BA SOYAYYA KADAI AKE BUKATA BA

BA SOYAYYA KADAI AKE BUKATA A ZAMANTAKEWA BA

©Ayeesh Chuchu

ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Da yawan mutane na tunanin soyayya kadai su ke bukata a rayuwar zamantakewar su, har wasu kan kwatanta cewa "In dai wance ko wane na so na ai shikenan banda matsala".
Ba ku da matsala ko? Shin soyayya kadai ku ke ganin ta ishe ku a zamantakewar ku? Akwai abubuwa muhimmai da ake bukata a zamantakewa, wanda idan babu su ba inda soyayya za ta je. Ita soyayya a matsayin tubali take a zamantakewa, da ita ne ake samun damar daura gini ta hanyar amfani da muhimman sinadaran ginin zai bukata.
Akwai masoyan da su na matukar son juna, amma ba su girmama junansu, basu da fahimtar juna a tsakaninsu. Wa su kuma su na son juna, amma ba su farin ciki da junansu, ba ta inda soyayya ba ta zuwa, za ta iya sa ka so wanda ko a mafarki ba ka tunanin za ka so, amma kwatsam ka ji kayi dumu-dumu cikin soyayya.
Matsaloli su yi ta faruwa a tsakanin ku, ku kasa magance su, wanda sun samo asali ne daga rashin ba ma sauran muhimman abubuwa dama a cikin soyayyarku.
Kuna ina masoyi zai cutar da masoyiyarsa haka ma masoyiya ta cutar da masoyinta, duk ba dan basu son juna ba, sai dan soyayya kadai su ke muradi. Maza nawa ke dukan matansu? Mata nawa ke ha'intar mazansu? Duk don su na son juna.
Su kan manta da girmama juna, samar da farin ciki a tsakanin su, tsayawa juna duk tsanani, babban burin su tunda su na son juna angama. Kwarai soyayya Nada matukar muhimmanci shiyasa na kira ta a matsayin tubali a nawa ra'ayin, saboda da ita ake gina rayuwar zamantakewa.
Amma kuma daukarta a matsayin (number one priority) abu da ke da matukar hatsari ga zamantakewa, dole tana da abokan tafiya wadanda sai da su ne za ta yi armashi ko in ce sai da su ne gini ke yin ƙarko.
Mu so juna, mu mutunta juna, mu girmama juna, mu ba junanmu hakkin da ya dace, mu tsaya ma junanmu, mu kula da junanmu, mu kyautata ma junanmu su na daga cikin abubuwan da za su sa gini soyayya yayi karko.
Sannan muna wani kuskure wajen sadaukar a soyayya mu kan manta da kanmu, idan ba mu so kanmu ba wa za mu so, jikinmu na da hakki akanmu. Da dama mu kan banzatar da damar da ke gare mu wajen sadaukar da ita kacokam ga wanda mu ke so, ko da sadaukarwa ba ta dace ba. Sai tafiya ta miƙa a lokacin da mu ka ga cewa wanda muke ma wannan sadaukarwa be cancanci ko da rabin sadaukarwa ba, a lokacin ne zamu dawo muna cizon yatsa.
Bayan mun bari damar da ke gare mu ta kubce, kada mu bari mutuncinmu da martabarmu ta salwanta a dalilin soyayya muyi ma kanmu adalci a yayin sadaukarwa.
Sannan kuma a soyayya akwai bukatar mu zama abokan juna, wadanda idan daya ya karkace daya zai taro dan uwansa, idan aka ce abokan juna na haƙika su ne wadanda duk daren dadewa su na tare, ko da sun yi fada daya zai fahimci daya, akwai kyakkyawar mu'amala a tsakaninsu. Idan kuskure ya faru a tsakaninsu za su zauna su fahimci juna. Za su yi kuka idan abin bakin ciki ya samu daya, za su dariya da farin ciki idan abun farin ciki ya sa mu, za su yi fada da juna amma hakan ba zai hana su kare juna ba a yayin wani abu na tashin hankali.

Kadan kenan daga cikin abubuwan da naga ya kamata in rubuta a nawa ra'ayin. Kofa a bude take wajen kawo gyara, tsokaci ko shawara.

Indo Shatu 🌸 (Chuchu)

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa