Social Media Relationships

Soyayyar social media tana zama ruwan dare a tsakanin ma'abota shafukan, sai dai mi? Tana tattare da illoli musamman ga mata. Da yawa ba son Allah da annabi bane, maybe ana neman wajen rage zango ne, ya gama firarshi da budurwar shi ke kuma sai a dawo kanki Hajiya Sidechick🤦🏽‍♀,nan za a kashe ki da kalaman soyayyar da ke narkar da zuciya ki ji no one but him. Shikenan ke amfanin ki a debe kewa dake. Tunda kuke bai taɓa furta "I'm on my way to see you" ba, Kullum aikinsa "Babe! I love you with all my heart ♥", emojis love kamar dan shi aka yi su, ga shegiyar karya da dadin baki. My sister you're fooling yourself, he's not worth your time and resources,kina ji na ko? 🙄, hope I'm making sense here? 🤣.
I'm not condemning social media relationships, tunda akwai wadanda suka yi kuma sun dace, amma ba shi zai baki license na ba kowane trash damar tunkararki ba, ki saurari wannan ki saurari wancen ke kenan ba ki da alkibla, ba a ce kiyi wulakanta mutum ba, tunda ba'a san inda ake dacewa ba. Amma ki natsu ki san wa za ki kula.
Duk namijin da ke son ki da aure wallahi tallahi haduwarku ta farko, ta biyu ta uku auren na ne a gaban shi. Idan birnin Sin kike zai zo ya same ki kuga juna, har ku amince da juna. Daga nan iyayenki zai tunkara dan neman izinin riƙa zuwa zance wajen ki. Idan sun amince Falillahi hamdu, idan basu amince ba bisa wani dalilinsu mai karfi sun fi ki sanin abinda ya dace da ke, ba kuma zasu cutar da ke ba. Wautar da muke yi fara soyayya ba tare da neman yarda iyayenmu ba. Sai anyi zurfi iyaye su ce basu yarda ba a samu matsala. Dayan biyu cikinku wani yace daya ya yaudare shi.
Nemi zabin Allah dana iyayenki.
Amma duk saurayin da zaku hadu da shi walau a online ko a fili kullum sai aikin Baby ke kadai nake so a rayuwa ta,Kullum zancen shi kenan, bai taba furta zai zo ganin ki ba bare maganar aure ta shiga kullum sai zancen banza da wofi, yaudararki zayyi, block the idiot, ba shi ya siya ma ki wayar ba, babu kwandalarshi a datarki.
I'm warning you, ki kula kada sai kinga pre-wedding pictures ko post-wedding pictures ki ce an yaudare ki, ki dame mu da DM da emails a taimaka ma ki wane yayi aure ya bar ki, ya yaudare ki. My sister tun farko ke kika yaudari kanki. Kin bata lokacinki a banza, kin kori masu sonki tsakani da Allah. Ki natsu ki hankalta shawara ce wadda ko Kanwata ta jini iya abinda zan fada ma ta kenan.

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa