... LEDAR PURE WATER

LEDAR PURE WATER
© Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Mata fa sunyi yawa kamar ledar pure water”. Zancen da za ka riƙa ji kenan daga bakunan jama'a yara da manya.
Eh! Mata fa sunyi yawa banda ja, amma kuma samun wadda kake so, take sonka kaso ɗari sai an tona.
Za ka taso kana da buri da tsari akan Macen da kake son aura. Sai lokaci ya yi kaga an sami canji wani abu ya canza ma raayin ka ko rayuwarka gaba daya da har ba ka iya cimma burinka akan irin macen da ka ke so.
A da za ka riƙa tunanin ina son mace mai kaza da kaza, ta kasance cikin yanayin da ka ke so. Duk yanda ka kai ga wannan mafarkin bai zama lalle ya tabbata ba, ya na iya canzawa.
Akwai hints ɗin da nake son kawowa akan mata, akwai lokacin da za ka ga macen da ta yi ma ka, kana tunanin ka yi dace, ka samu matar aure.
Sai dai kash! Ita a wajenta ba haka bane ba.
Ba ka cikin tsarin mazajen da ka ke so, tana da ta ta manufar akanka.
Abu ne mai sauƙi ka samu macen da kake so, abu ne kuma mai wahala kafin ka fuskanci ina ta dosa, abu ne mai wahala kafin ka raba ta da hange-hange,abu ne mai wahala ya zama kai kadai ta ke zantawa da shi.
Za ka samun macen da ka ke so amma ka rasa gane kanta, Walau ba ka san yadda za ka gabatar da kanka bane. Akwai wasu matakai da namiji dole yasan dasu idan ya tunkari mace.
Kowane ɗan Adam na da tsarinsa.
Ka na soyayya da ita, ta na nuna ma tana sonka while a zuciyarta ba haka ba ne. Bawai sonka ne ba ta yi ba a'a, baka taka matakin da take so ba.
Akwai matakai huɗu da zan taɓo
TSARIN HALITTA : wata tafi son namiji fari, dogo, gajere, baƙi, kakkaura, siriri dss. Toh fa idan tana cikin masu son baƙin namiji, dogo, kakkaura ka zo ga ka fari, siriri, gajere. You've failed. Duk yanda ka kai da iya tsari za ta ji cewa akwai inda ba ka cika ba.
Idan ba ta da wani a hannu za ta amince da kai, amma fa daga zarar ta samu irin wanda take so, za ka fara rasa kanta.
TSARIN HIRA DA HIKIMA : Kowacce mace na da yanda take jin dadin hira da masoyinta, tana da abubuwan da take da interest a kansu, idan ya zamo mai yawan karance-karance ce ko kallace-kallace, girke-girke toh fa idan ba firar su ka yi ma ta ba, ana samun matsala duk iya ƙololuwa da kai wajen iya hira. Kai ko Tom & Jerry ne abin da take so jefo shi cikin hirarku, nan za ka ga inda tafi zaƙewa hirar da ba ka tunanin za ku yi sai ka ga kunyi har lokaci ya shige. Ka fahimci miye burinta kuna tattaunawa a kansu duk yanda ta kai ga fara ƙinka, za ka samu gurbi a zuciyarta, coz you’re someone that support and stand by her side, you’ve been like a shoulder for her to lean on to laugh and cry.
TSARIN MI TAFI SO: Kowacce mace da irin tsarin da take so mijinta ya kasance. Wata na son mai aure, mara aure, yaro, dattijo, tazuru, tsoho. Toh fa anan idan ka fado cikin wanda ba ta so za’a iya samun akasi.
Hakanan a sana'a ma, arziki, burinka a rayuwa duk wadanda idan basu dace da tsarin da take so ba, ba lallai bane ku sasanta.
TSARIN GASA : Shin kai kadai ne wanda take so? Ka cika abubuwan da take son mijin aurenta da su? Idan har aka samu bambanci cewa akwai masu sonta ba kai kadai bane, kana da abokan hamayya, kuma a cikinsu akwai wanda ya cika abubuwan da tafi so kai ba ka cika su ba, za ta iya barin ka ta koma ma sa.
Na kawo waɗannan matakan ne saboda matsalolin da wasu mazan kan fuskanta a wajen mata da sunan yaudara.
Shawara ta anan kafin a zurfafa a soyayya, a fara neman zabin Allah, a nemi iyaye kuma idan har sun ba mutum go ahead, sun sanya albarka No any obstacles that can block your way Sai ƙaddara.
Kowacce mace na da dalilin da yasa take sonka.
Wata tana sonka saboda kudinka, kyawunka, wata dan tana son yin auren an matsa ma ta a gida, wata saboda ba ta da wanda za ta so, wata kuma saboda ba ka cika qualities din dream guy dinta ba, wata dai don ka zama reserve ne idan na hannu ya kubce kana nan a ajiye, wata a matsayin abokin da take amfanuwa da shi ta ajiye ka, wata ɗan uwa ta dauke ka, wata kuma saboda ba ta iya cewa ba ta sonka take tare da kai, wata kuma dan ta ganka dan shila take son ka, wata kuma tana sonka ne dan ka cika matakan da take so, wata kuma hakanan take jin sonka.
Duk wadannan sai mutum ya lura a wane mataki yake, mata sun wuce tunanin da ka ke. Kowace na da taste ɗin ta da kuma yanda ake tunkararta, idan ka kuskuro tun farko shikenan an sami matsala, za ka rasa ina ta dosa ne. Sai kayi da gaske tukunna.
Mace na son a nuna ma ta kauna, soyayya, kulawa, lallashi, dss.

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa