YOU CAN HAVE YOUR ROMANTIC DINNER DATE, A TSAKAR GIDAN KU GARI YAYI DUHU.. TAURARI SUN HASKA SARARIN SAMANIYA ..

Money
Money
Money!
Yes! We all love Money. Babu wanda zai ce bai son kudi, ko a ce wane ko wance kun cika son duniya. Muna son duniyar nan to the extend of wasunmu ma na mantawa da dalilin halittarsu a doron kasa. Wasunmu na mantawa da akwai Lahira.. 😂 So kar kace mun ba ka son kudi, I love Money🙈.. Amma mi? Kudi ba zasu zama number one priority din mu a rayuwa ba, a ce komi zamu gina muna gina shi ne based on money.. That's so bad..

Har ta kai relationships dinmu muna gina su saboda kudi. Mostly mu mata anan muke fadawa halaka da juyin juya halin rayuwa.
Ban manta ba someone sent me a message "Wai ke kina yi kamar ba ki son kudi waya san mi kike yi".... Murmushi nayi kawai.
Tabbas! Ina son kudi, shiyasa ma na daga dacewar in neme su da kaina, zan fi ganin value din su...
Mafi yawan mata na da burin auren mai kudi, ni fa banga laifin su ba. Laifin su daya, da suka sa kudin gaba da komi.
Mata nawa ke auren masu kudin amma ba su da kwanciyar hankali? Mata nawa ke auren masu kudi amma ba bu soyayya? Mata nawa ke auren masu kudin amma mazajensu basu da lokacinsu?

Matan masu kudi nawa suka fada harkar zina saboda rashin kulawar mazajensu? Miji ya tafi Italy, mata ta tafi Dubai🤨... Irin auren da kike mafarkin yi kenan? Auren kudi ko? Wehdone.

Lemme tell you a kullum sai na ji ko na karanta koken mata masu aure akan mazajensu..
Mu bar maganar social media da couples zasu sa pictures na junansu hugging each other, smiling and kissing Sai abin ya birge ki, kina mafarkin ina ma ke ce.. Baki san irin challenges na rayuwa da suke facing ba a BEHIND THE SCENES ba, abinda fa suke so suke nuna mana.

Ki auri wanda ya san mutuncin ki da na iyayenki, wanda zai supporting naki wajen cikar burinki, wanda zai ja hannun ki ya kai ki birnin mafarkin ki, yana tare da ke through the thick and thin, wanda duk kankantar abinda yake samu zai faranta ma ki rai da shi, kema kuma za ki yaba.. Kudi masu yawa basu ne farin ciki ba...
Kawaye kan iya zuga ki, su ce wance yanzu duk ajinki wane za ki aura? Ai kin fi karfin shi. Wallahil azeem idan kika biye su kin soye....
Kin san mi Allah ya tanadar masa a gaba? Wannan mutumin da kika raina kina ganin shi ba kowa bane, kika wulakanta shi akan Mr. Rich, wata rana ke da Mr. Rich kun zama nothing, that man da kika raina already yana da mission da vision, Sai ki gan shi ya zama wani abu.. A lokacin za ki ce oooh da yanzu fa nice matarshi.

What I want us to understand is that, ki auri miji mai ilimi both addini da na boko, kar ki kuskura ki auri jahili.. Ki auri wanda ke da mahanga a addinance da zamanance, idan kika kuskura kika auri wanda boko ta rinjayi addini sunanki shashasha, kika auri mai ilimin addini amma babu na boko sunanki sorry ☹ asalin sorry.. Don duk abinda kika yi da ya sha bambam da raayin sa, zai jahilce ki.. Kullum cikin rigima kuke.
Ki auri wanda kuke da kyakkyawar fahimtar juna.. Ki auri wanda zai taimaka maki wajen cikar burikanki, wanda zai dora ki akan hanya...

Kina mafarkin fita 5 star restaurants yin romantic dinner da mijin ki, you can have the five star restaurant within your locality dinku... You can be romantic at anywhere, da kudi ko babu kudi. It depends on your perception on how being romantic is....

You can have your romantic dinner date, a tsakar gidan ku, gari yayi duhu.. Taurari sun haska sararin samaniya.. Ga wani kamshin turaren wuta na tashi.. Kuna cin abinci kina rangwada da karairaya.. Laugh with your husband, ki fada mashi matsalolinki, ku tattauna future dinku..
Ni gaskiya I don't care with what society will say about my marriage lifestyle.... Duk ranar da kika fito daga gidan aure da sunan saki, kece a bar kyama, gulma da yamididi... Kiyi komi dan ki rike aurenki matukar ba shirka bane...

Ayeesh Chuchu

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker #thefragiletable #Enlarge2018

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa