LALE MARHABIN

Lale marhabin da zuwan wannan rana

Ranar da garin Makka ya haskaka

Ranar haihuwar fiyayyen halitta 

Ɗaha Musɗafa baban Zarah

Duk mai son Ɗaha ya so ahalinSa

Miji ga Khadijatu, angon Aishatu

Amini ga Abubakar Saddiqu

Siriki ga Aliyu ɗan abi Talib

Zuwan Ɗaha duniya ta haskaka

Ya kawo mana hanyar shiriya 

Domin tsira a gobe ƙiyama

Muna ma su Haske da walwali

Ɗaha ya zo mana da littafi 

Wanda anka kira da Qur'ani

Saƙo daga sarkin sarakuna

Allah mabuwayi gagara misali

 

Ɗaha mai kira zuwa ga tauhidi 

Domin tsira  a hawan siraɗi

Ɗaha masoyi ga al'ummarsa

Ya roƙi salama ga al'ummarsa

Mu so Manzonmu mai dubun falala 

Kyawawan halayen Ɗaha sun yawaita 

Duk wanda ya yi koyi da shi ya rabauta 

Kowa ya ƙi Ɗaha ya kafirta 

Lale marhabin da wannan rana 

Ranar haihuwar fiyayyen halitta 

Ɗaha Musɗafa baban Al-Qaseem

Kaka ga Hassan da Hussaini

Ya Allah ka dado tsira 

Ga Manzonka mai farar aniya

Don shi anka ƙagi duniya

Ɗa ga Aminatu da Abdallah 

Sallallahu alaihi wassalam

Ayeesh Chuchu 

12-03-1439Hijra

01-12-2017



Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa