Posts

Showing posts from June, 2019

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura. A wannan zamani da mu ke ciki aure ya zama abinda ya zama a Arewa. Yawaitar mutuwar aure kullum kara yawa su ke. Har ta kai ana iya aure wata daya a rabu. Akwai abubuwa masu dadi a rayuwar aure, musamman ka tuna cewa wannan na zaba a matsayin aboki ko abokiyar rayuwata. Sannan akwai kalubale da ke fuskantar aure wanda sai an taru gaba daya wajen tunkarar wannan kalubale. Da yawa a tunanin su rayuwar aure, rayuwa ce ta jin dadi da more rayuwa na dindindin, sai dai bayan shigar su sai suka iske abun ba haka bane. Masana sun nuna cewa rayuwar aure gaba dayanta wata makaranta ce mai zaman kanta, ba wai makarantar je ka ka dawo ba, a'a makaranta ce da ba'a fita ciki

DALILAI DA KAN SA A SO MISKILIN NAMIJI

DALILAI SHA DAYA DA KAN SA A SO MISKILIN NAMIJI Kwanakin baya nayi ta samu korafi daga bakin mata su na kawo kokensu akan miskilan maza. Da yawa na takaicin halayyar irin wadannan mazaje saboda dabi'arsu ta nuna halin ko in kula. Duk da an san cewa dabi'ar mata ce yawan magana, babban rauninsu a rayuwa shine "So", sabili da emotional side dinsu. Inda a maza ba hakan bane, kamar yadda na karanta a cikin littafin "Men are from Mars, Women from Venus", inda na gane bambance-bambance da ke tsakanin mace da namiji. Wasu na ganin cewa miskilanci ra'ayi ne, wani bangaren kuma na ganin halitta ce. Akwai taken da Bahaushe yayi ma miskili "Kafi mahaukaci ban haushi". Ana kallon miskilin mutum a kan cewa mutum ne shi mai girman kai, da jiji da kai, mutum mai wulakanci wanda sam ba haka bane ba. Yanayin halittar shi ce haka ta rashin son magana da kuma shiga abinda bai shafe su ba. Alal hakika ba'a fahimci ya rayuwar miskili take ba, shiyasa da y

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

ALAMOMI GOMA DAKE NUNA CEWA SOYAYYA TA KARE TSAKANIN KI DA SHI Akwai bambanci tsakanin namiji na sonki da kuma bai sonki, wanda zai nuna hakan a aikace, a baki da kuma yanayin mu'amalar ki da shi. Da yawan mata za su fara tunanin ko nayi wani laifi ne? Miye dalilin canzawar shi? Mi ya kamata inyi wajen kara karkato da hankalin shi a gare ni? Ire-iren wadannan tambayoyi ne da za su yi ta yawo a zuciyar budurwar da ta rasa gane kan saurayinta. Wata ba za ta fahimci cewa sonta ne ya daina ba, sai ta fara neman sasanci, ta shiga halin damuwa da tashin hankali musamman idan aka yi sa'ar cewa ta mutu a soyayyar sa. A matsayinki ta mace, wacce aka sani da rauni musamman a bangaren soyayya, ya zama wajibi ki natsu ba'a shiga soyayya ta ka, kin san mi kike so game da namiji sannan ki san alamun da ke nuni da cewa wannan yaudara ce ko kuma an daina yayinki, saboda mune a mafi yawan lokutta muke fadawa ciki. Monica Parikh dake a NYC masaniya akan zamantakewa da soyayya ta bayyan

Phone Calls

A wannan zamanin da mu ke ciki, daga lokacin da soyayya ta kullu tsakanin mace da namiji sai ku ga yawan phone calls ya qaru, a bangaren mace za ta yi ta jin dadi ai wane na matukar sona. Har labari za ta rika ba qawayenta "wallahi a rana sai muyi waya sau goma da shi, sama da 30mins ko 1hr". As time goes on, Sai ya rage kiran nan, maybe a rana sau hudu-biyar. Daga nan sai ta fara sama ranta ai ya fara kula wata, before you know ta fara korafi shi kenan fitinar yau daban ta gobe daban, kafin kace mi duk an ishi juna within 2 months. Da kin tambaya "wance ina wane?" "ke kyale ni da shi, dan rainin wayau ne bama tare yanzu".. Next month wani sabon bf ne.. Shima kuma haka. Miyasa a zamanin da ba'a samun wadannan matsalolin? Coz firarsu ta gani ga ga ki ce, koma minene a faifai za a kasa ayi ta ta kare. Duk wata doguwar firar waya rage karsashin soyayya take, make your phone calls short. Kuyi ta magana ba coma ba fullstop, tun ana fadin gaskiya ha