ƊIYA MACE
ƊIYA MACE!
"Ladidi idan kin gama abinda ki ke,ki zo ke da Innarki".
"To Baba".
Dauraye hannuwanta ta yi,ta shiga ɗaki ta dauki mayafinta dake ajiye a
saman gado.
Ta leka madafi "Inna ki zo Baba na neman mu".
"to gani nan zuwa".
Tare suka isa ɗakin Malam Iro,ya kalli iyalinshi ya kaɗa baki ya ce "Ba wani abu yasa na kira ku ba sai dan in shaida maku cewa na karɓi kuɗin auren Ladidi, watan gobe za a ɗaura aurenta da Danjuma".
"Haba Malam duka-duka nawa Ladidin take? Shekararta sha uku fa".
"Wayyo Allah! Na shiga uku! Dan Allah Baba kayi hakuri ka bar ni in cigaba da karatu na".
"Ke dalla rufe mun baki, shashasha kawai, ana neman a yi ma ki gata kina wa mutane iskanci. Ba ruwana da shekarunta, Nana Aisha matar annabi ai ba ta kai Ladidi ba tayi aure. Babu babban mutuncin da wuce mace a gidan mijinta, mata nawa aka ma aure da basu kai ki ba? Dan haka na gama magana".
Ladidi ta gama kukanta ta gode ma Allah. Abin ya ba Inna haushi da takaici, amma ganin ba yanda za ta yi yasa tayi biris tare da yin kunnen uwar shegu da lamarin.
***
BAYAN BIKI
Kwance take a kan gado, zazzabi mai zafi ya rufe ta,sai rawar sanyi take.
Shigowar sa ɗakin, ta tashi zaune da kyar. Ta ce "Danjuma ka taimaka
ka kai ni asibiti".
"Haba Ladidi tunda ni ke a gidanmu ban taɓa ganin an kai wani asibiti ba, magungunanmu na gargajiya ake sha, dan haka kema shi za ki sha ba ni son wani san iyawa".
Ba ta kuma maganar asibitin ba, sanin halin mijinta mutum ne mai
tsatstsauran ra'ayi.
***
A kwana a tashi Ladidi ta fahimci ciki gareta.
Wata safiyar Talata ana cikin yanayi na damuna. Danjuma ya fito
sagale da fartanya a kafaɗarshi yana niyyar tafiya gona.
Ladidi dake bakin murhu ta buɗe baki, "Maigida akwai maganar da zamu yi naga har ka yi shirin tafiya gona".
"Eh, faɗi maganar ki sauri ni ke. Ku mata ba ku tashi yin magana sai kunga mutum na tsaka da uzuri".
"Dama gani na yi cikin nan ya kai watanni huɗu ya kamata in fara zuwa
awon ciki".
"Awo? Yau na ga ta kaina. Lallai Ladidi ni fa kin ga ban yarda da asibiti ba sam, ga sassake nan da Inna ta aiko ki rika sha. Ba fa kan ki aka fara haihuwar fari ba, kowa maganin nan na gargajiya ya sha".
Ya sa kai ya fita daga gidan.
***
BAYAN WATA BIYAR
"Wayyo Allah na", shi ne furucin da ke fitowa daga ɗakin.
"Amma dai ke raguwa ce Ladidi, daure,yi nishi mai karfi".
"Ma'u ban iyawa mu tafi asibiti kawai".
"Duk faɗin gidan nan babu wanda ya taba zuwa asibiti haihuwa ba za'a
fara ta kan ki ba, haihuwata biyar amma duk gida ni ke haihuwa, ki yi hakuri dai ki daure ki cigaba da nishin nan. Kowace mace haka ta sha wuyar naƙuda".
Kwanan Ladidi biyu tana naƙuda ba tare da ta haihu ba,a cikon kwana
na uku ne bayan ta matuƙar galabaita,ta samu damar sunkuto jaririnta.
"ayyiriririri", shi ne abinda Ma'u ke furtawa.
Sai can suka lura da cewa sama da minti goma jaririn be yi kuka ba
ya sagar ma su da gwiwa. Ma'u ta daga yaron ta jijjiga shi, shiru bai
ko motsa ba.
Hakan ya tabbatar da yaron be zo da rai ba. Salati suka saka, nan da
nan sauran mutanen gidan su ka taru aka tabbatar da jaririn ya rasu.
Ladidi ta fashe da kuka ganin duk wahalar da tasha saboda yaron ne
amma be zo da rai ba. Nan su kai ta bata baki har tayi shiru.
Kanwar mahaifinta Gwaggo Balaraba ta zo taya ta zaman jego duk da ɗan
be zo da rai ba.
Kwance take a gadonta, hawaye na tsiyaya daga idanunta. Tunda ta
haihu ta rasa gane kanta, sam! Bata iya riƙe fitsari. Ta kai hannu
kan katifarta ta ji ta jingim da danshin ruwa.
Gwaggo Balaraba dake tsaye bakin kofa ta ce "Ladidi wai wane irin
zarni ne ke fitowa daga ɗakinki? Shiyasa fa na daina zama ɗakin yanda
kasan an baza taki a ɗakin".
"Gwaggo nima ban san abinda ke damuna ba, tunda na haihu ban iya rike fitsari, kafin in tashi har ya zubo".
"Ladidi kina da hankali kuwa?
Kina fama da ciwo amma ki ka ƙi magana".
BAYAN KWANA BIYU
"Gwaggo lafiya naga kin dauki jakarki?".
"Lafiyar kenan Ladidi gida zan tafi ba zan iya zama ba, zarnin fitsarin nan ba karamin cutata yake ba".
"Dan Allah Gwaggo kiyi hakuri ki zauna,kinga duk gidan nan babu mai
zuwa kusa da ni yanzu, kyamata suke".
"Ni banga laifin su ba, wa zai tsaya ya taƙura kansa, ni kinga tafiyata".
***
BAYAN WATA SHIDA
"Ladidi ba zan iya zama dake a wannan yanayi ba,da kyar nike iya
numfashi a dakin nan saboda zarni. Abu ɗaya zan iya ma ki shine in
sauwake ma ki aurena da ke kan ki har zuwa lokacin da za ki samu
lafiya. Dan haka na sake ki saki ɗaya".
Kallon shi take galala, ta kasa motsawa saboda mamaki. Tayi karfin halin cewa "Danjuma yanzu kai ma kyamatata ka ke? Bayan kai ne sanadin wannan ciwon nawa".
"Koma mi za ki ce, ba zan iya zama dake ba kina zarnin fitsari ,muhallinki fitsari duk wani abu dake da alaka da ke ba shi da ɗaɗin shaƙa, ba ki da wani amfani fa".
Hawaye masu zafi suka zubo daga kwarmin idanunta. Bugun zuciyarta ya ƙaru fiye da tsammani. Maƙoshinta ya bushe ƙayau, ba ta tunanin ruwa zasu iya wucewa ba tare da ta ji zafi da raɗaɗi saboda mawuyacin halin da ta fada.
"Danjuma! Nagode Allah shi saka mun, abinda zan iya ce ma kenan".
Ta juya cikin ɗakin zuciyarta na ƙuna da suya.
Haka ta koma gidansu da zama, mahaifiyarta kadai ke dawainiya da
ita. Duk ta lalace tayi baki ta rame, bata da aikin yi sai kuka. Ta
tuno wasu tsararrakinta na makaranta suna karatu, amma ita gata nan kunshe a ɗaki babu mai zuwa wajenta.
Muryar mahaifinta ta ji, "Asabe ya kamata mu kai Ladidi asibiti na
gaji da wannan ciwo na ta".
"kamar kasan abinda ke raina Malam, ganin baka yi magana ba yasa na yi shiru".
Wani daɗi ta ji ya ratsa ta.
Asibitin da ke karamar hukuma aka kai Ladidi.
ASIBITI
Tana mamakin yawan matan da ke ɗakin akalla sun tasar ma ashirin.
Kuma a cikinsu itace mafi kankantar shekaru, wasu ma sun kusa jika da
ita. Tana yawan sauraren hirarrakinsu wanda yawanci akan dalilin zuwansu asibitin ne.
Babban abinda yafi damunta babu wani ɗan uwanta da ke tare da ita,
mahaifiyarta ce kadai ke zuwa dubata.
Ma'aikaciyar jinyar dake kula da su ta shigo, ta ce "Idan Allah ya kai
mu gobe za'a tafi da ku asibitin Babbar Ruga da ke Katsina inda manyan likitoci zasu duba ku".
Babu wacce a cikinsu bata yi murna da jin haka ba.
ASIBITIN BABBAR RUGA
Asibitin Babbar Ruga (National Obstetrics Fistula Center,
Katsina),asibiti ne da ke kula da lalurorin da suka shafi mata daga
daukar ciki har bayan haihuwa.
Satin su uku kenan suna samun kulawa a asibitin, ana ba su abinci
sau uku a rana da kuma sutura wanda gwamnatin jiha ta dau nauyin
hakan. Babban abin da ke damun Ladidi be wuce rashin ganin ɗaya daga cikin yan uwanta ba.
Watansu ɗaya a asibitin,aka zo aka basu alawus na Naira dubu bakwai.
Hakan ba karamin taimaka ma su yake ba.
Cikin ikon Allah Ladidi ta shiga sahun waɗanda za'a koya ma sana'a
dan su dogara da kan su bayan sun bar asibitin.
Inda Ladidi ta zaɓi sana'ar ɗinki.
BAYAN WATA TAKWAS
Ladidi na daya daga cikin ɗaliban da aka yaye wadanda aka koya ma sana'a.
Ranar da za'a shigar dasu ɗakin tiyata, ranar mahaifiyar Ladidi ta
zo, sun sha kukan yaushe gamo.
An shigar da Ladidi ɗakin da za ai aikin,addu'a take a ranta Allah
yasa a samu nasarar aikin.
Bayan wasu awanni sun shuɗe aka fito da Ladidi, inda aka canza ma ta
ɗaki zuwa na waɗanda akai ma aiki. Kwanan Inna biyu ta koma ƙauye.
Ladidi ta cigaba da jinyar jikinta har zuwa lokacin da zata samu
lafiya.
Ana gobe za su tafi aka tara su, inda akai lakca akan musabbin
abubuwan da ke janyo yoyon fitsari.
Inda likita ya fara da cewa " Yoyon fitsari da aka sani a turance da
Vesico Vaginal Fistula (VVF) wata cuta ce ko nakasa dake kama mata
bayan haihuwa. Ita wannan cutar tana samuwa a dalilin yaga tsakanin
gaban mace da mafitsara wadda take janyo yawan fitsari babu kakkautawa
daga gaban mace. Manyan dalilan dake janyo ta sun haɗa da: "Auren wuri da ake ma yara kafin su girma su isa daukar lalurar miji da juna biyu.
Idan aka samu tsaiko a yayin naƙuda ba tare da anzo asibiti ba, wato
dai daɗewar mace a naƙuda yana haifar da yoyon fitsar.
Sai matan da ake ma fyaɗe ta karfi da yaji. Sai kaciya da ake ma mata
ko wata tiyata da ta danganci mafitsarar mace duk suna kawo yoyon fitsari".
Likitocin sun jima suna bayani dangane da ita cutar yoyon fitsari.
Daga nan aka sallame su bayan haɗakar kungiyar Millennium Development Goals (MDGs), sun ba kowacce tallafin Naira dubu hamsin da za su dogara da kansu akan sana'ar da suka koya.
***
Hankalinta gaba daya ta tattara shi ga ɗinkin da take yi, ba ta ji
sallamar kaninta Habu da ya shigo ba,har sai da ya taɓo ta, sannan
yace "Yaya dama kuɗin makaranta za ki bani da kuɗin cefane, na duba Baba ya fita".
Jakar dake kusa da ita tasa hannu ta jawo ta mika ma shi ya fita.
Murmushi kwance a saman fuskarta ta furta "Allah nagode maka da na
samu lafiya, sannan zuciyata bata naƙasa ba har na dogara da kaina ina
taimakon 'yan uwana da iyayena".
Tunda Ladidi ta dawo daga asibiti ta fara sana'ar dinki a gida, duk ba wani gwanancewa tayi ba, hakan bai hana ta samun abinda za ta yi ba don rufawa kanta asiri ba.
Zaune suke a tsakar gidansu tana taya Inna tsintar wake.
"Inna ina da burin komawa makaranta".
"Kin yi tunani mai kyau gaskiya, bari mahaifinki ya dawo in faɗa ma sa, na san ma ba zai hana ba".
Hakan kuwa aka yi, bayan dawowar Malam, Inna ta fada masa duk yanda suka yi da Ladidi, ya kuma yi na'am da zancen, tare da karfafa ma Ladidi gwuiwa.
wow..what a great piece. Kauye ana jahilci gaskiya.
ReplyDelete