MU GANE BAMBANCIN DAKE TSAKANINMU

Kadan daga cikin maza ne suka san abinda mata ke so, haka ma a bangaren mata. Wanda rashin sanin taƙamaimai halayya da bambancin jinsi na daya daga cikin ababen da ke kawo matsaloli acikin zamantakewa.

Jiya muna magana da wata kawata ke mun maganar saurayinta bai yawan kiranta kamar yadda na wance ke yi.
Sai nake tambayar ta shin idan bai kira ta ba ita tana kiran shi ko tura ma sa sakon sms?
A yanda ta nuna mun ita ba za ta iya ba, tunda har shi bai kira ba.

Kunga kenan daga an dau lokaci basu hadu ba, bai kira ta ba, ita ma ba ta kira ba shikenan soyayya ta bi ruwa.
Maza ku gane mata na son kulawa komin kankantarta, ka kira ta koda ba ka da abin cewa, tambayarta ya ranarta ta kasance anan za ka ji labari tiryan-tiryan. Saboda muna son Magana, muna son a tambaye mu mu bada amsa.
Wanda a wajen maza kuma ba haka bane.
Daga zarar ka dau lokaci ba tuntubi mace ba duk irin son da kake ma ta, ba za ta gane ba, matuƙar bata fahimci bambanci duniyar da ke tsakanin ku ba.
Da farko za ta fara tunanin wane ya daina so na, wane ya sa mu wadda ta fi ni, wane ya yaudare ni, tunani kala-kala zai ta zuwa ma ta a rai. Ita kuma fa ba za ta kira ka ba, don kar ta zubar da ajinta.
Wanda al'ada ce da aka taso da ita tun kaka da kakanni namiji ke bin mace. Sai dai yanzu da zamani ya canza. Duk da haka mace na da wannan feelings din, duk yadda ta kai ga sonka tana dannewa taƙi nunawa matuƙar ka ki ba ta kulawar da take so.
Ya faru da ni a da, amma a yanzu da na fahimci yanda duniyar maza take, na fara gane bambamce-bambamcen da ke tsakaninmu sai abin ya zo da sauki. Nasan cewa hali ne.
Sai dai mi, akwai bukatar maza da mata a hadu wajen fahimtar difference dake tsakanin jinsi nan guda biyu, ta nan ne zaku iya warware matsalolinku, don wani abun bai kai ya kawo ba sai ya rushe soyayyar da ake dade ana ginawa.

Ayeesh Chuchu
11-03-2018

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa