ABINDA MATA KE SO EP2 Mata na son namijin da ke da sense of humor. Wanda idan abin dariya ya kama zasu yi dariyarsu tare. Wanda zasu yi wasa ba tare da jin shakku ko dardar na cewa zai dau abin personal. Aa tana son wanda idan ta tsokane shi, shi ma zai taya ta tsokanar. Ba namijin da za ta kalla kullum daga maganar “I love you”, sai fa wani serious abu. Shi kullum bai san wasa.. Baya sa son wasa, yana forming elder elder... Baabaa baya son raini... We want someone that both of us can be stupid together.. Relationship da mutumin da bai da sense of humor akwai matsala... Kullum magana daya ce, har sai kin gaji da ita. Shi fa sam baya son abinda za ki raina shi. #ayeeshchuchuwrites #tableshaker
ABINDA MATA KE SO EP1 A mafi yawan lokutta maza kan yi ta korafin “wai ku mata mi kuke so ne?” “Ba a iya ma ku”... “Ba a birge ku”... Bla bla bla.... Har yanzu ba ku fahimci mi mata ke so ba, har wasu kanyi tunanin ba a birge mace ko wani abu makamancin haka. A duk inda mace take tana son namijin da zai rika motivating dinta. Ba wai ka zo ka zama motivational speaker ba😂.. Man! Wannan maganar motivation a relationship na ke magana a kai. Every woman wants a man that can inspires her, wanda zai iya taimaka ma ta a duk lokacin da ta bukaci haka.. Akwai lokuttan da mace za ta riski kanta cikin wani hali na damuwa da bakinciki, a wannan lokacin tafi bukatarka. A lokacin za ka iya lallashin ta da misalai maybe wadanda ma suka faru a kanka, ka nuna ma ta za ta iya wuce wannan wajen . Za ta iya zama kalar macen da take son zama.. Idan ta rasa wannan wajen ka, nan fa bestie ke shigowa, coz he will be there for her , he’ll cheer her up.. Zai ji matsalolin ta zai b...
Chuchu and LubnaSufyan calmlubna@gmail.com ayeeshasadeeq2010@gmail.com TREND Akwai abinda turawa kan kira 'TREND' da za'a iya fassarawa da wani abu sabo da zai shigo ko ince 'YAYI'. Kamar sabuwar shadda da samari zasu dinga yayi, burin kowanne a ciki ya mallaka, machine da makamantansu. A wajen mata kamar turare, dinki ko wani abu daya danganci kwalliya, wannan TREND bai tsaya a iya abubuwan amfani ba, har da wakoki ko finafinai da zasu shigo yan yayi. TREND dinmu na yau ta bangaren wakokine, wakokin da kan zo da salon rawa kala-kala. A shigowar 2018 din nan anyo wakoki kala-kala irin su Shaku-shaku, Kope challenge ga kuma sabuwa yar yayi wai ita collapse challenge Wadannnan kalolin rawa da su ka zo da rawar da burin kowanne matashi ko matashiya su saka wakar su kwaikwayi rawar. Ok! ba sai addini ya kai ga shigowa ciki ba, bara mu taba al'ada kamun muzo kan addini, akwai raye rayen da a al'ada ta malam Bahaushe ko namijin bai kamata ya yi ta ba balle h...
Comments
Post a Comment