SADARWA DA FAHIMTAR JUNA

SADARWA DA FAHIMTAR JUNA
©Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Idan mu ka yi duba ga yadda iyaye da kakanninmu suka yi rayuwar su cikin aminci da ƙaunar juna, akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin junansu.
A lokacin babu wayar sadarwa, babu kafofin sada zamunta (social media platforms).
Sai tsirarun ƴan boko da kan rubuta wasiƙa zuwa ga ƴan uwansu da masoyansu, duk da haka akwai fahimtar juna a tsakanin su. Ba kamar yadda zamantakewarmu ta taɓarbare ba, ga wayar ga kafofin sada zumuntar, duniya a tafin hannunmu amma duk basu kawo mana sauyi ba, sai ma ƙara taɓarbarewar zamantakewarmu.
Da yawanmu mun ba waya mafi yawan lokutanmu, har ta kan sa mu manta da kawunan mu.
Mun tsunduma tsulundum muna fira da abokanmu,mun manta da kawunan mu. Mun yi wancakali da sada zumunci a fili, waya ta dau hankalinmu. Duk yadda za mu kai ƙololuwa wajen faranta ran juna ta waya be kai na fili ba.
Sai ku ga ma'aurata na zaune a waje ɗaya, wasu ma har da yaran su amma ba su da lokacin junansu, sai a samu ɗaya na magana ɗaya kuma hankalin na ga duniya a tafin hannu.
Maimakon wannan kimiyar ta sa mu zama kusa da juna sai ta ƙara nisantar da mu, idan motar haya ka hau dan tafiya, sai mu hau har mu sauka ba mu kalli na gefen mu ba, mun maida hankalinmu ga wayar mu. Hakan ta kasance a gidajen biki, suna, ma'aikatu, masana'antu,makarantu mun zame kuramen ƙarfi da yaji.
Rayuwa duk sai ta sauya, iyaye basu da lokacin yaran su haka ma yaran sai dai a haɗu ta duniya a tafin hannun ka a gaisa.
Shiyasa kakanninmu su ka fi mu iya mu'amala da mutane, suna da fahimtar juna a tsakanin su.
Za ka samu mata da miji suna tattauna matsalolinsu, za ka samu iyaye da yaransu su na fira ana raha, hakan na ƙara fahimtar juna da soyayya shiyasa duk yanda yaran su ka kai da wayau iyayen na hankalce da su. Banda yanzu da yawancin iyaye basu san wainar da yaransu ke toyawa ba.
Nayi mamaki da na ji labarin yarinyar da tayi ciki har sai da za ta haihu iyayen su ka fahimci tana da ciki, wane irin sakaci ne wannan? Ƴaƴa fa amana ne a hannun iyaye, da taimakon Allah da naku iyaye shi zai tarbiyantar da yara.
Masoya kuma sun maida soyayyar su kacokam a zaurukan sada zumunta, idan fada suka yi anan za su shirya, haduwa da juna ya zama abu mai wahala a tsakanin su.
Kar ku yi tunanin yawan kiran waya, ko aika saƙonni shi ne abin da ke ƙara soyayya a tsakanin ku, shi zai sa ku fahimci juna? Ko ɗaya babu, masana halayyar dan Adam sun nuna cewa haduwar masoya guda biyu yana haifar da wani shauƙi da yanayi mai wuyar fassaruwa, idanu kadai su na iya nuna shauƙi da begen da masoyan ke ciki.
Babbar sadarwa a tsakanin masoya su fahimci junansu ko da kuwa sun samu sabani wanda dama wannan ko a tsakanin harshe da hakori ana saɓawa.

Indo Shatu🌸

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa