Posts

Showing posts with the label ZAMENTAKEWA

JIN ƘAN IYAYE

JIN KAN IYAYE   © Ayeesh Chuchu   Muna cikin wani zamani da ƴaƴa basu cika jin tausayin iyayensu ba. Ka yi girman da Allah ya hore ma ka amma ba za ka iya daukar nauyin iyayenka ba. Iyayen nan fa su suka raine ka har ka kai wannan matsayi da ka ke a yanzu.    Su suka tarbiyyantar da kai har wata ta gani ta kyasa. Bayan Allah madaukakin sarki babu halittar da ta cancanci godiya irin iyaye da su ka kawo ka duniya har ka zama abin da ka zama a rayuwa.   Allah SWT ya umarce mu da mu kyautatawa iyaye matukar kyautatawa. Wanda a yanzu kadanne ke kyautatawa iyaye, hakan yafi yawa ga maza waɗanda hakkin iyaye yafi rataya akawunansu, wasu daga sun yi aure sun fara tara iyali shi kenan sai su fita harkar kyautatawa iyaye, sun fifita iyalansu sama da iyayensu. To ɗan uwa bari ka ji, iyalanka da ka kyautatawa sama da iyayenka yanda ka yi ma iyayen nan suma sai sun maka sama da haka. Yanda ka ke kyautatawa iyayenka haka yaranka za su taso da...

ADDU'A MAKAMIN MUMINI

ADDU'A MAKAMIN MUMINI ©Ayeesh Chuchu  Ina matasa marasa aure?    Kun taɓa kawowa a ranku cewa addu'a babban makami ne  a yayin da ka/ki ke neman aboki ko abokiyar zama?    Ita addu'a makami ce ga mumuni, tana kaɗe masifu da dama.    Idan san samu ne tun kafin ka/ki yi aure ya kamata a fara addu'a ga abokan rayuwa.  Misali ke mace  Yaa Allah Ubangiji sammai da kassai, sarkin sarakuna, Kai ne mai rahama da jin kai, kai ne mai biyan bukatun bayinka. Yaa Allah Kai kace mu roke za ka amsa mana.   Yaa Allah Ka ba ni miji nagari, wanda zai soni, ya kaunace ni, wanda zai kula da ni, wanda zai kyautata mun,wanda zai tsayamun duk tsanani duk wuya. Yaa Allah Ka dauwamar da soyayyata da kaunata a cikin zuciyar mijina. Yaa Allah Ka bani Ikon yin biyayya ga umarnin mijina, ka bani Ikon kyautata masa, ka sa in zama mace ta gari a gidan mijina, Ka azurta mu da zuriya Dayyiba, ka bani Ikon sauke hakkin mijina da ya...