BA KOWACE MACE KE NEMAN MIJI A SOCIAL MEDIA BA

BA KOWACE MACE A SOCIAL MEDIA KE NEMAN MIJIN AURE BA😟

"Kin rasa mijin aure, kin zo Facebook kina neman miji".
"Kin sa hotonki kina tallar kanki dan ki samu miji".
"Kina fira da maza dan ki samu miji".
"kina posts dan ki samu miji"..
"Kina mutunci da mazan Facebook dan ki samu miji".
Is that all you can say about girls on social media? Duk namiji mai wannan tunanin stoop so low Wallahi. Lemme tell you not every girl on IG, Facebook or Twitter is looking for husband.
Muna social media dan ra'ayinmu, muyi gogayya da mutane daban-daban, muyi sharing ideas, a sada zumunci. Ni ba zanyi jayayya da kaddara ba, coz a lot of people met their spouses on social media. Abu ne mai kyau matukar da kyakkyawan niyya aka yi shi. Idan ni Aisha mijina a social media zamu hadu, ina fatan alkhairi ya hada mu ba sharri ba.
Amma ku zo kuna maganar miji matan social media suka fito nema this is bad.
Yes! It's not a bad thing mace ta nemi miji, tunda ba za ta auri kanta ba. Tana bukatar abokin rayuwa, amma yanda wasu mazan ke disrespecting mata a social media is alarming. Ni banyi muzgunawa wani ba, ina ba kowa girman shi duk girman duk kankantar ka. What I believe is that girmamawan nan ba zai makale mun ba,bare har ya zama wani kayan gabas.
Ban manta da ku you girls sending nasty pics on social media, wehdone ma'am "women leader of neman miji association". Kina tunanin hakan shi zai jawo ma ki miji? Ko shi zai sa namiji ya so ki? Kinyi wauta kin kuma cuci kanki.
Da yace tura min pics jikinki na rawa za ki tura,yace "baby nude dinki nake so", saboda kin zama magnet, yana uwar duniya kina uwar duniyar but the positive and negative charges attract. Ke ce video call, daga ke sai spaghetti top, ko underwears.. Twisting and twirling sending pishurs and videos. Rayuwar ki ce, sai ranar da kika ga pre-wedding pics ko invitation card a social media ki rugo da gudu kina kin shiga uku kin lalace wayyo Boobo ya cuce ki, ya yaudare ki.. Ehnnn ashe ma?
Kin kuwa san mi kike fada, ko kuwa kinsha burkutu ne? Oooh na manta giyar soyayya ce kika sha, itace ta juyar da ke kika koma sha tara sha takwas..
Irinku ke bata ma sauran mata suna, ake tunanin duk wata mace a social media miji ta fito nema.. Irin she's desperate to get married. Sai Allah ya saka mana sunan da kuke bata mana.
Wasu sada zumunci ya kawo su, wasu don su bunkasa sana'arsu. Ke da yake iskanci ya kawo ki, ko Ince neman kudi kika zo yi SOCIAL MEDIA ga ki ga ta, wata babbar makaranta ce kika kawo kanki, malamai da ɗaliban makarantar taku yawa ne dasu, walau a koya ma ki ko ki koyas ya danganta da irin kwarewar ki your excellency gold digger.

Mu fa tuna fa duk abinda muka yi a social media yana nuna su waye mu, sannan mu ababen tambaya ne a kan yanda muka tafiyar da accounts din mu, ya rage namu.

Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker #thefragiletable #stakeholdersonmytable

Comments

Popular posts from this blog

TREND

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa