IYAYE MATA

IYAYE MATA

Iyaye su ne mafi kusa da yaransu, wadanda su ka san shige da ficen yaransu saboda su ke zaune da su gida fiye da iyaye maza. Iyaye mata su ne mafi kusanci da yara musamman ma ɗiya mata. Wasu iyaye mata za a samu sun zama tamkar ƙawayen juna a cikin ƴaƴansu mata, har ta kai mutum zai iya shigowa gida ya ƙasa bambance uwa da yaran ta.
Wasu iyayen mata na ganganci wajen watsi da al'amuran yaransu musamman mata. Ba su damu da su zama abokan ƴaƴansu ba, ta hakan hanya mafi sauki da uwa za ta janyo ƴaƴanta kusa da ita, ya zama ko matsala gare su itace ta farko da zasu fara tunkara dan ta warware ma su matsalolinsu, ita ce abokiyar shawararsu. Idan Uwa ba ta jawo ƴaƴanta a jiki ba wa zai ma ta? Musamman yara mata sai sun zama tamkar kawayen juna ta hakan ne za ta yisaurin gane matsalolinta,idan kuna da kusanci sosai kun zama tamkar abokan juna da ɗiyarki kafin ta je wani waje neman shawara wajen ki za ta fara zuwa neman shawararki.
Amma watsi da yaran da iyaye mata kanyi na daga cikin ummul aba'isin bara gurbi acikin al'umma. Wasu za su fada wata matsala amma tunaninsu ba abinda mahaifiyarsu za ta iya yi, sai su tafi wajen abokai nan zasu fadi matsalar su, idan aka yi sa'a abokan na kwarai ne shine fa zasu samu shawara ta kwarai, idan kuma akasin hakan ne daga nan fa rayuwar yaran ta gurbata.
Wace irin uwa ce ɗiyarki har ta dau ciki ba ki sani ba, kuna zaune gida daya. Watau ba ta san lokacin da ta kan yi periods dinta ba, ba ta san lokacin siyan sanitary pads na ɗiyar ba.
Wannan ganganci ne babba, ya kamata iyaye mata su sa ido akan ƴaƴansu shige da ficensu. Su zauna su yi fira da su, su saki jiki dasu dan a samu shaƙuwa a tsakani.

Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani, ya ƙara shiryar da mu hanya madaidaiciya.

darussanrayuwa2017@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa