DA SAURAN RINA A KABA

RANAR MATAN KARKARA TA DUNIYA

DA SAURAN RINA A KABA

Ayeesh A. Sadeeq
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

Idan aka yi la'akari da yanayin da matan karkara ke ciki bana tunanin an samu wani cigaba na azo a gani ba.
Musamman idan aka yi duba da yawaitar kananan yara dake qara fantsama a cikin harkar nan ta tallace-tallace.
Wadannan ƙananan yara mata sune ake jefawa cikin halin ha'ula'i, musamman yawaitar cin zarafin su da ake yi nayi masu fyaɗe, yara ƙanana ana samun su dauke da cikin shege a dalilin haiƙe masu da ake yi, ko kuma da ra'ayin kansu ta hanyar yi masu romon baka.
Su fa mutanen karkara ba kasafai suke kallon gidajen talabijin ba, karanta jaridu da kuma sauraron Radiyo. Babbar hanyar da ya kamata a bi wajen wayar masu da kai bai wuce ta hanyar community outreach.
Wannan kira ne na musamman ga kungiyoyi masu zaman kansu da su taimaka a wajen ganin an rage mafi yawa daga cikin kason matsalolin da ake samu a karkara.
Ta fannin tallace-tallace da ƙananan yara kan yi, nayi duba da nazirin cewa ba zai yiwu iyayen wadannan yaran su yarda da a hana yaran su tallace-tallace ba, ba komi ke sa su wannan tallace-tallacen ba face talauci.
Kenan ba zai yuwa ka toshe ma mutum hanyar samun sa ba, ba tare da ka nema masa mafita ba.
Idan har ana son a dakile yawaitar tallace-tallacen nan sai an tabbatar iyayen yaran nan a nema masu sana'ar da zasu rika yi a gidajensu wanda baya bukatar sa hannun yaran. Hakan zai ba yaran damar fita neman ilimin Arabi da boko.
A fannin iyaye mata kuwa a karkara za a same su cikin mawuyacin hali mai tattare da zalunci da takura daga mazajensu. Suna rayuwar aure ne bisa ga jahilci, namiji zai tara mata hudu ba ci ba sha. Ta tallace-tallace su ka dogara, da ita suka ciyar da yaran su harda tufatar dasu. Mazan su kuwa daga zarar kaka ta zo to kakarsu ta yanke saƙa, wato lokacin sake-sake da aure-aurensu yazo.
Wani abun ban haushi da takaici sai kun je asibitoci za ku tabbatar da abinda nake fada, akwai yawaitar mata masu fama da cuta mai karya garkuwar jiki, wanda da yawa daga cikinsu basu san suna dauke da cutar ba. Sai a dalilin zuwa asibiti wala Allah wajen haihuwa ko a lokacin awo.
Da yawaitar mata masu fama da lalurar yoyon fitsari. Wanda yawanci saboda yawanci sun jahilci zuwa asibiti awo da haihuwa.
Kenan dai akwai sauran rina a kaba, sai an tallafawa wadannan mutane wajen fadakar dasu yanayin da suke ciki.

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker #Enlarge2018

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa