SAI MAZA SUN CANZA

SAI MAZA SUN CANZA!

© AYEESH CHUCHU
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

A wannan zamanin da mu ke ciki rayuwar aure ta zama wata irin bahaguwar rayuwa, wadda akan kasa gane kanta a wasu lokuttan.
Maza kune Allah ya ba ragamar jan akalar gidajenku, ku ne shuwagabanni masu mulkin alƙaryar gidajensu. Hakan ya zama abin tutiya, nuna iko da isa a cikin alƙaryarku. Har wasu kan yi amfani da wannan damar wajen aiwatar da mulkin kama karya a cikin gidajensu.
Dukkanku za ku tsayu gaban Allah a ranar gobe ƙiyama kuna q nannaɗe acikin sarƙa har sai kun tsira daga kun sauke haƙƙin da Allah ya rataya a wuyanku na iyalanku.
Ba'a ba ku wannan mulkin ba face dan kun kasance marasa rauni,amma kadan daga ciki ne ke kwatanta adalci a tsakanin su da iyalansu.
A wannan zamanin ne da mu ke ciki miji da Allah ya daura ma nauyin iyalinshi be damu da su ba, kullum cikin fita yake ya nemo amma hakan be sa ya sauke nauyin da ya rataya akansa ba. Wani ya tafi ya bar matar da ɗawainiyar ƴaƴansu, ita ce cinsu ita shansu, itace suturarsu, itace daukar nauyin karatunsu. Wallahi tallahi ba ku bi na bashin rantsuwa naga mata sama da goma wadanda ke daukar nauyin iyalansu ba dan mazajensu basu da shi ba, wadanda na gani ra'ayul aini kenan banda wadanda na kan ji, ko na karanta a zaurukan sada zumunta (social media platforms).
Irin kisan da maza ke ma mata abin ba'a cewa komi, kisan mummuƙe sai an gama gana masu azaba tukunna, sun gama tagayyara. Mi yasa mafi yawan masu fama da hawan jini, ciwon zuciya duk mata sun fi yawa a wannan zamanin. Macen yaran ta basu fi biyu ba sai a ji ta da hawan jini duk A DALILIN DA NAMIJI.
Dan mi mata yanzu suka yi yawa wajen neman aikin yi, wajen yin sana'o'i duk dan su rufa kansu da ƴaƴansu asiri. Saboda kadan daga cikin maza ne ke sauke nauyin da ya rataya a wuyan su.
Yanzu har ta kai namiji matuƙar ya san cewa matarshi na aiki ko sana'a to fa kakarsa ta yanke saƙa, idan ta ci sa'a ya ajiye dawa da gero to ta godewa Allah, sauran kayan cefane ta ji dasu.
Wani kuwa idan yau matar ta siyo gishiri to shi kenan ya bar ta da siyan gishiri kenan har illa MashaaAllahu. Shiyasa akwai lokuttan da ban ganin laifin matan da su na da shi ba su taimakawa mazansu,saboda mazan ne sun zama abinda suka zama.
A gabana wani ke fadin matuƙar matarshi ta na aiki to shi fa ba zai iya ci gaba da yin suturar yaransu ba, abinci kuma idan ya ajiye kayan masarufi ya rage na ta ta inganta abincin.
Miyasa da ba'a samun yawaitar matsaloli a zamantakewar iyali? Saboda maza sun tsayu tsayin daka wajen kyautata ma iyalansu. Su kuma mata suna kokarin yin biyayya ga mazajensu.
Amma yanzu wasu mazan sun yi kwallo da hakkin da ya rataya a kawunansu, don mi za a ga laifin mata? Tabbas kowane bangare da irin gudunmuwar da yake takawa, maza bashin da ku ka dauka ne ku ke biya.
Akwai azzaluman mazan da idan aka ga irin abubuwan da suke yi kare ba zai ci ba.
Namiji shi ke da iko da gidan shi, matukar be yi abinda zai kawo ɓaraka a tsakanin shi da matarshi ba, ko ta ƙi to ta so dole tayi biyayya a gare shi matukar hakan be kauce ma umarnin Allah ba.
Maza ba'a hana ku ƙara aure ba, amma idan za ku yi ku tabbatar zaku yi adalci don shine musababbin abinda ke tada mata hankali, wasu mazan dama basu sauke hakkokin iyalansu ba, sannan su zo suna hanƙilon ƙara aure tsakani fa da Allah akwai zalunci, matukar mazaje ba zasu gyara halayensu a matsayin su na shuwagabanni ba to fa mata ba zasu canza ba.

AYEESH CHUCHU
23-11-2017

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa