MARUBUCIYA HAFSAT ABDULWAHEED

MATAN AREWA

HAJ. HAFSAT ABDULWAHEED

An haifi Hajiya Hafsat Abdulwaheed a jihar Kano, an haife ta a ranar 5th May, 1952.

Tayi karatun firamare ɗinta a 'Shahuci Primary School' dake a Kano. Daga nan ta wuce sakandiren ƴan mata ta Provincial Girls School wanda aka sauya ma suna zuwa Shekara Girls Secondary School.

Tayi aure a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida (1966),ta auri Muhammad Ahmad Abdulwaheed, tana zaune a jihar Zamfara.
Ta na da ƴaƴa, daga cikin ƴaƴanta akwai Kadaria Ahmad fitacciyar ƴar jarida.

Marubuciya ce dake rubutunta cikin harshen Hausa. Hajiya Hafsat ta fara rubutu ne tun tana makarantar firamare, inda ta samu damar ƙarbar lambobin yabo daga British Council.

A shekarar 1970 Haj. Hafsat ta shiga gasar Rubutu da kamfanin maɗaba'ar wallafa littatafai ta Northern Nigerian Publishing Company (NNPC) ta gudunar, inda ta shigar da labarinta mai suna 'SO ALJANNAR DUNIYA'. Wanda ta rubuta shi tun tana aji biyar na firamare.
Labarin SO ALJANNAR DUNIYA ya zo na biyu.

Hajiya Hafsat Abdulwaheed ita ce mace ta farko da ta fara rubutu a harshen Hausa cikin mata marubuta da ake dasu a yankin Arewa.

Ta rubuta littatafai da dama fiye da talatin , inda ta samu damar fitar da guda biyar daga ciki.
Kadan daga cikinsu sun haɗa da So Aljannar Duniya, Ƴardubu Mai Tambotsai, Nasiha Ga Ma'aurata, Namijin Maza Tauraron Annabawa, sai littafinta na waƙe a cikin harshen Turanci mai taken Ancient Dance.

Hajiya Hafsat mace ce jaruma kuma ƴar gwagwarmaya mai rajin kare hakkin mata (woman right activist).

Tana daga cikin matan da su ka taɓa fitowa takarar muƙamin gwamna a yankin arewacin Nijeriya.

Haƙiƙa tana cikin Matan Arewa da su ka kafa tarihi a cikin mata.

Tauraruwa ce, a bar koyi ga matan Arewa.

Source : Wikipedia

Rubutawa
Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com
1-12-2017

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa