ADDU'A MAKAMIN MUMINI

ADDU'A MAKAMIN MUMINI

©Ayeesh Chuchu 

Ina matasa marasa aure? 

  Kun taɓa kawowa a ranku cewa addu'a babban makami ne  a yayin da ka/ki ke neman aboki ko abokiyar zama? 

  Ita addu'a makami ce ga mumuni, tana kaɗe masifu da dama. 

  Idan san samu ne tun kafin ka/ki yi aure ya kamata a fara addu'a ga abokan rayuwa. 

Misali ke mace 

Yaa Allah Ubangiji sammai da kassai, sarkin sarakuna, Kai ne mai rahama da jin kai, kai ne mai biyan bukatun bayinka. Yaa Allah Kai kace mu roke za ka amsa mana. 

 Yaa Allah Ka ba ni miji nagari, wanda zai soni, ya kaunace ni, wanda zai kula da ni, wanda zai kyautata mun,wanda zai tsayamun duk tsanani duk wuya. Yaa Allah Ka dauwamar da soyayyata da kaunata a cikin zuciyar mijina. Yaa Allah Ka bani Ikon yin biyayya ga umarnin mijina, ka bani Ikon kyautata masa, ka sa in zama mace ta gari a gidan mijina, Ka azurta mu da zuriya Dayyiba, ka bani Ikon sauke hakkin mijina da ya’yana. 

Yaa Allah ka shiryarmun da mijina hanya madaidaiciya, ka azurta shi azurtawa mai amfani, ka bashi Ikon sauke hakkinmu da ya rataya akan shi. 

Yaa Allah idan ka kaddara ma mijina da kara aure Ubangiji Allah ka bashi Ikon yi adalci a tsakaninmu, Yaa Allah ka saukaka zafin kishi a tsakaninmu Ka dawwamar da zaman lafiya a tsakaninmu. Yaa Allah Ka da Ka ba abokiyar zamana (kishiya) Ikon cutar da mu, Kada Ka ba mu Ikon cutar da ita. Yaa Allah ka haða kawunanmu. 

  ‘yar uwa ki lizimci irin wannan addu'ar a duk lokacin da kika yi sallar nafila kika kai goshonki kasa (sujjada) ba wai sai kinyi aure ba, matsaloli sun fara kunno ma ki kai sannan za ki fara rokon Allah, tun kafin su zo za ki fara yaqarsu da addu’a. 

Haka kaima dan uwana daure ka rika kwatankwacin wannan addu'aaddu'ar dan dacewa da abokiyar zama tagari. 
Ubangiji Allah ya hada mu da abokan zama nagari. 

Amin

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa