AISHA AUGIE KUTA

AISHA AUGIE KUTA

An haifi Aisha Augie a garin Zaria, a ranar 11th April, 1980. Ɗiya ce ga marigayi  Sanata Adamu Baba Augie da Justice  Amina Adamu. Ta yi aure tana da yara uku maza.

 

Ta yi karatun digiri ɗinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta karanci fannin Mass Communication. Inda ta ke Masters ɗinta a bangaren Media and Communication a jami'ar Pan African University da ke Lagos. 

Aisha Augie kwararriyar mai daukar hoto ce, wanda hakan ya samo asali daga kyautar kyamara (camera) da mahaifinta ya ma ta. 

Abin mamaki ne a Nijeriya kuma yankin Arewa a ga mace na daukar hoto, sai dai a wajen Aisha Augie daukar hoto abu ne da ta dade tana sha'awar yi. 

Aisha Augie mace ce da ta jajirce wajen ganin cigaban yara mata da kuma matasa baki daya. Ta kasance mai bada gudunmuwa a harkokin da suka shafi yara mata, dalilin hakan ne ma UNICEF ta rantsar da ita a matsayin "High Level Women Advocate on Education with a focus on girls and young women". 

Aisha Augie ta samu karramawa da dama irinsu  Creative Artist of the Year wanda aka yi a The Future Awards a shekarar 2011.

Sai kuma  British Council a gasar "Through-My-Eyes" a shekarar 2014, a dai shekarar 2014 ta ƙara samun karramawa a matsayin Sisterhood Award for Photographer of the Year. 

Sannan tana riƙe da muƙamin Senior Special Assistant on New Media ta jihar Kebbi. 

Ayeesh Chuchu ✍️
22-12-2017
 

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa