SON ABIN DUNIYA
SON ABIN DUNIYA A TSAKANIN ƳAƳA MATA
Ayeesh Chuchu
ayeeshasadeeq2010@gmail.com
Muna cikin wani zamani da matuƙar za'a samu abin duniya to idanun kan rufe ne ta kowane hali domin samun cikar buri.
Hakan yasa mata ma ba'a bar su a baya ba, wajen ganin sun sami abin duniya ta kowane hali. Wannan ya samo asali ne daga rashin wadatacciyar zuciya na wasu daga cikin mata, musamman ma ƴan mata a wannan zamanin.
Har ta kai ta kawo mace kan iya zubar da ƙima da mutuncinta wajen ganin ta sami abin duniya.
Akwai abubuwan da ke jawo son abin duniya ga ƴaƴa mata wanda sun sha faruwa kuma suna kan faruwar. Kadan daga cikinsu sun haɗa da:
-Rashin cusawa yara tsoron Allah, daga inda yaro ya tashi ba a cusa masa tsoron Allah ba a duk inda yake, to tabbas dole a samu matsala. Wannan tsoron Allah ne zai taimakawa yaro a duk inda yake iyaye basu da shakku akansa, saboda duk abinda zayyi zai tuna da cewa Allah da ya halicce shi na kallonsa. Hakan take a wajen ɗiya mace, matuƙar aka cusa ma ta tsoron Allah duk inda take za ta kasance cikin taka tsan-tsan, koda tayi niyyar kauce hanya tsoron Allah nan ba zai bar ta.
Amma idan yara suka tashi da tsoron iyaye, za'a samu matsala saboda a gaban iyayen ne kadai zasu iya zama nagartattu, amma daga zarar sun bar gaban iyayensu to abinda suka ga dama shi zasu yi.
-Rashin sauke hakkin iyaye akan ƴaƴansu. Yana ɗaya daga cikin musababbin da ke jefa mata cikin mawuyacin hali. Idan aka yi sa'a da yarinyar da ba ta kai zuciyarta nesa ba, sai ta faɗa ga halaka. Ire-iren hakan na faruwa sosai, musamman iyayen da kan tura yaransu makarantun gaba da sakandire ba tare da sun dau dawainiyar yaran ba. Hakan kan jefa yaran cikin halaka, daga yarinya ke fara koyon siyar da mutunci da ƙimarta don ta ga ta samu abubuwan bukata na rayuwa.
-Hulda da ƙawayen banza, yana daga cikin abubuwan da ke rura wuta a zuciyar mata musamman matasa, ta inda idan aka yi rashin sa'a da raunanniyar zuciya garesu to cikin ƙanƙanin lokaci su kan bi ra'ayin ƙawayen su. Saboda tasirin ƙawaye a rayuwa su kan bada gudunmuwar su, kamar yadda Bature ke cewa "Show me your friends, I'll tell you who you are". Wanda Malam Bahaushe yace "Abokin ɓarawo, ɓarawo ne".
Wanda alal haƙiƙa kadan daga ciki ne kan tsallake wannan siradin.
A yanzu idan mace bata saka suturu na kece raini, ba ta riƙe manyan wayoyi da sauran abubuwan ƙawa na rayuwa sai ta zama koma baya a cikin ƙawayenta. Hakan ke sa da yawan ƙawaye kan zuga ƙawayensu wajen bin gurbatacciyar hanya don su sami abun duniya.
-Son zuciya da sa ma rai abinda kasan ba za ka samu ba. Wannan matsala ce babba mai zaman kanta, mata na da dabi'ar idan wance tayi abu to nima sai nayi shi ko ta halin ƙaƙa ne. Shine ke jefa da yawan matasa mata ga halaka. Daga nan zasu fara bin maza wadanda dama su abinda suke nema kenan, su kuma matuƙar za'a biya masu bukatar su ta yau da kullum, shikenan zasu iya komi domin ganin sun shigo cikin tsararrakinsu sanye da tufafi na alfarma.
Wadannan na daga cikin matsalolin da ke haifar da son abin duniya ga zukatan mata wanda har ya kai su ga halaka.
Har ta kai ta kawo ƴan mata sun san su je gidan boka, don a mallake masu saurayi da zai riƙa cika ma su jakka da kudade da abubuwan more rayuwa. Babu ruwansu da mai gaba za ta haifar, matuƙar buƙatarsu ta biya shikenan.
Basu tsaya a nan ba, har sai sun tabbatar da cewa ba su kaɗai bane suka faɗa ga halaka, sai sun jawo ƙawayensu sun nuna ma su wannan hanyar itace hanya mafi dorewa a gare su.
Truth. May Allah guide us,amin
ReplyDelete