Posts

Showing posts with the label kasidar juma'a

LALE MARHABIN

Image
Lale marhabin da zuwan wannan rana Ranar da garin Makka ya haskaka Ranar haihuwar fiyayyen halitta  Ɗaha Musɗafa baban Zarah Duk mai son Ɗaha ya so ahalinSa Miji ga Khadijatu, angon Aishatu Amini ga Abubakar Saddiqu Siriki ga Aliyu ɗan abi Talib Zuwan Ɗaha duniya ta haskaka Ya kawo mana hanyar shiriya  Domin tsira a gobe ƙiyama Muna ma su Haske da walwali Ɗaha ya zo mana da littafi  Wanda anka kira da Qur'ani Saƙo daga sarkin sarakuna Allah mabuwayi gagara misali   Ɗaha mai kira zuwa ga tauhidi  Domin tsira  a hawan siraɗi Ɗaha masoyi ga al'ummarsa Ya roƙi salama ga al'ummarsa Mu so Manzonmu mai dubun falala  Kyawawan halayen Ɗaha sun yawaita  Duk wanda ya yi koyi da shi ya rabauta  Kowa ya ƙi Ɗaha ya kafirta  Lale marhabin da wannan rana  Ranar haihuwar fiyayyen halitta  Ɗaha Musɗafa baban Al-Qaseem Kaka ga Hassan da Hussaini Ya Allah ka dado tsira  Ga Manzonka mai farar aniya Don shi anka ƙ...