RABUWAR IYAYE
RABUWAR IYAYE
Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com
11-07-2018
Muna cikin wani zamani da auri saki ya yawaita a tsakanin ma'aurata. Akwai dalilai masu karfi da ke assasa mutuwar aure.
Sai dai mi? Mutuwar auren na kawo matsaloli a rayuwar yaran da ke tsakanin ma'auratan. A irin wannan zamanin da mu ke ciki, iyaye ma na tare suna bakin kokarin wajen tarbiyyantar da ƴaƴansu ana samun matsaloli ina ga iyayen da suka rabu da juna.
Da yawan yaran hankulan su na rabuwa ne gida biyu, su kan rasa shakuwa ta iyaye da ƴaƴansu musamman idan daya daga cikin iyayen ke tare da ƴaƴan, kunga kenan sun rasa shakuwa ta daya bangaren.
Matuwar aure a tsakanin iyaye na jawo rashin yarda a tsakanin yaran, zasu riƙa kallon iyayen ta wata fuska ta daban, ana samun masu nuna ƙyayya ga daya daga cikin iyayensu saboda dalilinsu na ganin cewa watakila uban ne ya assasa rabuwarsu da mahaifiyarsu, ko kuma ta bangaren ita mahaifiyar ce musabbabin hakan.
Wasu daga cikin yaran basu samun kulawar da ya kamata a ce sun samu daga bangaren iyayensu, sai a samu akasi wajen rashin tarbiyya, ilimi da kuma sauran ababen da yaro ya kamata ya samu wajen inganta rayuwarshi.
Ta dalilin hakan sai yara su fada mawuyacin hali, iliminsu da tarbiyyarsu su samu naƙasu, su kan rasa wannan gatan da yaran da ke tare da iyayensu ke samu, ba su cika samun gatan a jawo su a jika ba, a nuna masu soyayya da kauna. Shiyasa idan matsala ta same su, maimakon su tunkari iyayensu da matsalar sai dai ina, a waje zasu nemi inda za a warware masu matsalolinsu, idan aka yi rashin sa'a sai a daura su a turbar banza.
Shawara ta ga ma'aurata su daure su cigaba da hakuri da juna, su kyautata mu'amalarsu da abokan rayuwarsu da ƴaƴansu, wasu matsalolin basu taka kara sun karya ba bare har saki ya shigo ciki.
Sannan gallazawa juna ba mafita bace musamman idan da yara a tsakanin, hakan zai kawo gaba a tsakanin ku da yaranku, duk yaron da zai tashi yau da gobe yana ganin iyayensa na fada za a wayi gari baraka ta shigo tsakanin iyayen da yaran.
Ku zauna ku fahimci junanku, ku kuma sauke hakkin da ke rataye a wuyanku walau mata ko miji, kowanne nada responsibilities dinsa.
Comments
Post a Comment