Posts

Showing posts from 2018

#FreePadsForGirls

#FreePadsForGirls Ina ta samun sakonni akan kamfen dinmu na #FreePadsForGirls, da yawa sun nuna farincikinsu da kuma goyon bayan su akan kamfen din. Alal hakika abu ne mai muhimmanci mu haɗa hannu wajen ganin wannan kamfen ya isa ga jami'an gwamnati. Ba dole sai pads din nan sun zama kyauta ba, a'a akalla ace dai an rage kaso mafi tsoka na farashinsu. Da yawan iyaye ba lallai bane su san muhimmancinsa ga ƴaƴa mata, sannan su iyaye ma ta ba kasafai mazajensu ke siya masu ba, sai fa mazaje yan boko da ke sako shi a provision. Yaran talakawa kuwa musamman na kauyuka ba ta pad iyayen suke ba, ta ya ya za'a ci abinci suke yi. Idan muka yi duba da package guda na Virony sanitary pad 700 - 800 yake, wane uba ne a kauye zai cire 800 ya siya pad ga yarinya daya, yana ganin wannan ya isa ya siya kwanon abinci ko zaman teburin mai shayi. Sannan akwai matsalar da yawa yaran nan basu san yadda za su yi amfani da pads din ba, basu san yanda za su kula da kansu ba. Rashin menstrual

TREND

Chuchu and LubnaSufyan calmlubna@gmail.com ayeeshasadeeq2010@gmail.com TREND Akwai abinda turawa kan kira 'TREND' da za'a iya fassarawa da wani abu sabo da zai shigo ko ince 'YAYI'. Kamar sabuwar shadda da samari zasu dinga yayi, burin kowanne a ciki ya mallaka, machine da makamantansu. A wajen mata kamar turare, dinki ko wani abu daya danganci kwalliya, wannan TREND bai tsaya a iya abubuwan amfani ba, har da wakoki ko finafinai da zasu shigo yan yayi. TREND dinmu na yau ta bangaren wakokine, wakokin da kan zo da salon rawa kala-kala. A shigowar 2018 din nan anyo wakoki kala-kala irin su Shaku-shaku, Kope challenge ga kuma sabuwa yar yayi wai ita collapse challenge Wadannnan kalolin rawa da su ka zo da rawar da burin kowanne matashi ko matashiya su saka wakar su kwaikwayi rawar. Ok! ba sai addini ya kai ga shigowa ciki ba, bara mu taba al'ada kamun muzo kan addini, akwai raye rayen da a al'ada ta malam Bahaushe ko namijin bai kamata ya yi ta ba balle h

KASUWANCIN ZAMANI

Image
Sannu a hankali na gane cewa smartphones ba wai dan kayi chats kadai ne amfanin su ba. You can use smartphone to advertise your business, ba wai a social media kadai ba. Google is very helpful when it comes to network marketing business, akwai Google My business wanda za ka iya amfani da shi wajen tallata kasuwancinka free. But what is need most shine content na page dinka. Misali na shiga Google kawai na rubuta Ayeesh Chuchu a search engine, duk wani abu da ke dauke da Ayeesh Chuchu zai bayyana a search results dinka. Maybe wani na neman wani abu, kamar a ce ya yi searching "bakery in Katsina". Ace ka/ki na sana'ar bakery, already Kuna da sites a Internet. Wannan search engine din zai tattaro dukka bakeries da ke Katsina wadanda ke internet. Sannan zai zabo wadanda ke da contents mai kyau. Anan amfanin content ya shigo. Kun ga kenan hakan zai iya taimakawa wajen bunkasa kasuwancinku. Abinda yasa nayi wannan maganar shine I got a customer through Google my business

DA SAURAN RINA A KABA

RANAR MATAN KARKARA TA DUNIYA DA SAURAN RINA A KABA Ayeesh A. Sadeeq ayeeshasadeeq2010@gmail.com Idan aka yi la'akari da yanayin da matan karkara ke ciki bana tunanin an samu wani cigaba na azo a gani ba. Musamman idan aka yi duba da yawaitar kananan yara dake qara fantsama a cikin harkar nan ta tallace-tallace. Wadannan ƙananan yara mata sune ake jefawa cikin halin ha'ula'i, musamman yawaitar cin zarafin su da ake yi nayi masu fyaɗe, yara ƙanana ana samun su dauke da cikin shege a dalilin haiƙe masu da ake yi, ko kuma da ra'ayin kansu ta hanyar yi masu romon baka. Su fa mutanen karkara ba kasafai suke kallon gidajen talabijin ba, karanta jaridu da kuma sauraron Radiyo. Babbar hanyar da ya kamata a bi wajen wayar masu da kai bai wuce ta hanyar community outreach. Wannan kira ne na musamman ga kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka a wajen ganin an rage mafi yawa daga cikin kason matsalolin da ake samu a karkara. Ta fannin tallace-tallace da ƙananan yara kan y

YOU CAN HAVE YOUR ROMANTIC DINNER DATE, A TSAKAR GIDAN KU GARI YAYI DUHU.. TAURARI SUN HASKA SARARIN SAMANIYA ..

Image
Money Money Money! Yes! We all love Money. Babu wanda zai ce bai son kudi, ko a ce wane ko wance kun cika son duniya. Muna son duniyar nan to the extend of wasunmu ma na mantawa da dalilin halittarsu a doron kasa. Wasunmu na mantawa da akwai Lahira.. 😂 So kar kace mun ba ka son kudi, I love Money🙈.. Amma mi? Kudi ba zasu zama number one priority din mu a rayuwa ba, a ce komi zamu gina muna gina shi ne based on money.. That's so bad.. Har ta kai relationships dinmu muna gina su saboda kudi. Mostly mu mata anan muke fadawa halaka da juyin juya halin rayuwa. Ban manta ba someone sent me a message "Wai ke kina yi kamar ba ki son kudi waya san mi kike yi".... Murmushi nayi kawai. Tabbas! Ina son kudi, shiyasa ma na daga dacewar in neme su da kaina, zan fi ganin value din su... Mafi yawan mata na da burin auren mai kudi, ni fa banga laifin su ba. Laifin su daya, da suka sa kudin gaba da komi. Mata nawa ke auren masu kudin amma ba su da kwanciyar hankali? Mata nawa ke

YAUDARA

YAUDARA Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Na dade ina son inyi magana akan wannan maudu'in amma ban san ta ina zan fara ba, ataikace sai na fara typing sai in rasa abin rubutawa ba wai dan ban san mi zan rubuta, sai dan yadda maudu'in ke da sarkakiya, ta yanda nake son ya kasance balance ta kowane bangare. A kullum yaumin ina son in ja hankalin yan uwana matasa maza da mata da mu ji tsoron Allah mu kuma kyautata niyyar mu akan duk abinda muka sa a gaba. A kwanan nan na ji cases da basu kirguwa akan wane ya yaudari wance, wance ta yaudari wane. Shin mi muke so mu zama ne? Duniyar nan idan ka ji wasu abubuwan da ke faruwa sai ka ji mutanen kansu na sure ma ka, soyayyar ma na fita daga ranka, saboda amana tayi karanci. Duniyar ta zamo so scary. A nawa tunanin da ra'ayin banga amfanin soyayyar da ba za ta kai ku ga aure ba, to don mi za ku yi ta bayan kun san ba auren juna za ku yi ba, yafi tun farko kar ku samo abinda ku ka san ba za ku iya karasa shi ba. Kace

SANA'A SA'A (I)

Image
SANA'A SA'A Ayeesh A. Sadeeq ayeeshasadeeq2010@gmail.com Sana'a yanzu da kudi kalilan ma za ka iya farawa, kawai what you need is the passion, ba wai dan wance ko wane na abu kaza ba nima in ce sai nayi. A'a! Ya zamanto kana son abun, ta yanda duk wuya duk dadi za ka iya jurewa. Sannan kafin ka fara kasan mi mutane suka fi so, mi suke bukata, misali kana iya duba area da ka ke mi aka fi bukata. Misali ta yiwu a locality din ka sun fi bukatar abinci, sai ka duba wane abinci ne zai fi saurin shiga wajen mutanen, asin za ka fi yin ciniki a matsayinka na starter. Akwai bukatar a lura da wane yanayi (weather) ake ciki, ba za ki zo kina saida kununaya da zobo ba ana wannan sanyin, a matsayinki ta starter ba lallai ne ki samu ciniki ba.  Akwai sana'o'i da ake da competition sosai yanzu, to dole sai kin duba mai less competition for a starter. Saboda kar ki zo ki zuba kudi ya zamanto babu customers da zasu siya, ki fara da kadan sannan wanda zai fi saurin shiga

Roadside

Image
I was in tricycle when I snapped this picture along katsina road, Funtua, Katsina state, Nigeria. Isn't it beautiful?

BA KOWACE MACE KE NEMAN MIJI A SOCIAL MEDIA BA

BA KOWACE MACE A SOCIAL MEDIA KE NEMAN MIJIN AURE BA😟 "Kin rasa mijin aure, kin zo Facebook kina neman miji". "Kin sa hotonki kina tallar kanki dan ki samu miji". "Kina fira da maza dan ki samu miji". "kina posts dan ki samu miji".. "Kina mutunci da mazan Facebook dan ki samu miji". Is that all you can say about girls on social media? Duk namiji mai wannan tunanin stoop so low Wallahi. Lemme tell you not every girl on IG, Facebook or Twitter is looking for husband. Muna social media dan ra'ayinmu, muyi gogayya da mutane daban-daban, muyi sharing ideas, a sada zumunci. Ni ba zanyi jayayya da kaddara ba, coz a lot of people met their spouses on social media. Abu ne mai kyau matukar da kyakkyawan niyya aka yi shi. Idan ni Aisha mijina a social media zamu hadu, ina fatan alkhairi ya hada mu ba sharri ba. Amma ku zo kuna maganar miji matan social media suka fito nema this is bad. Yes! It's not a bad thing mace ta nemi miji,

My Moments 2

Image
Wadannan hotuna na dauke su ne a lokacin da naje kitso, a hanya ta ta dawowa. A lokacin hadari ya hadu kamar za a yi ruwa.

My Moments

Image
Daukar hotuna na daya daga cikin ababen da ke dauke mun kewa, su dau mun lokaci ba tare da na ankara ba. Yana daga cikin abubuwan da nake so in zama, sai dai mi? Yanayin al'adarmu ba kasafai ake ganin mata acikin jerin mutane dake daukar hoto ba, bare har su dauke ta a matsayin sana'a. Mutane su gane cewa zamani ya canza, matukar mace za ta kama mutuncinta banga aibin ta shiga sana'o'i da aka san maza da su ba. Bai zama dole ya zama sana'a a gare ta ba. Kamar ni passion ne a wajena..

A TUNANINA

A TUNANI NA A tunani na yawan shekaru, ilimi, arziki basu ke nuna natsuwa, hankali da cikar kamalar mutum ba.    Sai kaga yaro mai karancin shekaru tattare da natsuwa, hankali da cikar kamala.   Hakan wata baiwa ce daga Ubangijin al'arsh mai girma da yake ba bayinsa ba tare da karfi ko dabarar mutum ba.   Da yawan mutane sun dauki masu karancin shekaru a matsayin wawaye da basu da 'yanci ko damar faɗin albarkacin bakinsu, hakan babban nak'asu ne a rayuwarmu. Muna manta cewa kowane ɗan Adam da irin tasa baiwar.   Duk abinda kaga Allah ya baka bafa iyawar ka ce tasa aka baka, face dai wannan nufi ne na Allah SWT.   Yan uwana matasa kar ku manta cewa kuma fa kuna da damar faɗin ra'ayinku game da harkokin rayuwa, kuna da damar tofa albarkacin bakinku. Shifa ilimi kogi ne. Kuma dokar kasa ta baku wannan damar, kamar yadda yazo a cikin tsarin constitution,shafin da ke magana akan FUNDAMENTAL RIGHT. Wanda ke nuna cewa ko wane dan kasa na da damar bayyana ra'ayin shi

RABUWAR IYAYE

RABUWAR IYAYE Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com 11-07-2018 Muna cikin wani zamani da auri saki ya yawaita a tsakanin ma'aurata. Akwai dalilai masu karfi da ke assasa mutuwar aure. Sai dai mi? Mutuwar auren na kawo matsaloli a rayuwar yaran da ke tsakanin ma'auratan. A irin wannan zamanin da mu ke ciki, iyaye ma na tare suna bakin kokarin wajen tarbiyyantar da ƴaƴansu ana samun matsaloli ina ga iyayen da suka rabu da juna. Da yawan yaran hankulan su na rabuwa ne gida biyu, su kan rasa shakuwa ta iyaye da ƴaƴansu musamman idan daya daga cikin iyayen ke tare da ƴaƴan, kunga kenan sun rasa shakuwa ta daya bangaren.    Matuwar aure a tsakanin iyaye na jawo rashin yarda a tsakanin yaran, zasu riƙa kallon iyayen ta wata fuska ta daban, ana samun masu nuna ƙyayya ga daya daga cikin iyayensu saboda dalilinsu na ganin cewa watakila uban ne ya assasa rabuwarsu da mahaifiyarsu, ko kuma ta bangaren ita mahaifiyar ce musabbabin hakan. Wasu daga cikin yaran basu samun kulawar

SHAYE-SHAYE A TSAKANIN MATASA

Image
SHAYE-SHAYE A TSAKANIN MATASA Ayeesh A. Sadeeq 27-06-2018 ayeeshasadeeq2010@gmail.com   Shaye-shaye ya zama ruwan dare a tsakanin matasan wannan zamanin, abin al'ajabi da mamaki bai wuce yanda gaba daya jinsin wato maza da mata ke tu'ammali da kayan maye. Da yawan su hakan ya faro asali ne daga abokan da su ke mu'amala da su. Mafi yawancin iyaye da malamai na matukar kokari wajen ganin sun nuna ma matasa illar da ke tattare da shaye-shaye. Sai dai akan yi rashin sa'a da wasu iyayen da ke bada gudunmuwarsu wajen lalacewar yaransu.   A matsayinmu na matasa akwai buƙatar mu san wadanne abokai ya kamata mu yi hulda da su, kamar yadda bature ke cewa "Show me your friends and I'll tell you who you are". Wasu zasu taso da kyakkyawar tarbiyya, sai dai kash! Abokan da suke haduwa dasu kan gurbata wannan kyakkyawar tarbiyya. Akwai matsalar nan ta da yawan iyaye basu damu da sanin abokanan ƴaƴansu ba, idan aka yi rashin sa'a sai yaran su hadu da abokanan

Social Media Relationships

Image
Soyayyar social media tana zama ruwan dare a tsakanin ma'abota shafukan, sai dai mi? Tana tattare da illoli musamman ga mata. Da yawa ba son Allah da annabi bane, maybe ana neman wajen rage zango ne, ya gama firarshi da budurwar shi ke kuma sai a dawo kanki Hajiya Sidechick🤦🏽‍♀,nan za a kashe ki da kalaman soyayyar da ke narkar da zuciya ki ji no one but him. Shikenan ke amfanin ki a debe kewa dake. Tunda kuke bai taɓa furta "I'm on my way to see you" ba, Kullum aikinsa "Babe! I love you with all my heart ♥", emojis love kamar dan shi aka yi su, ga shegiyar karya da dadin baki. My sister you're fooling yourself, he's not worth your time and resources,kina ji na ko? 🙄, hope I'm making sense here? 🤣. I'm not condemning social media relationships, tunda akwai wadanda suka yi kuma sun dace, amma ba shi zai baki license na ba kowane trash damar tunkararki ba, ki saurari wannan ki saurari wancen ke kenan ba ki da alkibla, ba a ce kiyi wulakant

Rape

Image
RAPE BY AYEESH CHUCHU Rape can be described as a forceful sexual relationship without consent. Rape is a type of sexual assault usually involving sexual intercourse or other forms of sexual penetration carried out against a person without that person's consent or violent penetratiion of a woman. Worldwide, rape is primarily committed by males. Rape by strangers is usually less common than rape by persons the victim knows, and male-on-male and female-on-female prison rapes are common and may be the least reported forms of rape. The issue of rape cannot be over emphasized, the society has not grown to the stage where people boldly report cases of rape to the security, some are afraid of stigmatisation, some of the raped person can't voice out, they end up with psychological injuries. There is no one right or wrong way to behave to avoid rape. But there are some things a woman can do that may make her less likely to suffer some kinds of rape. What a woman does depends on ho

BULALIYA

Nayi mamaki kwarai! Wace irin rayuwa ce wannan? Kayi abu wanda za ka cutar da kanka, ka saɓi Ubangijinka duk don mutanen duniya su yaba, ko ince don samun common likes and comments on social media. It's very unfortunate yanda wasu matan su ka mayar da kansu da rayuwarsu kazantacciya. Kin bi maza, kin bi mata 😏😫 duk don ki sami abin duniya ki shiga sahun slay Queens, peppe dem gang, ki zama one in town, ki wuce ana kun ganta can, she's hot and sexy. Yaa Allah! Abinda kike so a ce ma ki kenan? Hot 🔥! Wato ke zazzafa ce irin abincin nan mai shegen zafi ko? To sannu wuta uwar yan zafi, wallahi Allah zaki gamu da Ubangijinki idan ba ki tuba ba, kin riƙe mutuncinki. Miye sutura? Miye waya? Miye mota? Dukkansu abubuwan da ke tafiya da zamani daga anbar yayinsu shikenan fa sun tashi aiki, ko kuma su lalace. Ki ce yau a Habuja, gobe a ganki  Lagos, jibi kina Kano, gata kina Dubai, ko kafar kare kika ci iyakar yawon da za ki yi kenan. Da anyi magana kice ke taki kaddarar kenan,za

Testing

Na taba magana akan wannan kalmar ta "testing" da matasa samari ko ince wasu mazan ke amfani da shi wajen gurbata tarbiyyar ƴaƴan mutane. Hakan kuma na taba posting din wani issue na wata baiwar Allah makamancin hakan. Wallahi Allah maza ku ji tsoron Allah, wai namiji zai ce ma ɗiyar wani "Baby mu hadu a hotel kaza" "baby turo mun hoton this and that". Idan ta qi, ya gwada duk tricks dinsa abin yaci tura, sai alaji ya karkato kai "ai dama testing din ki nayi inga idan yar hannu ce ko tier leather ce". Sannu Chef uban yan girki da zai dandana zaqin Maggi, gishiri, Onga, Mr. Chef ko knorr a abinci. Nace ba, gidan ku da testing din, wato testing ko? . Kwantiniyo Allah na ganinka wallahi, idan ba ka ƴaya kana da ƙannai mata. Idan aka ce za a yi testing din su ya za ka ji? Malam ka auna abin fa a ma'aunin hankali. Ka tuba tun Mala'ikan daukar rai ba baƙunce ka ba, kana cewa ma yayan mutane testing din su ka ke. Duk namiji mai tsoron A

SON ABIN DUNIYA

Image
SON ABIN DUNIYA A TSAKANIN ƳAƳA MATA Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Muna cikin wani zamani da matuƙar za'a samu abin duniya to idanun kan rufe ne ta kowane hali domin samun cikar buri. Hakan yasa mata ma ba'a bar su a baya ba, wajen ganin sun sami abin duniya ta kowane hali. Wannan ya samo asali ne daga rashin wadatacciyar zuciya na wasu daga cikin mata, musamman ma ƴan mata a wannan zamanin. Har ta kai ta kawo mace kan iya zubar da ƙima da mutuncinta wajen ganin ta sami abin duniya. Akwai abubuwan da ke jawo son abin duniya ga ƴaƴa mata wanda sun sha faruwa kuma suna kan faruwar. Kadan daga cikinsu sun haɗa da: -Rashin cusawa yara tsoron Allah, daga inda yaro ya tashi ba a cusa masa tsoron Allah ba a duk inda yake, to tabbas dole a samu matsala. Wannan tsoron Allah ne zai taimakawa yaro a duk inda yake iyaye basu da shakku akansa, saboda duk abinda zayyi zai tuna da cewa Allah da ya halicce shi na kallonsa. Hakan take a wajen ɗiya mace, matuƙar aka cusa ma

ƊIYA MACE

ƊIYA MACE! "Ladidi idan kin gama abinda ki ke,ki zo ke da Innarki".   "To Baba". Dauraye hannuwanta ta yi,ta shiga ɗaki ta dauki mayafinta dake ajiye a saman gado.    Ta leka madafi "Inna ki zo Baba na neman mu". "to gani nan zuwa". Tare suka isa ɗakin Malam Iro,ya kalli iyalinshi ya kaɗa baki ya ce "Ba wani abu yasa na kira ku ba sai dan in shaida maku cewa na karɓi kuɗin auren Ladidi, watan gobe za a ɗaura aurenta da Danjuma". "Haba Malam duka-duka nawa Ladidin take? Shekararta sha uku fa".   "Wayyo Allah! Na shiga uku! Dan Allah Baba kayi hakuri ka bar ni in cigaba da karatu na". "Ke dalla rufe mun baki, shashasha kawai, ana neman a yi ma ki gata kina wa mutane iskanci. Ba ruwana da shekarunta, Nana Aisha matar annabi ai ba ta kai Ladidi ba tayi aure. Babu babban mutuncin da wuce mace a gidan mijinta, mata nawa aka ma aure da basu kai ki ba? Dan haka na gama magana". Ladidi ta gama kukan

DUK TSANANI DUK WUYA!

DUK TSANANI DUK WUYA! © Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com 17-04-2018 A al'adance mace ba ta da hurumin da za ta kai karar mijinta koda kuwa ita ce ke da gaskiya, koda kuwa an ci zarafi da mutuncinta. Koda kuwa tana zaune ne cikin mawuyacin hali, al'ada ba ta bata wannan damar ba. Dole tayi biyayya ga mijinta koda kuwa hakan ya saɓa faɗar Allah da ma'aikinSa SAW. Hakan mu ka taso kaka da kakannin ana hakan. Saboda shi miji shugaba ne, kuma shugaba baya laifi ko? Haka ake koyar da mata tun suna yaran su, ko gida akan fifita namiji sama da mace. Tun daga kan haihuwa, idan namiji ne za a siya ma shi ƙaton gida da mota idan masu arziki ne, talaka kuwa gona ce za a bashi, a kuma yankar masa fegi a cikin gida inda zai saka matarshi. A taiƙace ma auren gata ake ma shi, ita kuma mace ko ohooo. Ita ba mutum ba ce ai, kuma ba ta zuciya a kirjinta. Tun daga nan rashin adalci ya shiga a tsakani, cewa aka yi iyaye su yi adalci a tsakanin ƴaƴansu. Shin adalcin kenan? Tun d

INA MAFITA?

"Lami! Lami!! Lami!!!". "Na'am Inna". "Ina ki ka shige ne? Sai kwala ma ki kira nake?". "Bitar karatun da akai mana a makaranta nake yi". "To yi maza ki siyo man gishiri goma, manja na hamsin da ajino na talatin shagon Audu. Kar fa ki tsaya wasa". "To Inna". Cikin azama ta amshi kuɗin ta fita daga gidan.                                *** "Lami ke ce da ranar nan?". "Eh! Inna ta aiko ni". "Shigo cikin shagon mana kin tsaya daga waje kamar wata baƙuwa". "A'a sauri Inna tace inyi kar in dade". "Ba ki son in ba ki alawar kenan? Yau harda Naira goma zan ƙara ma ki". "Ni dai a'a". Fitowa yayi daga shagon, ya duba hanya yaga babu mai tahowa, yasa hannu ya kinkimi Lami yarinya yar kimanin shekara bakwai. "ka bari, ban so, zafi yake mun". Jikinta na ta kyarma kamar ana kaɗa mazari gab! Gab!! Gab!!! Ya shige da ita cikin shagon,be ɓata lo

Appreciation

Image
When appreciation is low, conflict is high. Lack of appreciation is often the root cause of infidelity in relationships. #relationships #ayeeshchuchuwrites #love

LOKACI

LOKACI Kowane dan Adam yana da lokacinsa na wanzuwar abubuwa a cikin rayuwarsa. Wani kan gama karatu da wuri ya kere ma sa'oinsa, wani ya samu aiki da wuri, wani yayi aure da wuri da sauran ababe makamantan hakan. Haka kuma kowa da tasa ƙaddarar a rayuwa, taka daban haka kuma tawa ƙaddarar daban, abin da ake so dai mutum ya yarda da kowace irin ƙaddara walau mai kyau ko akasin haka.    Mutane kan yi kuskuren fahimtar waye kai da kuma abokinka, ta iya yiwuwa abokinka, dan uwanka ko makwabcinka ya riga ka samun nasara a rayuwa, ya samu shahara cikin ƙanƙanin lokaci amma kai shiru kamar an shuka dussa. Mutane zasu danganta ka da marar nasara a rayuwa ko wani wanda ya gaza samun nasara.   Sun manta cewa kai da shi ba hanyarku ɗaya ba, ba kwazonku ɗaya, ba haka aka ƙaddaro ma ku ba, kuna da bambamci. Kowanen ku nada tsarin ta sa rayuwar.   Kadan daga cikin mutane ne zasu yi hakurin ganin cigabanka, wasu zasu yi ma dariya wasu zasu yi ma gwalo, kai wasu har zunɗe da yafice zasu ma

Why?

Image
Why do you change like weather???

#ayeeshchuchuwrites #marriage #relationship

Image

MU GANE BAMBANCIN DAKE TSAKANINMU

Kadan daga cikin maza ne suka san abinda mata ke so, haka ma a bangaren mata. Wanda rashin sanin taƙamaimai halayya da bambancin jinsi na daya daga cikin ababen da ke kawo matsaloli acikin zamantakewa. Jiya muna magana da wata kawata ke mun maganar saurayinta bai yawan kiranta kamar yadda na wance ke yi. Sai nake tambayar ta shin idan bai kira ta ba ita tana kiran shi ko tura ma sa sakon sms? A yanda ta nuna mun ita ba za ta iya ba, tunda har shi bai kira ba. Kunga kenan daga an dau lokaci basu hadu ba, bai kira ta ba, ita ma ba ta kira ba shikenan soyayya ta bi ruwa. Maza ku gane mata na son kulawa komin kankantarta, ka kira ta koda ba ka da abin cewa, tambayarta ya ranarta ta kasance anan za ka ji labari tiryan-tiryan. Saboda muna son Magana, muna son a tambaye mu mu bada amsa. Wanda a wajen maza kuma ba haka bane. Daga zarar ka dau lokaci ba tuntubi mace ba duk irin son da kake ma ta, ba za ta gane ba, matuƙar bata fahimci bambanci duniyar da ke tsakanin ku ba. Da farko za t

BIN YAN TSIBBU

Image
BIN YAN TSIBBU   Abin mamaki da takaici ne a ce mace na bin bokaye don ta mallaki namiji. Abin ban haushi da takaici yanda abin ya zama ruwan dare a tsakanin ƴan mata yanzu.   To ke Jummala tun yanzu ba ki yi auren ba kin fara bin bokaye don a karkato ma ki da zuciyar shi, ina ga anyi auren ai sai abinda yayi gaba. Shin kin gwammace ki siyar da Aljannarki saboda namiji?  Ki zo ki aure shi ba kwanciyar hankali, kinga kin zo duniya a zero za ki koma a zero. Ki lura, ki kuma hankalta bin bokaye ba zai kai ki ko'ina ba face ga halaka, saboda imaninki tunin kin zubar da shi, kin kasa yarda da cewa Allah shi ke komi.   Mi zai hana ki tashi ki roki Allah tsakiyar dare a lokacin da wasu daga cikin bayinSa ke bacci ki kai ma Sa kukanki kina mai imani da yaƙinin cewa shi zai amsa ma ki addu'ar ki, ya biya ma ki bukatar ki. Abin da yafi daga mun hankali bai wuce yanda wasu ke bin bokaye da Malamam tsibbu ba fa dan su auri saurayi suke bin su ba, sai dan wata biyan bukata tasu ta ba

RASHIN YABAWA

Image
RASHIN YABAWA Yana daya daga cikin ababen da ke kawo rikici a zamantakewar ma'aurata rashin yabawa. Miji na iya bakin kokarin sa wajen ganin ya kyautatawa matarsa sai a samu akasi ita sam ba ta ganin kokarin sa, duk abinda yayi sai ta kawo inda ba'a kyauta ma ta ba. Wanda hakan shi ke sa daga baya mazan su zame hannayensu a harkokin iyalinsu. Duk inda namiji yake bai fa son a raina kokarin sa, koda kuwa a zahirance ba haka abin yake ba, yafi son a kambama sai yaji dadi ya kara himma. Haka kuma a fannin mata, mace na iya bakin kokarinta wajen kyautata ma namiji, amma shi a wajen sa ba abinda take yi. Idan girki ta yi sai ya samu inda aka yi kuskure, nan zai hau sababi, ba ya tunanin ba fa kullum take wannan kuskuren ba, miyasa ba zai fahimce ta ba. Daga nan an dauko makaman wargaza ingantacciyar alaka, tun kowa na yi dan a kyautata ma juna daga karshe sai a daina. Kowa ya koma yin abinda yaga dama, abinda yaga zai iya. Da haka yara ke tasowa abinda suka ga iyayen su nayi s

TIMABEE

Image
FATIMA BABAKURA (TEEMABEE) Matashiyar yar kasuwa Mai sana'ar hada jakkunan hannu (handbags) na mata. Fatima Babakura wadda aka fi sani da TEEMABEE, matashiyar budurwa mai aƙalla shekaru ashirin da biyu. Tayi karatun degree ɗinta na farko a jami'ar Mcmaster University Canada. Ta fara sana'ar hada jaka ne a shekarar 2013, inda ta fara zanawa a takarda. Daga nan ne ta tsunduma ka'in da na'in wajen haɗa jakkunan hannu na mata. Fatima Babakura na daya daga cikin matasa mata masu kaifin basira da hazaƙa. Wadanda suka kara fito da martabar yan Afrika a idanun duniya. Mace mai kananan shekaru wadda ta fito daga yankin Arewa maso gabashin Nijeriya abin a jinjina ma ta ne. Ta fitar da samfur na jakkuna da yawa daga shekarar 2013, ta siyar dasu ga mutanen dake wajen Kasar Canada kama da Dubai, London, South Africa, USA da sauran shagunan siyar da kaya dake a Canada. Babban burin Fatima bai wuce ta ga ta gina katafen kamfani a Nijeriya ba, wanda ba zai tsaya a iya jakku

SANNU BA TA HANA ZUWA

Image
SANNU BA TA HANA ZUWA   AYEESH CHUCHU   Ya kai ɗan uwana , ka ganta kana so koh? Kana son aurenta , kana son ta zama uwar ya'yanka koh?   Idan har kana son ta haura waɗannan matakai , sai ka bi a hankali , kar ka yi garaje . Sai ka fahimci wacece wadda ka ke son ta taka waɗannan matakai . Shin ka san wacece ita ? Mi ya ja ra'ayinka ka ji kana sonta ? Wadanne halaye suke burge ka a tattare da ita ? Shin iliminta da wayewarta (ba wayewar 'yan bariki ba) sun ma ka ? Shin ka taɓa cin karo da wani hali na ta mara kyau ? Wanda ka ke jin za ka iya zama da ita . Shin ita ɗin ka ke so? Ko kuwa wani abu na ta. Shin kana tunanin za ta iya ba ya'yanka tarbiyyar da ta dace? Shin ita ɗin ka taɓa cin karo bacin ranta ko a lokacin da take cikin bakinciki ? Ta ya kake tunanin za ka iya shawo kanta a irin wannan yanayi ? Shin za ka iya canza wasu daga cikin dabi'unta wadanda basu dace ba? Shin ka