SANNU BA TA HANA ZUWA

SANNU BA TA HANA ZUWA

  AYEESH CHUCHU

 

Ya kai ɗan uwana, ka ganta kana so koh? Kana son aurenta, kana son ta zama uwar ya'yanka koh?
  Idan har kana son ta haura waɗannan matakai, sai ka bi a hankali, kar ka yi garaje.
Sai ka fahimci wacece wadda ka ke son ta taka waɗannan matakai.
Shin ka san wacece ita?
Mi ya ja ra'ayinka ka ji kana sonta?
Wadanne halaye suke burge ka a tattare da ita?
Shin iliminta da wayewarta (ba wayewar 'yan bariki ba) sun ma ka?
Shin ka taɓa cin karo da wani hali na ta mara kyau? Wanda ka ke jin za ka iya zama da ita.
Shin ita ɗin ka ke so? Ko kuwa wani abu na ta. Shin kana tunanin za ta iya ba ya'yanka tarbiyyar da ta dace?
Shin ita ɗin ka taɓa cin karo bacin ranta ko a lokacin da take cikin bakinciki? Ta ya kake tunanin za ka iya shawo kanta a irin wannan yanayi?
Shin za ka iya canza wasu daga cikin dabi'unta wadanda basu dace ba?
Shin kai ɗin za ka iya tsaya ma ta a lokacin tsanani da wahala?
Shin za ta baka  farin ciki da kake bukata?
Shin wane dalili ne ya jawo hankalinta a kanta?
Shin za ka iya zama da ita a kowane hali?
Kadan kenan daga cikin wasu tambayoyin da ya kamata ka yi ma kanka kafin ka tsunduma a neman aure.

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa