ILIMIN ƳA MACE

MUHIMMANCIN ILIMI, AIKI KO SANA’AR ĎIYA MACE 
©Ayeesh Chuchu 
Musulunci cikakkiyar hanya ce dake cika kamalar mutum. Duk wani aiki da musulmi zai gabatar matukar da kyakkyawar niyya zai samu ladan aikinsa. 
Babu addinin da ya ba mace ‘yancinta kamar addinin musulunci. Addinin musulunci ne ya yi adalci a tsakanin hakkin mace da na namiji. Hakanne ma ya sa addinin islama be bambamce tsakanin mace da namiji ba wajen neman ilimi. 

Addini musulunci addini ne na masu ilimi, wanda ya kwadaitar da neman ilimi. Ba’a turo annabawa ba face dan su isar da sakon Allah SWT na ilimi, kamar yadda yazo a cikin ALQUR’ANI mai girma in da Allah SWT Ya bayyana dalilin aiko da Manzo. 

[Suratul Baqara aya ta 151 

﴿ﻛَﻤَﺂ ﺃَﺭْﺳَﻠْﻨَﺎ ﻓِﻴﻜُﻢْ ﺭَﺳُﻮﻻً

ﻣِّﻨﻜُﻢْ ﻳَﺘْﻠُﻮﺍْ ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢْ ﺀَﺍﻳَــــٰـــﺘِﻨَﺎ

ﻭَﻳُﺰَﻛِّﻴﻜُﻢْ ﻭَﻳُﻌَﻠِّﻤُﻜُﻢُ ﭐﻟْﻜِﺘَــــٰـــﺐَ

ﻭَﭐﻟْﺤِﻜْﻤَﺔَ ﻭَﻳُﻌَﻠِّﻤُﻜُﻢ ﻣَّﺎ ﻟَﻢْ

ﺗَﻜُﻮﻧُﻮﺍْ ﺗَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ﴾

 “Kamar yadda Muka aika Manzo a cikinku, daga gare ku, yana karanta ayoyinMu a gare ku kuma yana tsarkake ku, kuma yana sanar da ku Littafi da hikima, kuma yana sanar da ku abin da ba ku kasance kuna sani ba”.] 

Hakan na nuni da cewa addinin musulunci addini ne na neman ilimi. 
Haka Allah SWT Yace “Ka ce, Ashe waɗanda suka sani, suna daidaita da waɗanda ba su sani ba? Masu hankali kawai ke yin tunani”

﴿ﻗُﻞْ ﻫَﻞْ ﻳَﺴْﺘَﻮِﻯ ﭐﻟَّﺬِﻳﻦَ

ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ ﻭَﭐﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻟَﺎ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻮﻥَ

ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻳَﺘَﺬَﻛَّﺮُ ﺃُﻭْﻟُﻮﺍْ ﭐﻟْﺄَﻟْﺒَــــٰـــﺐِ﴾

 [Suratul Zumar aya ta 9].
Suratul Faɗir aya ta 28 

﴿ﺇِﻧَّﻤَﺎ ﻳَﺨْﺸَﻰ ﭐﻟﻠَّﻪَ ﻣِﻦْ

ﻋِﺒَﺎﺩِﻩِ ﭐﻟْﻌُﻠَﻤَــــٰۤـــﺆُﺍْ ﺇِﻥَّ ﭐﻟﻠَّﻪَ

ﻋَﺰِﻳﺰٌ ﻏَﻔُﻮﺭٌ﴾

“Malamai  kawai ke tsoron Allah daga cikin bayinSa. Lalle Allah Mabuwayi ne, Mai gafara”. 
Gaba ɗaya cikin waɗannan ayoyin babu inda aka bambance cewa namiji kadai ke da damar neman ilimi. An  nuna muhimmancin ilimi ga rayuwar Dan Adam. 
Haka Annabin Rahama SAW ya ce “Neman ilimi farilla ga dukkan musulmai (mace ko namiji).” [Ibn Majah ne ya ruwaito hadisin]. 
Akwai hadisin Annabi SAW da ke cewa “Ku nemi ilimi ko da daga nan zuwa birnin sin ne”. [ al-Bazzar ya ruwaito shi daga cikin littafin Al-Musnad]

A wani hadisin da Muslim ya ruwaito, Annabi SAW ya ce “Duk wanda ke hanyar tafiya neman ilimi, Allah zai saukake ma sa hanyar sa ta shiga aljanna”. 
Hakan na nuni da cewa dukkan waɗannan ayoyi da hadisai na magana ne akan neman ilimi, inda ba su bambamce tsakanin mace da namiji ba. Neman ilimi wajibi ne ga kowa. 

An karɓo daga Abu Sa’id Al-khudri ya ce wasu mata sun zo wajen Annabi SAW, su ka ce “Ya Manzon Allah, maza sun wuce mu a fagen neman ilimi, ka sama mana  rana ɗaya ce da za a rika koyar da mu”. Anan Manzon Allah SAW ya ware masu rana ɗaya yana sanar da su dokokin Allah SWT da kuma basu shawarwari. [Bukhari ne ya ruwaito wannan hadisin]. 
Uwa kamar makaranta ta ke  idan ta samu wadataccen ilimi tabbas al’umma za su ilmantu. 

Tabbas addinin musulunci yaba mace damar shiga harkokin rayuwa matukar za ta kare martabarta. 

Yazo a tarihi cewa mata na halarta yaqunan musulunci inda suke taimakawa wajen kula da waɗanda aka raunana, sannan wasu daga cikinsu na shiga cikin yakin. 

A khalifanci Sayyidina Umar ya wakilta Shaffa Bint Abdullah a mai kula da yankin BAZAAR.. 
Mace na da damar yin kasuwanci dan ta kashe kudi matukar za ta nemi halalinta.

Musulunci ya shar’anta cewa indai mace na da aure mijinta ne ke da alhakin kula da ita ta hanyar biya ma ta bukatunta. 

Haka idan ba ta da aure iyayenta ko wasu makusanta na ta ke da wannan alhakin. 
Duk da haka ba’a tauye ta ba wajen neman na kanta. Kamar yadda Nana Khadija ta zamo shahararriyar yar kasuwa a garin Makkah, wadda ta sadaukar da dukiyarta wajen dafa ma Annabi SAW da kuma ɗabbaqa addinin islama. 
Kenan dai mace za ta iya yin aiki ko sana’a dan ta tallafawa rayuwar ‘yan uwanta da mabukata matukar ta kiyaye dokokin Allah.

Babu wani bambanci tsakanin mace da namiji a matsayinsu na mutane wadanda suke a matsayin wakilai a doron kasa wadanda aka halitta dan dan su bautawa Allah. Mace da namiji basu da bambanci a wajen bautawa Allah. 

Mace da namiji suna da ‘yancin a musulunce. 
A tsarin musulunci mace na iya aiki a cikin gidanta ko a waje, tana iya taimakawa mijinta wajen biyan wasu bukatu na gida, ko ta taimaki’ yan uwa musulmai. 

Mace nada ‘yancin dai-dai da namiji a fanni kasuwanci da sana’a. Tana da karfi da iko kamar da namiji a fanni aiki, kasuwanci dss. 

Musulunci ya halalta neman na kai  tsakanin musulmai ba tare da an tauye mace ko namiji ba. 

Kamar yadda yazo a cikin suratul Najm aya ta 39 “kuma mutum ba shi da kome face abin da ya aikata”. 

 Wato dai wanda yake mutumin kirki, Allah Ya san shi. Kada ku dinga tsarkake kanku da bakunanku domin neman girma ko domin neman wani abu daban. 
A cikin suratul Nisa’ aya ta talatin da biyu tayi magana akan ‘yan mace da namiji wajen neman halal [Maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mata suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku roki Allah daga falalarSa. Lalle Allah Ya kasance ga dukkan kome, Masani]. 
[Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da yaudara, face idan ya kasance daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kanku… Suratul Nisa’i 29].

Haka kuma akwai hadisin da Bukhari ya ruwaito “Da mutum ya yi roko ko bara, da ya gwammace ya dauki igiya ya daura itace akansa ya siyar”. 
Wadannan ayoyi da hadisai suna nuna mana muhimmancin neman halal inda ba’a bambamce tsakanin mace ko namiji ba. 
Malamai sunyi ittifaki cewa mace za ta iya yin aiki a wajen da ba’a haramta ma ta sanya hijabi ba, zata kare mutunci da martabar ta ba tare da an cutar da ita ba. Ba’a yarda ta keɓe ita kadai da wanda ba muharraminta ba a boye, amma idan a fili ne hakan ba laifi matukar ta suturta jikinta, ta kame harshenta daga munanan zantuka. 

Dan haka masu ganin kamar ina gogayya da shari’a ne sun min qage kuma sun zalunce ni, da wadanda ke ganin ina goyon bayan yahudanci da Yahudawa ku sani kun min mummunan fahimtar, sai Allah ya saka min dan bani goyon bayan Yahudawa da yahudanci. 

Burina a kullum al’umma su fahimci irin yancin da addinin islama yaba mace, wanda wasu daga ciki suka tauye mata saboda dubun jahilci da kuma ganin rauninta. 
Ina nan akan bakana na cewar ilimi da aikin ‘ya mace nada matukar muhimmanci ga rayuwar al’ummar musulmi. 

Mata nawa ne ke zarya gidajen marayu da sansanin gudun Hijira dan kai tallafi. 
Akwai gidan marayun da naga jerin sunayen mata cikin wadanda ke kawo tallafi sun fi maza yawa. Saboda mata nada rauni da tausayi. 
Ina da damar fadar ra’ayina a Facebook, duk wanda post dina be mashi ba na roke da Allah ya tsallake ya bar min kayana. 
Ina godiya ga wadanda suka bini Inbox suka ci zarafi na. Jazakumullahu khair. 

Ban rike ku ba, amma duk wadanda suka kira mun kalmar kafirci ina rokon Allah ya bi mun haqqina akansu. 
‘Yar uwarku a musulunci 

Nana Aa’ishah 

Bissalam

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa