Posts

Showing posts from April, 2018

SON ABIN DUNIYA

Image
SON ABIN DUNIYA A TSAKANIN ƳAƳA MATA Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com Muna cikin wani zamani da matuƙar za'a samu abin duniya to idanun kan rufe ne ta kowane hali domin samun cikar buri. Hakan yasa mata ma ba'a bar su a baya ba, wajen ganin sun sami abin duniya ta kowane hali. Wannan ya samo asali ne daga rashin wadatacciyar zuciya na wasu daga cikin mata, musamman ma ƴan mata a wannan zamanin. Har ta kai ta kawo mace kan iya zubar da ƙima da mutuncinta wajen ganin ta sami abin duniya. Akwai abubuwan da ke jawo son abin duniya ga ƴaƴa mata wanda sun sha faruwa kuma suna kan faruwar. Kadan daga cikinsu sun haɗa da: -Rashin cusawa yara tsoron Allah, daga inda yaro ya tashi ba a cusa masa tsoron Allah ba a duk inda yake, to tabbas dole a samu matsala. Wannan tsoron Allah ne zai taimakawa yaro a duk inda yake iyaye basu da shakku akansa, saboda duk abinda zayyi zai tuna da cewa Allah da ya halicce shi na kallonsa. Hakan take a wajen ɗiya mace, matuƙar aka cusa ma

ƊIYA MACE

ƊIYA MACE! "Ladidi idan kin gama abinda ki ke,ki zo ke da Innarki".   "To Baba". Dauraye hannuwanta ta yi,ta shiga ɗaki ta dauki mayafinta dake ajiye a saman gado.    Ta leka madafi "Inna ki zo Baba na neman mu". "to gani nan zuwa". Tare suka isa ɗakin Malam Iro,ya kalli iyalinshi ya kaɗa baki ya ce "Ba wani abu yasa na kira ku ba sai dan in shaida maku cewa na karɓi kuɗin auren Ladidi, watan gobe za a ɗaura aurenta da Danjuma". "Haba Malam duka-duka nawa Ladidin take? Shekararta sha uku fa".   "Wayyo Allah! Na shiga uku! Dan Allah Baba kayi hakuri ka bar ni in cigaba da karatu na". "Ke dalla rufe mun baki, shashasha kawai, ana neman a yi ma ki gata kina wa mutane iskanci. Ba ruwana da shekarunta, Nana Aisha matar annabi ai ba ta kai Ladidi ba tayi aure. Babu babban mutuncin da wuce mace a gidan mijinta, mata nawa aka ma aure da basu kai ki ba? Dan haka na gama magana". Ladidi ta gama kukan

DUK TSANANI DUK WUYA!

DUK TSANANI DUK WUYA! © Ayeesh Chuchu ayeeshasadeeq2010@gmail.com 17-04-2018 A al'adance mace ba ta da hurumin da za ta kai karar mijinta koda kuwa ita ce ke da gaskiya, koda kuwa an ci zarafi da mutuncinta. Koda kuwa tana zaune ne cikin mawuyacin hali, al'ada ba ta bata wannan damar ba. Dole tayi biyayya ga mijinta koda kuwa hakan ya saɓa faɗar Allah da ma'aikinSa SAW. Hakan mu ka taso kaka da kakannin ana hakan. Saboda shi miji shugaba ne, kuma shugaba baya laifi ko? Haka ake koyar da mata tun suna yaran su, ko gida akan fifita namiji sama da mace. Tun daga kan haihuwa, idan namiji ne za a siya ma shi ƙaton gida da mota idan masu arziki ne, talaka kuwa gona ce za a bashi, a kuma yankar masa fegi a cikin gida inda zai saka matarshi. A taiƙace ma auren gata ake ma shi, ita kuma mace ko ohooo. Ita ba mutum ba ce ai, kuma ba ta zuciya a kirjinta. Tun daga nan rashin adalci ya shiga a tsakani, cewa aka yi iyaye su yi adalci a tsakanin ƴaƴansu. Shin adalcin kenan? Tun d

INA MAFITA?

"Lami! Lami!! Lami!!!". "Na'am Inna". "Ina ki ka shige ne? Sai kwala ma ki kira nake?". "Bitar karatun da akai mana a makaranta nake yi". "To yi maza ki siyo man gishiri goma, manja na hamsin da ajino na talatin shagon Audu. Kar fa ki tsaya wasa". "To Inna". Cikin azama ta amshi kuɗin ta fita daga gidan.                                *** "Lami ke ce da ranar nan?". "Eh! Inna ta aiko ni". "Shigo cikin shagon mana kin tsaya daga waje kamar wata baƙuwa". "A'a sauri Inna tace inyi kar in dade". "Ba ki son in ba ki alawar kenan? Yau harda Naira goma zan ƙara ma ki". "Ni dai a'a". Fitowa yayi daga shagon, ya duba hanya yaga babu mai tahowa, yasa hannu ya kinkimi Lami yarinya yar kimanin shekara bakwai. "ka bari, ban so, zafi yake mun". Jikinta na ta kyarma kamar ana kaɗa mazari gab! Gab!! Gab!!! Ya shige da ita cikin shagon,be ɓata lo