#FreePadsForGirls

#FreePadsForGirls

Ina ta samun sakonni akan kamfen dinmu na #FreePadsForGirls, da yawa sun nuna farincikinsu da kuma goyon bayan su akan kamfen din.
Alal hakika abu ne mai muhimmanci mu haɗa hannu wajen ganin wannan kamfen ya isa ga jami'an gwamnati.
Ba dole sai pads din nan sun zama kyauta ba, a'a akalla ace dai an rage kaso mafi tsoka na farashinsu. Da yawan iyaye ba lallai bane su san muhimmancinsa ga ƴaƴa mata, sannan su iyaye ma ta ba kasafai mazajensu ke siya masu ba, sai fa mazaje yan boko da ke sako shi a provision.
Yaran talakawa kuwa musamman na kauyuka ba ta pad iyayen suke ba, ta ya ya za'a ci abinci suke yi.
Idan muka yi duba da package guda na Virony sanitary pad 700 - 800 yake, wane uba ne a kauye zai cire 800 ya siya pad ga yarinya daya, yana ganin wannan ya isa ya siya kwanon abinci ko zaman teburin mai shayi.
Sannan akwai matsalar da yawa yaran nan basu san yadda za su yi amfani da pads din ba, basu san yanda za su kula da kansu ba. Rashin menstrual hygiene ba karamin barazana bane ga lafiyar ɗiya mace. Hakan na janyo infections. Sannan basu pads din ba tare da sun kula da kansu ba, kamar canzawa sau uku ko hudu a rana,tsaftace jiki. Saboda a lokacin pores din da ke jikin mace a bude suke dole sai ta linka tsaftace jikinta fiye da lokacin da ba na menstrual period ba.
A dazu na tattauna da wasu daga cikin yara mata akan sun ma san pad din, wadannan yara daga kauyuka suke. Koda na fara tambayarsu kunya ta hana su sakewa, da kyar na shawo kansu suka yi magana. Sun fada mun cewa suna dai ganin pad din wajen colleagues dinsu amma basu san amfanin sa ba.
Na sake tambayar su shin da mi suke amfani a lokacin al'adarsu? Sun fada mun cewa da tsumma ne.
A iya tattaunawar da mu ka yi akwai bukatar ayi creating awareness a makarantun mata akan menstrual hygiene before azo maganar bada pad ma. Saboda koda an bada pad din idan basu san yanda zasu kula da kansu ba bayar da pads din bai da amfani. Saboda shi wannan disposal pads din are not hygienic like reusable ones.
Reusable pads are more hygienic and durable, Sannan su kashe kudin bai kai na disposal ba. Mace za ta iya amfani da disposal pads guda biyar ko shidda a shekara daya. Abinda aka fi bukata shine wannan hygiene din.

Ayeesh A. Sadeeq
26-11-2018
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa