ABIN DUNIYA

Dazu ne ina kallon wani shiri (tv show) akan relationships mai suna Home Affairs.
Ana kiransu a waya ko a tura ma su saƙo ga masu neman shawara ko ga masu son bada ta su gudunmuwar.
Su kan gayyato masana a bangaren zamantakewa don a tattauna da su akan wani maudu'i, su kuma bada shawara.
Ana tsaka da shirin ne wani ya kira yana koken budurwarsa ta cika demanding, shi kuma yana sonta. Mutane da dama sun kira a shirin kowa da irin matsalarsa.

Abinda ya ja hankalina na kawo batun anan ba komi bane face tabbas akwai mata masu irin wannan halayyar, wasu su na son samarin na su amma son abin hannun samarin ya rinjaya. Akwai wadanda su dama abin hannunka su ke so, sai bukatar su ta taso zasu neme ka.

Irin su kuwa da dama cikin samarin idan su ka ga kiransu ko suka gansu sai gabansu ya fadi saboda fargabar abinda zasu fada kuma.
Na taba fadar cewa shi fa namiji ba ATM ba ne da kowane lokaci ake tatsar kudi a wajensa, ko ATM akwai loton da yake sa "Unable to dispense cash " ko "out of service ".
To ki fahimta mana a matsayinki na mace, idan namiji mai bayarwa ne tun farko za ki gane cewa shi mai bayarwa ne, haka nan kuma idan dunqulallen hannun gare sa.
Kyautatawa ce fa tsakaninku dan ya ba ki kudi ko ya siya ma ki wani abu, babu inda aka ce dole ne,sai dai mi? Ita kyauta na karfafa soyayya.

Idan ya ba ki ki karba idan be ba ki ba kar ki roka.
  Sai dai kuma maza idan kuna da halin yi kuyi, idan ba ku da shi ku hakura. Amma ka sani yanzu soyayya ta zama kamar gasa, wani a shirye yake da ya kashe ma budurwarka ko nawa ne dan ya samu koda rabin son da take ma ka ne, kai kuma kana nan ka tsaya sanya.
Mata nada raunin, wata abu qanqani sai ya juyar ma ta da tunani, ta kasa gane abinda take so. Sai kaga cikin qanqanin lokaci ta juya ma baya saboda wani.
Tsaya ki ji yar uwa kar ki bari abun duniya ya rude ki, ki saki reshe ki kama ganye,wani ba sonki yake ba tsakaninsa da Allah ba wani abu na ki yake so, ke daga yanda yake kashe ma ki kudi haduwar farko ba dangin Iya ba na Baba haba! Ai ya dace ki dau haske. Idan kwadayi ya shiga kan ki shikenan kin halaka.
Idan dama kuma gold digger ce abin nema ya samu.
Allah ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, ya tsare mana mutuncinmu, ya hada mu da abokan zama nagari.

Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com
ayeeshchuchu.blogspot.com

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa