BIN YAN TSIBBU

BIN YAN TSIBBU

  Abin mamaki da takaici ne a ce mace na bin bokaye don ta mallaki namiji. Abin ban haushi da takaici yanda abin ya zama ruwan dare a tsakanin ƴan mata yanzu.
  To ke Jummala tun yanzu ba ki yi auren ba kin fara bin bokaye don a karkato ma ki da zuciyar shi, ina ga anyi auren ai sai abinda yayi gaba.
Shin kin gwammace ki siyar da Aljannarki saboda namiji?  Ki zo ki aure shi ba kwanciyar hankali, kinga kin zo duniya a zero za ki koma a zero.
Ki lura, ki kuma hankalta bin bokaye ba zai kai ki ko'ina ba face ga halaka, saboda imaninki tunin kin zubar da shi, kin kasa yarda da cewa Allah shi ke komi.
  Mi zai hana ki tashi ki roki Allah tsakiyar dare a lokacin da wasu daga cikin bayinSa ke bacci ki kai ma Sa kukanki kina mai imani da yaƙinin cewa shi zai amsa ma ki addu'ar ki, ya biya ma ki bukatar ki.
Abin da yafi daga mun hankali bai wuce yanda wasu ke bin bokaye da Malamam tsibbu ba fa dan su auri saurayi suke bin su ba, sai dan wata biyan bukata tasu ta banza ta wofi.
Ka laifin haɗa Allah da wani ga dattin Zina.
Duniya kadai da abinda ke cikinta suka sa a gaba, babu ma tunanin aure a ransu a irin wadannan lokuttan. Bukatarsu wane ya cika su da kudi da manyan wayoyi.
Ya kamata ku hankalta ku natsu, ku tuba ga Allah.
Wani mutum bai isa ya baku ko yayi maku abinda Allah bai so ba. To miyasa ku ba za ku tashi ku roƙe shi, kuna masu kankan da kai. Sai ku ga addu'ar ku ta karbu fiye da tunaninku, shi fa Allah mai jin roƙan bayinSa ne, mai rahama da kuma jin ƙan mu ne.

Allah shi kara shiryar da mu hanya madaidaiciya. Amin

Ayeesh Chuchu
25-02-2018

Comments

  1. wannan gaskiya ne. Neman duniya ake tayi an manta da Allah. Allah ya kyauta.amin

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Matan Arewa

ABINDA MATA KE SO (EP1)

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA