Posts

Showing posts from October, 2017

WA ZAN AURA?

WA ZAN AURA???  ©Ayeesh Chuchu  ayeeshasadeeq2010@gmail.com   Wannan ce tambayar da ke zuwa a zukatan wadanda ba su yi aure walau mace ko namiji.    Muna cikin zamanin da competition ya yi yawa,saboda yawan competition ɗin sai ya zamo muna manta abubuwa ma su muhimmanci da ya kamata mu duba kafin a yi aure, burinmu dai ayi auren dan wance ko wane ya yi, ko dan sha'awa da makamantansu wanda at long last we end up in the wrong hand,ko kuma auren yaƙi zuwa ko'ina.     Aure ba abin wasa bane, ba kuma je ka dawo ba ne, ana Fatan idan anyi aure ya zama har abada,mutuwa kadai za ta raba wannan auren.   Rashin nazari da kuma tantance abinda ya dace da mutum a yayin neman aure babban matsala ce, yana daga cikin ummul aba'isin da mafi yawan auren da ake yi basu zuwa ko ina. Saboda rashin dace a cikin aure ba abinda bai haifarwa, yana iya illata rayuwar mutum gaba daya.  Da yawan mutane sun yi aure amma su na jin ina ma za su dawo basu da wannan auren saboda irin matsalolin da

SADARWA DA FAHIMTAR JUNA

SADARWA DA FAHIMTAR JUNA ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Idan mu ka yi duba ga yadda iyaye da kakanninmu suka yi rayuwar su cikin aminci da ƙaunar juna, akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin junansu. A lokacin babu wayar sadarwa, babu kafofin sada zamunta (social media platforms). Sai tsirarun ƴan boko da kan rubuta wasiƙa zuwa ga ƴan uwansu da masoyansu, duk da haka akwai fahimtar juna a tsakanin su. Ba kamar yadda zamantakewarmu ta taɓarbare ba, ga wayar ga kafofin sada zumuntar, duniya a tafin hannunmu amma duk basu kawo mana sauyi ba, sai ma ƙara taɓarbarewar zamantakewarmu. Da yawanmu mun ba waya mafi yawan lokutanmu, har ta kan sa mu manta da kawunan mu. Mun tsunduma tsulundum muna fira da abokanmu,mun manta da kawunan mu. Mun yi wancakali da sada zumunci a fili, waya ta dau hankalinmu. Duk yadda za mu kai ƙololuwa wajen faranta ran juna ta waya be kai na fili ba. Sai ku ga ma'aurata na zaune a waje ɗaya, wasu ma har da yaran su amma ba su da lokacin junansu

BA SOYAYYA KADAI AKE BUKATA BA

BA SOYAYYA KADAI AKE BUKATA A ZAMANTAKEWA BA ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Da yawan mutane na tunanin soyayya kadai su ke bukata a rayuwar zamantakewar su, har wasu kan kwatanta cewa "In dai wance ko wane na so na ai shikenan banda matsala". Ba ku da matsala ko? Shin soyayya kadai ku ke ganin ta ishe ku a zamantakewar ku? Akwai abubuwa muhimmai da ake bukata a zamantakewa, wanda idan babu su ba inda soyayya za ta je. Ita soyayya a matsayin tubali take a zamantakewa, da ita ne ake samun damar daura gini ta hanyar amfani da muhimman sinadaran ginin zai bukata. Akwai masoyan da su na matukar son juna, amma ba su girmama junansu, basu da fahimtar juna a tsakaninsu. Wa su kuma su na son juna, amma ba su farin ciki da junansu, ba ta inda soyayya ba ta zuwa, za ta iya sa ka so wanda ko a mafarki ba ka tunanin za ka so, amma kwatsam ka ji kayi dumu-dumu cikin soyayya. Matsaloli su yi ta faruwa a tsakanin ku, ku kasa magance su, wanda sun samo asali ne daga rashin b

RAYUWA

RAYUWA ©Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Burin kowane mutum a rayuwa ya samu jin dadi, ya ji ba shi da wata matsala,sai dai ita rayuwar ta mu kullum cike take da ƙalubale,daga wannan sai wancan, sai muyi ta tunanin ina ma mune wane, bayan wanen ma cewa yake ina ma ni ne wane, haka rayuwar take tafiya. Kowane mutum na rayuwa cikin wani mafarki da yake fatan ina ma zai tabbata, sai dai kadan ne ke cimma wannan mafarkin na su. Wasu sun rasa rayukan su wajen gwagwarmaya, wasu kuwa rayuwar ta zo ma su a bai-bai.A duk inda ka tsinci kan ka, har in kana son cimma burinka a rayuwa sai ka jajirce, ba wai za ka wa yi gari ka ga mafarkin ka ya cika ba, kana bukatar tsayuwa tsayin daka matuƙar kana son cimma Burin nan, sai kayi kamar ba ka son kanka.Sai ka jajirce kamar manomi, da idan ya shuka ce iri mai kyau a ƙasa mai kyau, za ka samu amfanin gona mai kyau. Shi ma manomi bawai daga shuka yake zuba ido ba, sai ka jajirce wajen zuba taki, ban ruwa, cire duk wani abu da ka iya barazan