SANA'A SA'A (I)

SANA'A SA'A

Ayeesh A. Sadeeq
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Sana'a yanzu da kudi kalilan ma za ka iya farawa, kawai what you need is the passion, ba wai dan wance ko wane na abu kaza ba nima in ce sai nayi. A'a! Ya zamanto kana son abun, ta yanda duk wuya duk dadi za ka iya jurewa.
Sannan kafin ka fara kasan mi mutane suka fi so, mi suke bukata, misali kana iya duba area da ka ke mi aka fi bukata. Misali ta yiwu a locality din ka sun fi bukatar abinci, sai ka duba wane abinci ne zai fi saurin shiga wajen mutanen, asin za ka fi yin ciniki a matsayinka na starter.
Akwai bukatar a lura da wane yanayi (weather) ake ciki, ba za ki zo kina saida kununaya da zobo ba ana wannan sanyin, a matsayinki ta starter ba lallai ne ki samu ciniki ba. 

Akwai sana'o'i da ake da competition sosai yanzu, to dole sai kin duba mai less competition for a starter. Saboda kar ki zo ki zuba kudi ya zamanto babu customers da zasu siya, ki fara da kadan sannan wanda zai fi saurin shiga.

Za ki iya fara sana'ar turaruka  kanana wadannan oil perfumes din nan na Arab. Kinga shi turare koda yaushe ana amfani da shi. Sana'ar snacks ki tallata tsakanin gidaje da unguwanni, yan uwa da abokan arziki.

Misali kin siyo turarukan akan 350 ko 400,za ki iya saida su 500 each.  Kinga kinada ribar 150 ko 100 each, kin sayo kusan guda 15. A 5k kina da ribar 1500 ko 2200. Ita riba ko ya take ba'a raina ta.

Daga nan sai ki raba riban biyu, rabi kisa a asusu, rabi ki qara a capital dinki wato uwar kudin. Kafin kice mi kin tara kudi masu yawa, wadanda za ki iya bunƙasa sana'arki, daga kanana kina saro harda manyan turarukan. Haka za ki rika yi.
Maybe kinga kin tara da yawa za ki iya canza wata sana'ar, ko kiyi improvising da kanki, ki zauna ki natsu kiga miya kamata kiyi wanda mutane zasu so shi, sannan ya zamo cikin farashi mai rahusa. Yanzu an samu cigaba, akwai internet kiyi amfani da internet wajen bunkasa sana'arki ta hanyar bincike sabbin dabaru.

Idan na samu dama zan kawo bayanin yanda za ki tallata hajarki.

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa