GWAJI KAFIN AURE

GWAJI KAFIN AURE

©AYEESH CHUCHU

A yau zan sake taɓo wannan maudu'in wanda a waccan shekarar na taɓa yin rubutu makamancin hakan, sai dai a wannan karon akwai bambanci.
Abinda ya ja hankalina na son yi bayani dangane da GWAJI KAFIN AURE sai yanda masoya suka dau duk mai wannan maganar a matsayin maƙiyinsu.
A jiya ne wani ɗanuwa a kafa ta sada zumunta (Facebook) yake bayyana mun irin damuwar da yake ciki, a dalilin yace ma wadda yake tunanin za ta zama matarshi kuma uwar ya'yanshi su je GWAJI dan a tabbatar da lafiyar junansu.
Buɗar bakinta “Ashe wane ba ka sona baka yarda da ni ba? Idan har sai na je gwaji na gwammace in hakura da aurenka”.
What nonsense is that? Ban san cewa har yanzu akwai ma su jahiktar gwaji kafin aure ba,gwajin nan ba karamin taimako yake ba wajen rage yaɗuwar cututtuka a tsakanin al'umma.
A kiyasin shekarar (2016) Nijeriya ta zo ta biyu a cikin kasashen da ke fama da masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki (HIV/AIDS), sannan ta na cikin ƙasashen da ma su fama da cutar amosarin jini (sicklecell) suka yawaita.
Shin ba ma taimaki kanmu da kanmu ba? Wajen ganin an daƙile yawaitar wannan cuta. Adadin jariran da ake haihuwa dauke da cutar sikila a kullum ƙara yawaita su ke saboda jahilci na al’ummarmu, musamman kauyuka da suka dau masu dauke da cutar sikila a matsayin wasu mutane ma su dauke da shafar Jinnu, saboda irin yanayin da su ke riskar kansu na yau da lafiya gobe babu.
Kirana ga masu neman aure su tabbatar da sun yi gwaji kafin su yi aure, dan tabbatar da lafiyar junansu da kuma na ƴaƴansu.
Yanzu an cigaba an daina aure cikin duhun kai. Cututtuka sun yawaita waɗanda Cututtuka ne masu yaɗuwa a tsakanin mutane (communicable diseases).
A binciken da masana lafiya suka yi, sun gano cutar hanta (hepatitis) ita ma tana yaɗuwa a tsakanin mutane ta hanyar zufa, tari, numfashi da sauransu.
Shin ba ku san cewa jikinmu amana ne a gare mu ba? Shin ba ma tashi tsaye dan kare lafiyarmu da ta iyalenmu ba?
Mafita anan muyi GWAJI KAFIN AURE dan tabbatar da lafiyar abokan zamanmu.
Shawarata anan kowanne ya je asibiti yayi gwaji dan tabbatar da lafiyarshi (Rigakafi yafi magani).
Sanin yanayin da mutum ke ciki shi zai sa ya nemi maganin cutar da ke damunsa tun kafin ta kai wani mataki da ba ta jin magani.
Ita cuta ba mutuwa ba ce, sai Allah ya dau ran mai lafiya ya bar mara lafiya. Kowacce mutuwa akwai sanadinta.
Baa saukar da cuta ba sai da aka saukar da maganinta, kada sanin kana dauke da wata cuta ya sa ka karaya, ka fidda rai da rayuwa, mutuwa lokacine da ita. Cigaba da rayuwarka yanda ka ke a da, ba tare da nuna damuwa ko tsangwamar kai ba.
Idan har ana son kaucewa broken hearts kafin aure, a daure daga sa'ar da ka ga wadda ka ke so, ka gabatar da kanka, ku fahimci Status ɗin junanku tun kafin tafiya tayi nisa, a zo a sami matsala, gara tun farko kusan Status ɗin junanku wanda idan kunyi na’am da za ku iya auren juna, Shikenan. Idan kuma kuna ganin akwai cutuwa kunga tun kafin ku yi nisa cikin soyayya kunyi ma kanku rigakafin broken hearts.
A yanzu na kasa tantance wane jinsi ne yafi kawo matsala wajen GWAJI KAFIN AURE, kwanakin baya akwai wadda ta zo man da makamanciyar irin wannan matsalar ta wancan bawan Allah.
Ya kamata mu hankalta musan cewa duniya fa ta cigaba, kullum sabbin fasahohi ƙara bayyana suke, ba zamu ci gaba da zama kara zube ba, cikin jahilci.
It's high time we stop all this nonsense about CBC (Complete Blood Count).
Ku je kuyi gwaji dan tabbatar da lafiyarku, yin gwaji baya nufin rashin yarda da juna (zargi), a’a dan dai ayi rayuwa mai cike da aminci da lafiya.
Hakan zai taimaka ainun wajen ganin an rage yaɗuwar waɗannan cututtuka da ke yaɗuwa a tsakanin al’umma, wasu ta hanyar auratayya.
Dan neman shawara ko gyara a tuntuɓe ta ayeeshasadeeq2010@gmail.com
Ma'assalam

Comments

  1. Salam, Malama Allah Ya saka maki da mafificin alheri. Malama ban ji kin yi maganar cutar Sikila ba a rubutun ki. Ni a fahimta ta, daya-dayar hanyar magance cutar Sikila shine gwaji kafin Aure. Mutane har yanzu sun kasa samun wayewa game da wannan al'amari na Sikila.

    ReplyDelete
  2. Gaskiya haka ne. Har yanzu akwai duhun kai dangane da gwajin genotype. Na taba magana akan gwajin genotype ɗin, In Shaa Allah zan duba shi sai inyi posting. Nagode kwarai

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa