Posts

Showing posts from May, 2019

ALFANU DA RASHIN ALFANUN BESTY

ALFANU DA RASHIN ALFANUN BESTY A TSAKANIN JINSI BIYU ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Bestie dai kalma ce da ake amfani da ita wajen nuna kimar mutum da irin matsayin da ya/ta ke da shi a zuciya, wanda a Hausance akan ce "Amini ko Aminiya", wato dai mutumin da kuke kut-kut. Duk mutumin da za ka ba amana, ka fadawa sirrin da ke ranka, ba tare da wani dar ba. Ko kuma mutumin da a duk lokacin da wata matsala ko damuwa ta taso ma daya daga cikin su, su kan zauna su tattauna dan warware matsalolinsu, su na masu aminta da juna. Hakan na faruwa a tsakanin jinsin namiji da namiji, mace da mace ko kuma dai wanda yanzu ake yi a zamanance wato abota tsakanin mace da namiji. A wannan zamani da mu ke ciki an zamanantar da abun, musamman fitowar kafofin sada zumunta da kuma makarantun gaba da sakandire, inda za a samu akwai cudanya tsakanin mace da namiji. Duk kuwa da cewa a addinance da gargajiyance babu wata alaĆ™a tsakanin mace da namiji da ta wuce soyayya ta aure. Sai d

WANI LOKACI

WANI LOKACI #ayeeshchuchuwrites Bayan wani dan lokaci, radadin ya kan rage radadi. A hankali mu kan gane dalilin faruwar wasu ababen. Mu kan fahimci dalilin da yasa suka yi hakan. Sai dai mi? Mu kan koyi cewa ba kowa ne a rayuwar ya kan zo ya tsaya a cikinta ba har abada! A wasu lokuttan su kan zo ne kamar taurarin cikin littafin rayuwarmu. Ba su zo dan komi ba, sai dan su koya mana wasu ababe a rayuwa, su sauya yanayin rayuwarmu,  har wani sa'in ma su koya mana yanda zamu so kanmu. Har mu san muhimmancin da muke da shi. Irin wadannan taurari abu ne mai wahala mu samu makwafinsu a lokacin zasu bar mu a cikin littafin rayuwarmu. Amma mi? Abu mafi muhimmancin a nan shi ne dole mu bar su su tafi, koda kuwa bamu son su tafi din. Daga farko abin zai mana ciwo, zai nukurkushe mu.. Irin nukurkusar da za ta sa mu kasa bambamce tsakanin rana da dare. Irin radadin da ko ina mu ka shiga yana biye da mu, yana tuna mana lokuttan da muka yi a tare masu dadi. Wanda har ya kan sa mu rink