MARUBUCIYA HAFSAT ABDULWAHEED
MATAN AREWA HAJ. HAFSAT ABDULWAHEED An haifi Hajiya Hafsat Abdulwaheed a jihar Kano, an haife ta a ranar 5th May, 1952. Tayi karatun firamare ɗinta a ' Shahuci Primary School' dake a Kano. Daga nan ta wuce sakandiren ƴan mata ta Provincial Girls School wanda aka sauya ma suna zuwa Shekara Girls Secondary School. Tayi aure a shekarar alif ɗari tara da sittin da shida ( 1966 ),ta auri Muhammad Ahmad Abdulwaheed, tana zaune a jihar Zamfara. Ta na da ƴaƴa, daga cikin ƴaƴanta akwai Kadaria Ahmad fitacciyar ƴar jarida. Marubuciya ce dake rubutunta cikin harshen Hausa. Hajiya Hafsat ta fara rubutu ne tun tana makarantar firamare, inda ta samu damar ƙarbar lambobin yabo daga British Council. A shekarar 1970 Haj. Hafsat ta shiga gasar Rubutu da kamfanin maɗaba'ar wallafa littatafai ta Northern Nigerian Publishing Company (NNPC) ta gudunar, inda ta shigar da labarinta mai suna 'SO ALJANNAR DUNIYA'. Wanda ta rubuta shi tun tana aji biya...