TIMABEE

FATIMA BABAKURA (TEEMABEE)

Matashiyar yar kasuwa
Mai sana'ar hada jakkunan hannu (handbags) na mata.

Fatima Babakura wadda aka fi sani da TEEMABEE, matashiyar budurwa mai aƙalla shekaru ashirin da biyu. Tayi karatun degree ɗinta na farko a jami'ar Mcmaster University Canada.

Ta fara sana'ar hada jaka ne a shekarar 2013, inda ta fara zanawa a takarda. Daga nan ne ta tsunduma ka'in da na'in wajen haɗa jakkunan hannu na mata.

Fatima Babakura na daya daga cikin matasa mata masu kaifin basira da hazaƙa. Wadanda suka kara fito da martabar yan Afrika a idanun duniya.

Mace mai kananan shekaru wadda ta fito daga yankin Arewa maso gabashin Nijeriya abin a jinjina ma ta ne.

Ta fitar da samfur na jakkuna da yawa daga shekarar 2013, ta siyar dasu ga mutanen dake wajen Kasar Canada kama da Dubai, London, South Africa, USA da sauran shagunan siyar da kaya dake a Canada.

Babban burin Fatima bai wuce ta ga ta gina katafen kamfani a Nijeriya ba, wanda ba zai tsaya a iya jakkuna ba har da kayan sawa.

Comments

Popular posts from this blog

Matan Arewa

ABINDA MATA KE SO (EP1)

MANYA-MANYAN KURA-KURAI DA MA'AURATA KE YI BA SU SANI BA