WA ZAN AURA?

WA ZAN AURA??? 

©Ayeesh Chuchu 
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

  Wannan ce tambayar da ke zuwa a zukatan wadanda ba su yi aure walau mace ko namiji. 

  Muna cikin zamanin da competition ya yi yawa,saboda yawan competition ɗin sai ya zamo muna manta abubuwa ma su muhimmanci da ya kamata mu duba kafin a yi aure, burinmu dai ayi auren dan wance ko wane ya yi, ko dan sha'awa da makamantansu wanda at long last we end up in the wrong hand,ko kuma auren yaƙi zuwa ko'ina.

    Aure ba abin wasa bane, ba kuma je ka dawo ba ne, ana Fatan idan anyi aure ya zama har abada,mutuwa kadai za ta raba wannan auren.

  Rashin nazari da kuma tantance abinda ya dace da mutum a yayin neman aure babban matsala ce, yana daga cikin ummul aba'isin da mafi yawan auren da ake yi basu zuwa ko ina. Saboda rashin dace a cikin aure ba abinda bai haifarwa, yana iya illata rayuwar mutum gaba daya. 

Da yawan mutane sun yi aure amma su na jin ina ma za su dawo basu da wannan auren saboda irin matsalolin da suke fuskanta a rayuwar auransu. 

WA ZAN AURA??? 

Tambaya ce mai muhimmanci da ya kamata duk wani mai niyyar yin aure ya tambayi kan sa. Akwai qualities ɗin da addinin musulunci ya shar’anta ga mace ta gari da namiji na gari. Wadanda su ya kamata mu fara dubawa wajen neman aure ba wai kyale-kyale da san ran mu ba. 

No hurry in life, Mu natsu wajen zaben abokan rayuwar mu, kada san zuciya ya kai mu ya baro mu, mu kyautata niyyar mu sai Allah ya taimake mu. 

A duk sanda mutum zai nemi aure ya sa aranshi cewa zai yi wannan auren ne dan cika umarnin Allah madaukakin sarki da kuma ɗabbaka sunnar Annabi S.A.W, nemi zabin Allah wato istikhara sai Allah ya zamo ma jagora a cikin lamuran neman auren ka. 

Da yawan matasa ba su damu da neman zabin Allah ba, burin su dai tunda su na son abu to sai sun yi. 

ISTIKHARA tun farko ya kamata mutum ya yi ta, kafin soyayyar abu ya yi nisa cikin zuciyarka. Misali ka ga yarinyar da ka ke so, kafin ka faɗi ma ta ya kamata ka fara neman zabin Allah, haka ke ma mace kafin ki amshi tayin soyayyar shi ya kamata ki nemi zabin Allah, kada babbar mota, kuďi, katon mansion, kyau ya rude ki. Ki cire wadannan abubuwan ki sa a ranki cewa zabin Allah ki ke nema, kuma kina son yin aure ne dan neman lada wajen Ubangijinki ba dan kawarki ko yar uwarki tayi aure ba. 

Wasu na aure ne dan ganin shekarunsu sun ja, gida an matsa ma su su yi aure,abokansu sunyi aure, wasu dan ba su da masoya, dan su sami mai taimakonsu ko dan wata bukata ta kansu. Mutum ya cire duk wadannan abubuwan ya sa a ran shi cewa zai yi ne dan Allah dan kuma ya cika rabin addininsa. 

Da yawa iyaye da al’umma na taimakawa wajen ingiza wadanda basu yi aure ba zuwa wrong hand, saboda yawan maganganun su. 

Kira na ga wadanda ba su yi aure ba su natsu kada Surutun mutane yasa su yi auren je ka nayi ka. 

Toshe kunnuwanku ku natsu wajen zaben abokan zama, tunda dai ba wanda zai zauna ma ku a gidajen aurenku. 

Ba wai ina nufin mata ko maza ku bijire ma iyayenku ba, a’a ku yi amfani da tausasan kalamai wajen nusar da su illar uzzurawa mutum wajen neman aure, na san ba za’a rasa wanda ka san ko ki ka san irin haka ya faru da shi ko ita. 

Da yawan zawarawa da mu ke da su duk irin wannan matsalar ce ta rashin sanin wa zan aura?

Yawaitar mutuwar aure na damuna, sannan ya kara sa tsoro a zukatan yan mata da Samari na rashin sanin takamaimai wa za su aura.

 

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa