YAUDARA

YAUDARA

Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Na dade ina son inyi magana akan wannan maudu'in amma ban san ta ina zan fara ba, ataikace sai na fara typing sai in rasa abin rubutawa ba wai dan ban san mi zan rubuta, sai dan yadda maudu'in ke da sarkakiya, ta yanda nake son ya kasance balance ta kowane bangare.
A kullum yaumin ina son in ja hankalin yan uwana matasa maza da mata da mu ji tsoron Allah mu kuma kyautata niyyar mu akan duk abinda muka sa a gaba.
A kwanan nan na ji cases da basu kirguwa akan wane ya yaudari wance, wance ta yaudari wane. Shin mi muke so mu zama ne? Duniyar nan idan ka ji wasu abubuwan da ke faruwa sai ka ji mutanen kansu na sure ma ka, soyayyar ma na fita daga ranka, saboda amana tayi karanci. Duniyar ta zamo so scary.
A nawa tunanin da ra'ayin banga amfanin soyayyar da ba za ta kai ku ga aure ba, to don mi za ku yi ta bayan kun san ba auren juna za ku yi ba, yafi tun farko kar ku samo abinda ku ka san ba za ku iya karasa shi ba.

Kace kana son yarinya, ka gama hure ma ta kunne ta gama korar duk samarinta, babu kowa a standby, kawai ba amo ba tsammani Alaji sai ka rabe gefe ka je ka nemo wata, sannan kana lallabowa wajen side babe kana kashe ta da kalaman yaudara idan anan kadai ka tsaya.
Kawai sai dai ta ji an daura ma aure, ko an kai gaisuwa. Ta yiwu ma ta tambaye ka, ka hau wallahi tallahi karya ne. Ka kara daura ta akan famfon iska, kana fada ma ta"no one but you ".
Ita kuma da yake ta samu Toshewar basira, tayi gam dakatar da tukunyar giyar soyayya bata bambamce tsakanin fari da baki bare kuma abu da ya hada da" the love of my life " Shikenan magana ta kare.
Sanda za ta ankara da yaudarar ta kake yi lokaci ya kure ma ta, a sannan za ka lallaba ka tafi ka barta anci moriyar ganga.

Ita kuma a lokacin ne za ta fara dana sanin tarayyarku da ita, idan mai hankali ce direct wajen Allah zata kai karar ka, ka dai san addu'ar wanda aka zalunta, ta fara "Yaa Allah dan girman al'arshenKa, dan karfin MulkinKa, dan soyayyarKa da rahamarKa ga bayinKa. Kai ne Al Azizu, Al Jabbar, Kai ne Arrahmanu Arrahimu, dan tsarkin mulkin Ka dan soyayyar Ka ga Manzon Rahama Annabi SAW, Ya Allah Audu da ya zalunce ni Ya Raheemu ka saka mun akan wannan zaluncin yayi mun.
Tana kuka tana fada ma, kana tunanin za ka tsira ne?
Idan kuwa ba mai tawakkali bace, wallahi Allah sai tabi duk hanyar da za ta bi wajen ganin ta tarwatsa dan qanqanin farincikin da kake samu, sai kaga al'amura na dagulewa.

Haka a bangaren mata ma, idan kin san ba auren shi za ki yi babu amfanin kullum ki zauna kina yaudarar dan mutane, kina nuna ma shi babu wanda kike so sai, ya dau dukka hope dinsa ya daura akanki, yana ganin future din shi a tare da ke. Wani ma har ta kai tunanin sa da rayuwar sa gaba daya dake yake gina ta a matsayin uwar yayanshi. Kawai sai ki tarwatsa wannan plan din na shi. Kina tunanin Allah zai bar ki haka?
Tun farko gara ku fito ki fada masa, wane ina da wanda nake so zan aura. Duk da shi aure mukaddari ne daga Allah, ina ma ka addu'ar Allah ya hada ka da alkhairin sa a duk inda yake. Nagode da kulawar ka a kaina. Shikenan kunyi rabuwar mutunci ana ganin mutuncin juna.
Amma kin zo kin tara samari sama da goma kowane cewa kike babu wani sai shi, shin hajiya kin nema ma kanki zaman lafiya kuwa?
Mu tuba! Mu san cewa irin wadannan kananan abubuwan da muke raina wa suke jaza mana rashin kwanciyar hankali da zaman lafiya a rayuwar mu ta zamantakewa.
A kullu halin mu kasance masu kyautata niyyar mu akan kowace alaka da zamu kulla, shi fa Allah baya daurawa bayin Sa abinda ya san ba zasu iya ba.
Sai abu ya afku mu daurawa shaidan ko mu ce kaddara ce, akwai Kaddarar amma son ran mu yafi yawa fiye da Kaddarar.

Cases da naji just recently cikin satin nan akan irin wadannan abubuwan suna da yawa. Zalunci ne babba, ku maza kuna gaba da mata. Matukar ka san ba ka halin auren mata biyu don mi za ka hada yan mata biyu a lokaci guda, kowace kuma ka nuna da ita kake yi, sai daga baya ka zame kar barsu. Ka zalunce su ka kuma zalunci kanka.

Addu'ar mu a kullum idan Allah zai jarabce mu ya jarabce mu da abinda imaninmu zai iya dauka. Ya kuma hada mu da masu son mu dan Allah.

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker #thefragiletable.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa