ƘALUBALE

ƘALUBALE
©Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Kowane abu ka sa a gaba dole ka fuskanci ƙalubale a ciki, walau ƙalubalen yazo ma ka cikin sauƙi walau akasin hakan.
Ita rayuwa ba ka taɓa samun yanda ka ke so dari bisa dari, hakan ba zai sa ka karaya ba, amfanin ƙalubalen a rayuwa ka san yanda za ka kauce ma faruwar wani abu a gaba, kwatankwacin abinda ya faru.
Da yawan mu na da saurin karaya akan abubuwa masu muhimmanci, musamman idan mun fuskanci ƙalubale. Maimakon mu tari ƙalubalen da hannu biyu, don mu san taya zamu warware sa, a'a sai mu yi kwallo da abun da mu ka dade muna muradi. Wani sa'in maimakon mu dubi ƙalubalen da mu ka fuskanta da idon basira, mu san hanyoyin da za mu bi mu warware su, mu san musababbin wanzuwar su, idan sun faru a gaba ta ya zamu fuskance su, a'a sai fara tunanin da sa hannun wane da wance, ko kuma mu bijire ma Allah. Mu riƙa tunanin kamar mu kadai Allah ya jarabta, mu kasa gode ma Sa akan sauran ni'imomin da ya yi mana. Sai mu butulce ma Sa.
Kowa da irin ƙalubalen da yake fuskanta a rayuwa, idan har ba za mu tsayu tsayin daka ba wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa haƙiƙa rayuwa za ta zo mana a birkice.
Ƙalubale kan iya zo mana a fannoni da dama na rayuwa walau a neman ilimi, sana'a, aiki, zamantakewa da sauran fannoni na rayuwa. Dole mu jajirce wajen tarar matsalolinmu ba wai mu guje ma su ba, rungumar su za mu yi ƙam-ƙam domin mu nema masu mafita.
Akwai mutanen da kan gujewa matsalolin su, su kasa fuskantar ƙalubalen da ke fuskantarsu a tunanin su guje ma matsalolin shi zai sa su yi rayuwa mai cike da inganci.
Guje ma matsalolinmu ba shi ne warwarar ƙalubale ba, a'a mu rungumi matsalarmu ta nan zamu san yadda za mu warware ta.
  Dole ne mu natsu wajen fuskantar ƙalubalen rayuwa, mu yi tunani mai zurfi sannan mu jajirce.
Mu yarda da yanda abubuwa ke kasancewa, dan ba zamu iya guje ma su ba don tun fil azal a tsare su ke, ba zamu iya canza komi ba yanda mu ke so. Wasu hakanan zamu bar su su cigaba da tafiya sai dai mu san taya zamu fuskancesu.
Da yawan mutane kan ɗora laifin wanzuwar matsalolin su ga abokan huldarsu. Ko da tunanin ka da hangenka ya nuna ma dai-dai ne, su na da hannu cikin matsalolin ka, hakan ba zai ba ka lisisin nuna su a matsayin masu kawo ma cikas a rayuwa, bi su ta ruwan sanyi ka warware matsalolin ka.
Muna da matsalar kwatanta rayuwar mu da ta wasu, bayan kowa da irin tsarin halittarsa da rayuwarsa akwai bambanci tsakanin mutane. Kar kayi ƙoƙarin kwaikwayon wane, yi ƙoƙarin zamo wa abin da ka ke son zama. Idan kana tunanin wane duk abin da yasa a gaba yana samu amma a kullum kai cikin rashin samun nasara ka ke, kayi duba na tsanaki wane ma da inda yake fuskantar ƙalubale da ba lallai ne ka sani ba.
Sai ka ga kuna sana'a ɗaya da wane amma wane yafi ka samun nasara, kuna aji ɗaya da wane amma wane yafi ka gane karatu, kuna aiki ɗaya da wane amma wane yafi ka samun ɗaukaka, kar kayi baƙinciki, yi iya ƙoƙarin ka, ka jajirce ka kuma miƙa ma Allah lamuranka. Babu wanda yafi wani, sai wanda yafi wani tsoron Allah.

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa