LOKACI

LOKACI

Kowane dan Adam yana da lokacinsa na wanzuwar abubuwa a cikin rayuwarsa. Wani kan gama karatu da wuri ya kere ma sa'oinsa, wani ya samu aiki da wuri, wani yayi aure da wuri da sauran ababe makamantan hakan.

Haka kuma kowa da tasa ƙaddarar a rayuwa, taka daban haka kuma tawa ƙaddarar daban, abin da ake so dai mutum ya yarda da kowace irin ƙaddara walau mai kyau ko akasin haka.

   Mutane kan yi kuskuren fahimtar waye kai da kuma abokinka, ta iya yiwuwa abokinka, dan uwanka ko makwabcinka ya riga ka samun nasara a rayuwa, ya samu shahara cikin ƙanƙanin lokaci amma kai shiru kamar an shuka dussa. Mutane zasu danganta ka da marar nasara a rayuwa ko wani wanda ya gaza samun nasara.

  Sun manta cewa kai da shi ba hanyarku ɗaya ba, ba kwazonku ɗaya, ba haka aka ƙaddaro ma ku ba, kuna da bambamci. Kowanen ku nada tsarin ta sa rayuwar.

  Kadan daga cikin mutane ne zasu yi hakurin ganin cigabanka, wasu zasu yi ma dariya wasu zasu yi ma gwalo, kai wasu har zunɗe da yafice zasu ma duk a ganin su KA GAZA.

  Daga ranar da su ga ka fara samun cigaba a rayuwa daga ranar za su fara tururuwar ganin nasararka, za su fara maganganu akan yadda ka samu cigaba a rayuwa irin wacce ba su yi tsammani ba, tun fa ba ka ida cimma nasara ba, saboda sun hango nasarar a tattare da kai.

Sun manta cewa ko fa yatsunmu ba dai-dai suke ba, haka ma rayuwar wani da wani ba ɗaya take ba.

  Daga ranar da ka hango ko ka ga nasara a tattare da kai, za ka tabbatar da cewa lokutan da ka ɓata wajen cimma burinka basu tafi a banza ba,dan kuwa kai kadai kasan irin ƙalubalen da ka fuskanta a rayuwa kafin ka cimma nasarar.

  Ka da ka yi hanzari a rayuwa dan wane ya cimma kaza ya zamanto kaima sai ka cimma masa, ka zamo mai haƙuri dan ita ƙofar masu haƙuri ba a cunkushe ta ke ba, ƙalilan ne mutanen cikinta waɗanda suka zamo masu neman cimma nasararsu cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

   Shi fa Ubangiji Madaukakin Sarki da ya hallice ka Ya san dalilin zuwanka duniyar nan, kwanakin da za ka yi, mi za ka zama, Ya riga ya gama tsara ma ka rayuwarka, kuma ya san mi kake ciki a Rayuwarka dan kuwa SHI masanin dukkan al'amura ne.

Kar ka yi garaje a rayuwa, bi a sannu har ka cimma nasara. Toshe kunnuwanka ga duk masu tunanin ba za ka kai ba, wadanda su ne mutane na farko da zasu fara mamakin nasararka.

Miƙa ma Allah lamurranka, sai ya zamar ma ka jagora a rayuwarka.

Ayeesh Chuchu
30-03-2018

#ayeeshchuchuwrites

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa