TREND

Chuchu and LubnaSufyan

calmlubna@gmail.com
ayeeshasadeeq2010@gmail.com

TREND

Akwai abinda turawa kan kira 'TREND' da za'a iya fassarawa da wani abu sabo da zai shigo ko ince 'YAYI'. Kamar sabuwar shadda da samari zasu dinga yayi, burin kowanne a ciki ya mallaka, machine da makamantansu. A wajen mata kamar turare, dinki ko wani abu daya danganci kwalliya, wannan TREND bai tsaya a iya abubuwan amfani ba, har da wakoki ko finafinai da zasu shigo yan yayi.

TREND dinmu na yau ta bangaren wakokine, wakokin da kan zo da salon rawa kala-kala. A shigowar 2018 din nan anyo wakoki kala-kala irin su Shaku-shaku, Kope challenge ga kuma sabuwa yar yayi wai ita collapse challenge Wadannnan kalolin rawa da su ka zo da rawar da burin kowanne matashi ko matashiya su saka wakar su kwaikwayi rawar.

Ok! ba sai addini ya kai ga shigowa ciki ba, bara mu taba al'ada kamun muzo kan addini, akwai raye rayen da a al'ada ta malam Bahaushe ko namijin bai kamata ya yi ta ba balle har a tsallako akan mace. Ina hankalinki da kunyarki suka tafi? Mace da aka sani da kunya da kamun kai.

Yanzun ma wata rawa na gani da ake faduwa. Tun ina hangota a ketaren mu har ta tsallako cikin mu, yar uwa ke ba mai shafar aljanu ba, ba mai ciwon hauka ba, ba mai farfadiya ba kinzo kina bajewa kan titi ko a kasa kema kinbi trend ko? Kin manta da yanda mutuwa bata sallama ko?

What if kina bajewar nan mala'ikan mutuwa na gaba dake? Ki ce ma Allah mi? Ko za ki ce trend ne kika bi kar ace ba ki waye ba? Haka zaki mike ana jeho miki tambayar kabari kina kakarewa sai mala'iku suyi miki zuwa daya da guduma, nan zaki fahimci asalin bajewa. For goodness sake me ma yake damunki ne?

Kin zo kina faduwa kasa kina birgima ke nan kin bi trend, mace fa kike. Kin manta mutunci da daraja ta ya mace. Uwa kike, diya kuma mata ga wasu mutane amma kin zo rariya kina zubar da wannan daraja taki.
Duk namijin kirki da ya san ciwon kanka yake kuma nemawa yaransa uwa tagari wallahi ko kusa ba zai kusanto wajen da kike ba. Wadanda zasu taya dama abokan watsewa suke nema sai suka ci karo da daidai da wadda suke so.
Ita fa rayuwar nan idan kika ce abinda mutane keyi kema a dole sai kinyi sai kin wahala. Babu abinda yafi ma ki mutunci da darajarki ta Ya mace... Tun wuri kiyi ma kanki karatun ta natsu. Ba kowane trend ne za ki gani ba kice sai kinyi, kiyi anfani da hankalinki wajen tantance abu mai kyau da mara kyau.
Ki auna kiga idan nayi abu kaza miye makomar rayuwata? Ba wai ki zo kina abubuwa irin na matan jahilai ba, bambamci mace mai ilmi da mara ilimi Shine amfani da ilimin.
Abinda ban gane ba shin dadi ne ke cikin birgimar ko kuwa mi? Ki natsu, ki hankalta ki yi ma kanki karatun ta natsu.

Comments

Popular posts from this blog

SOYAYYA TSAKANIN KI DA SHI TA KARE

Matan Arewa