba to fa kun buɗe ƙofar gaba a tsakaninku.
A nazarin da nayi na duba da kyau akan musabbabin mutuwar wasu daga cikin rayuwar Auren da na ji ko na gani.
Ma'aurata da dama auren soyayya su ka yi da juna, amma daga an gama ɗokin auren sai matsaloli su fara kunno kai, a rasa dalilin da ke kawo rikici a tsakanin Ma'aurata wanda ya samo asali daga RASHIN FAHIMTAR JUNA da basu yi ba.
Idan kuka fahimci junanku ba komi bane zai riƙa kawo hargitsi a tsakaninku ba. Shiyasa masana halayyar Dan Adam suka ce FAHIMTAR JUNA YAFI SO.
Dalili kuwa da yawan ma'auratan da suka rabu da juna ba rashin SO yasa suka rabu ba, yawanci ma sai a tarar da suna matuƙar son junansu, amma rashin fahimtar juna ya kawo cikas! A zamantakewar su.
Duk irin son da kuke ma juna walau mata da miji, saurayi da budurwa, yara da iyaye idan babu wannan fahimtar junan kamar kun dasa fulawa (flower ) ne babu ruwa. Mi kenan? Fulawar nan za ta mutu, haka soyayyarku za ta dushe a cikin zukata. Mostly, mu kan kasa fahimtar mi abokan zamanmu ke so, taya zamu fahimci dalilinsu na yin wani abu da ke bata mana rai.
Ko a tsakanin iyaye idan babu fahimtar juna tsakanin iyayen da yaransu za a sami communication gab, wanda yaran kan yi tunanin iyayensu basa ƙaunarsu, iyaye su yi tunanin yaransu basu daraja su. Hakan ya samo asali ne daga rashin fahimtar junansu.
Da yawan ma'aurata daga lokacin da suka yi aure ba su da lokacin zama da junansu su tattauna wata matsala a tsakaninsu wadda suke ganin ta a matsayin barazana ga rayuwar Aurensu. Ba wai sai a lokacin samartaka ake zuwa taɗi ba, a'a da Aurenku ma za ku zauna kuyi hira. Ku jaddada ma juna ababen da ke zukatanku. Ko matsala kuka samu ku zauna ku warware ta a tsakaninku ta nan zaku fahimci junanku. Ku zauna ku tattauna abubuwan da zasu ƙara inganta rayuwar aurenku, ku yi kokarin yin fatali da communication gab da ke tsakaninku.
Idan har za ku fahimci junanku sai kun san wadannan keys din :
Wanene abokin/abokiyar rayuwata? Mi ya/ta fi so? Mi ya/ta ke bukata? Mi ya/ta ke nema?
Idan kuka fahimci wadannan keys din a tsakaninku to tabbas za ku fahimci junanku ta yanda ko da daya ya kuskuro za ku fahimci dalilin hakan.
Hakan take a bangaren iyaye ma, yana da kyau ku ware ma yaran ku lokaci na musamman da za ku rika tattaunawa a tsakaninku ta hakan ne za ku fahimci su waye yaran ku? Da abubuwan da suke bukata a rayuwarsu. Rashin zama da su kan haifar da tarin matsaloli.
Zama dasu kan haifar da shaƙuwa a tsakaninku ta hanyar da duk irin matsalar da suke fama da ita kune mutane na farko da zasu sanarmawa.
Mu daure mu sa fahimtar juna a tsakaninmu dan mu samu alaƙa mai ƙarfi.

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa