JIN ƘAN IYAYE

JIN KAN IYAYE 

© Ayeesh Chuchu
  Muna cikin wani zamani da ƴaƴa basu cika jin tausayin iyayensu ba. Ka yi girman da Allah ya hore ma ka amma ba za ka iya daukar nauyin iyayenka ba. Iyayen nan fa su suka raine ka har ka kai wannan matsayi da ka ke a yanzu. 

  Su suka tarbiyyantar da kai har wata ta gani ta kyasa. Bayan Allah madaukakin sarki babu halittar da ta cancanci godiya irin iyaye da su ka kawo ka duniya har ka zama abin da ka zama a rayuwa. 

 Allah SWT ya umarce mu da mu kyautatawa iyaye matukar kyautatawa. Wanda a yanzu kadanne ke kyautatawa iyaye, hakan yafi yawa ga maza waɗanda hakkin iyaye yafi rataya akawunansu, wasu daga sun yi aure sun fara tara iyali shi kenan sai su fita harkar kyautatawa iyaye, sun fifita iyalansu sama da iyayensu. To ɗan uwa bari ka ji, iyalanka da ka kyautatawa sama da iyayenka yanda ka yi ma iyayen nan suma sai sun maka sama da haka. Yanda ka ke kyautatawa iyayenka haka yaranka za su taso da ƙaunar ganin sun ji tausayinka. 

 Har aya aka saukar a Al-Qur’ani mai girma akan kyautatawa iyaye kamar yadda ya zo a cikin suratul Isra’i, aya ta ashirin da uku da kuma hudu. 

 “Kuma Ubangijinka Ya hukunta kada ka bauta wa kowa face Shi, kuma game da mahaifa biyu ku kyautata kyautatawa, ko dai ɗayansu ya kai ga tsufa a wurinka ko dukansu biyu, to kada ka ce musu ‘tir’ kuma kada ka tsawace su, kuma ka faɗa musu magana mai karimci”. 

 “Kuma ka sassauta musu fikafikan tausasawa na rahama. Kuma ka ce” Ya Ubangijina! Ka yi musu rahama, kamar yadda suka yi renona, ina ƙarami.”.

Shin ba ka kyautatawa iyayenka ba? Ka tausaya masu, ka kula da su kamar yadda su ka baka kulawa. A wannan lokacin ne su ka fi bukatar ka a kusa da su, dan ka ji matsalolinsu ka kuma tausaya masu. 

  Ba kamar uwa ya kamata a kyautatawa fiye da kowa kamar yadda ya zo a cikin suratul Lukman ayata goma sha hudu “Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu, uwarsa ta dauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yayensa a cikin shekara biyu (Muka ce masa), Ka gode Mini da kuma mahaifanka biyu. Makoma zuwa gare Ni kawai take”. 
Shin ɗan uwa wadannan ayoyi ba su isa su gamsar da kai ba akan kyautatawa iyayenka?

 Ka kyautata musu tun suna raye su sa maka albarka. Kar ka zo ka yi dana sanin a bayan rayuwarsu. 

 Ba ƙaramin gata Allah SWT ya ma ka ba, da ya bar ma ka iyayenka a raye har girmanka suka aurar da kai, suka baka tarbiyya ta gari, yi amfani da wannan damar ɗan uwa. 

 Wasu na can ba su san iyayensu, ba su rayu da su ba, basu san dadinsu ba, ka gode ma Allah da kai kana da wannan damar. 

 Wasu na jin ina ma su ne ke da iyayen ba kai ba, su kyautata musu iya kyautatawa. 
Muyi amfani da damarmu kafin ta kuɓuce ma na. 
Ayeesh Chuchu 

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa