BULALIYA
Nayi mamaki kwarai! Wace irin rayuwa ce wannan? Kayi abu wanda za ka cutar da kanka, ka saɓi Ubangijinka duk don mutanen duniya su yaba, ko ince don samun common likes and comments on social media.
It's very unfortunate yanda wasu matan su ka mayar da kansu da rayuwarsu kazantacciya. Kin bi maza, kin bi mata 😏😫 duk don ki sami abin duniya ki shiga sahun slay Queens, peppe dem gang, ki zama one in town, ki wuce ana kun ganta can, she's hot and sexy.
Yaa Allah! Abinda kike so a ce ma ki kenan? Hot 🔥! Wato ke zazzafa ce irin abincin nan mai shegen zafi ko? To sannu wuta uwar yan zafi, wallahi Allah zaki gamu da Ubangijinki idan ba ki tuba ba, kin riƙe mutuncinki.
Miye sutura? Miye waya? Miye mota? Dukkansu abubuwan da ke tafiya da zamani daga anbar yayinsu shikenan fa sun tashi aiki, ko kuma su lalace.
Ki ce yau a Habuja, gobe a ganki Lagos, jibi kina Kano, gata kina Dubai, ko kafar kare kika ci iyakar yawon da za ki yi kenan.
Da anyi magana kice ke taki kaddarar kenan,zaluntar kanki kike don ita addu'a tana kore mummunan kaddara, sannan tsayar da sallah yana hana aikata munanan ayyukan alfasha.
To yaya ma za ki yi sallah, after all kanki akwai wig, akaifarki kinyi fixing nails, girar idanunki kinsa eye lashes. Duk abubuwan da aka haramta kin aikata su, tun daga alwala ma kin fadi wanwas, bare aje ga sallah.
Ki tuba kafin mala'ikan daukar rai, ya dauke ki a yanayi irin wannan.
Astaghfirullah!
#ayeeshchuchuwrites
Comments
Post a Comment