RASHIN YABAWA

RASHIN YABAWA

Yana daya daga cikin ababen da ke kawo rikici a zamantakewar ma'aurata rashin yabawa.
Miji na iya bakin kokarin sa wajen ganin ya kyautatawa matarsa sai a samu akasi ita sam ba ta ganin kokarin sa, duk abinda yayi sai ta kawo inda ba'a kyauta ma ta ba. Wanda hakan shi ke sa daga baya mazan su zame hannayensu a harkokin iyalinsu. Duk inda namiji yake bai fa son a raina kokarin sa, koda kuwa a zahirance ba haka abin yake ba, yafi son a kambama sai yaji dadi ya kara himma.

Haka kuma a fannin mata, mace na iya bakin kokarinta wajen kyautata ma namiji, amma shi a wajen sa ba abinda take yi. Idan girki ta yi sai ya samu inda aka yi kuskure, nan zai hau sababi, ba ya tunanin ba fa kullum take wannan kuskuren ba, miyasa ba zai fahimce ta ba.
Daga nan an dauko makaman wargaza ingantacciyar alaka, tun kowa na yi dan a kyautata ma juna daga karshe sai a daina. Kowa ya koma yin abinda yaga dama, abinda yaga zai iya.
Da haka yara ke tasowa abinda suka ga iyayen su nayi suma shi zasu yi, sai fa idan anyi arziki da yara masu matukar fahimta.

Ayeesh Chuchu

Comments

Popular posts from this blog

Matan Arewa

ABINDA MATA KE SO (EP1)

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA