Matan Arewa

Okkkayyy!
Dan anyi maganar kishiya kun fi kowa tada jijiyan wuya.
Kece "wayyo Allah, ka cuce ka yaudare ni"..
Kwana biyu kuma ki fara "ai ta gama mallake shi".
  I'm fed up with "arewa women are not romantic"..
Ya tura dan SMS na kara jadadda soyayyar shi a gare ki.
Duk rawar ganin da yayi, you can't even reply with "I love you" idan wahalar typing kike. Yasan kin gani kin kuma yaba.
Haba! Kiyi laifi ba za ki ce "sorry" ba.
Ya yi ma ki kyauta babu "Thank you".

Da kin haihu shi kenan ya zama Baban Indo, dan wasa da hirar soyayya kunyi bankwana da su.
Da anyi magana ki ce yara.
Ko kin girma da haka.
In za ki fita kin iya kwalliya da kashe dauri, da kin dawo gida kin kama yawo da zani da shirt, ko daurin kirji. Dare nayi ki haye gado shi kenan.
Kin ajiye ma Baban Indo abinci, ya ci ko kar yaci ke dai ai kin girka.
Tsakanin ki da mijin ki sai dai maganar kudi "A bani kudin cefane, a bani kudin ankon bikin gidan wance, zan je gidan suna".

Ke gaba daya kwakwalwarki tana kan su Ali Nuhu da Maryam Yahaya, maganar ki dai yaushe sabon film zai fito.
Daga nan kuma sai Zee World, miji na fita kin fada Instagram ki kalli duk gulmar da ke faruwa, daga nan kuma ki fada WhatsApp group din Sirrin Mace nan za ki saki baki kiyi ta sharara surutu. Kin fi kowa murya, batsa babu wadda baki iya ba...
Daga nan sai ki dora spaghetti a wuta, idan kinyi abin kwarai kiyi stew, wata rana kiyi mai da yaji.

Ke baki da wani tunani gaba daya wanda zaki kawo cigaba a rayuwarki da ta iyalanki.
Daga gulmar gidan wance sai kallon fina-finan Kannywood da Bollywood.
Ba ki iya tabuka ma mijin ki da wata shawara da ta danganci aikin shi ko kasuwancinshi.

Ya samu yar bana bakwai dake langabewa ta kashe shi da soyayya, ki fada mun idan ba za ta mallake shi ba?

It's high time mu gyara dabi'unmu da halayenmu.

#ayeeshchuchuwrites #tableshaker

Comments

Popular posts from this blog

TREND

Cigaba Da Rayuwa

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE