UMM ZAKIYYAH

UMM ZAKIYYAH

  An haifi Umm Zakiyyah a shekarar 1975, a Long Island dake ƙasar New York.

Kafin a haife ta iyayenta mabiya addinin Kirista ne, Mahaifiyarta mai suna Delores Moore da mahaifinta Clark sun musulunta ne ana dauke da cikin Umm Zakiyyah.

Ita ce ɗiya ta farko da aka haifa cikin musulunci a gidansu, inda aka sa ma ta suna "BAIYINAH".

Umm Zakiyyah ta kashe mafi yawan lokuttan ta wajen rubuce-rubucen maƙala, rubutun waƙe a jaridu.

Zamanta ɗaliba a jami'ar Emory da ke a Atlanta ta ƙasar Georgia. Ta sadaukar da mafi yawan lokuttan ta wajen rubuce-rubuce a jaridar da makarantar su ke fitarwa ta ɗalibai.

A shekarar 1997 ta kammala karatunta na digiri, inda ta fito da kwalin digiri a bangaren BA. Elementary Education.

Daga nan ta fito a matsayin Marubuciya, Malama kuma mai bada darussa akan al'amuran rayuwa.

A shekarar 2001 ne ta fitar da littafinta na farko mai sunan IF I SHOULD SPEAK, littafin da ya ƙara fito da baiwar da Allah ya yi ma Umm Zakiyyah a bangaren rubuce-rubuce.

Littafinta na IF I SHOULD SPEAK ya zagaye ƙasar United Kingdom da Australia, tana daya daga cikin wadanda littatafansu suka zama "bestsellers" a  United States.

Littafin na ta dai ya samu sharhi daga mujallu da jaridu irinsu Muslim Magazine da Muslim Link Newspaper.

Abin mamaki littafinta na ɗaya daga cikin littatafan da Dr. Robert D. Crane yayi sharhi akansu, ya kuma yaba da kwazon Umm Zakiyyah.

A shekarar 2008 ta samu kyautar karramawa daga  Muslim Girls Unity Conference Distinguished Authors Award.

Umm Zakiyyah na daga cikin marubuta mata da littatafan su suka kewaye wasu daga cikin ƙasashen duniya irinsu United Kingdom, Australia, Egypt, Pakistan, Malaysia, Uganda, Nigeria, United Arab Emirates, Saudi Arabia, Bahrain da India.

Ta rubuta littatafai da dama irinsu His other wife, Reality of Submission, The abuse of Forgiveness da sauran su.

Ayeesha A. Sadiq
12-12-2017
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa