#FreePadsForGirls
#FreePadsForGirls Ina ta samun sakonni akan kamfen dinmu na #FreePadsForGirls, da yawa sun nuna farincikinsu da kuma goyon bayan su akan kamfen din. Alal hakika abu ne mai muhimmanci mu haɗa hannu wajen ganin wannan kamfen ya isa ga jami'an gwamnati. Ba dole sai pads din nan sun zama kyauta ba, a'a akalla ace dai an rage kaso mafi tsoka na farashinsu. Da yawan iyaye ba lallai bane su san muhimmancinsa ga ƴaƴa mata, sannan su iyaye ma ta ba kasafai mazajensu ke siya masu ba, sai fa mazaje yan boko da ke sako shi a provision. Yaran talakawa kuwa musamman na kauyuka ba ta pad iyayen suke ba, ta ya ya za'a ci abinci suke yi. Idan muka yi duba da package guda na Virony sanitary pad 700 - 800 yake, wane uba ne a kauye zai cire 800 ya siya pad ga yarinya daya, yana ganin wannan ya isa ya siya kwanon abinci ko zaman teburin mai shayi. Sannan akwai matsalar da yawa yaran nan basu san yadda za su yi amfani da pads din ba, basu san yanda za su kula da kansu ba. Rashin menstru...